54

294 21 2
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

5️⃣4️⃣

**********Idonta kan makekiyar tv bango tana kallan tashar sunna tv inda Malam Argugun yake wa'azi akan zaman takewar auratayya ji take tamkar sunanta yake kira yana wa'azin dan kusan gaba d'aya wa'azin ya shafi rayuwarta, da zamantakewar aurenta, wani hawayen bak'in ciki masu ciwo ne suka zubo mata, cikin kukan dake cinta tana danne shi tace " in sha Allah yau za'ayita ta k'are, bazan dauwamar da rayuwata cikin tsoro da firgicin tunuwar asirina ba, gwamma kawai na fad'a duk abinda zai faru ya faru.

Ta mik'e zata fita ya shigo sanye da jallabiya yatsanshi na latsa carbin tally counter, dakyar cikin dakewar zuciya ta runtse idonta da k'arfi muryarta na sark'ewa tace " in....ina....san....maga...na dakai, ta fad'a a rarrabe kamar me koyan magana.

"Nooooooo! Ajlaal yace da k'arfi had'i da wawurar computer gabanshi ya bugata da k'asa idanuwanshi sukayi jajir kamar wuta " a'a Deeyanah karkiyi min haka please, data ce zata fad'a mishi bai tab'a d'auka da gaske zata iya sanar dashi ba, bai d'auka tana da irin wannan k'arfin halin da dakewar zuciyar ba, yayi zaton shaci fad'i ne kawai ta fad'a ne danya kyale ta, dayasan da gaske take da yayi mata barazanar kashe shi idan ta sake ta fad'a mishi.

Ba musu ya k'araso ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun har lokacin tana tsaye bata zauna ba, "ina jinki, yace yana bin jikinta dake rawa kamar mazari da kallo, kasa magana tayi ta kuma kasa zama, yakai mintuna goma a zaune yana jiranta, jin batace komai ba yasashi mik'ewa zai bar wajen, tayi saurin zubewa gabanshi had'i da rik'e k'afarshi gam ta saki rikitaccen kuka wiwi kamar wacce ake zarewa ranta.

Komawa yayi ya zauna ya zuba mata ido yana nazartar ta, an sake d'aukar lokaci batayi magana ba, bata kuma da niyyar yin magana, "Lafiya Deeyanah?

Ya fad'a a nutse, jajayen idanuwanta ta d'ago ta zuba mishi ta kalli cikin kwayar idanuwanshi, " bari na kalle ka Yaya wata k'ila bazan sake samun damar kallanka ina matsayin matarka ba, cikin rashin fahimta yace " ban gane ba?

Sake fashewa tayi da kuka tare da sake rik'e k'afafuwanshi gam, " na lalata komai Yaya, na wargaza komai, na cuci kaina, na lalata rayuwata nayiwa kaina babbar illa, na sari kaina da bak'in dafi, nayi BAK'AR SHUKAR da har in mutu bazata daina yad'o ba, Yaya BAK'AR SHUKAR danayi ce ta fara fidda bak'ak'en 'ya'ya, ka yafe idan zai yiyu Yaya.

"Wai meke faruwa ne?

Ya fad'a gabanshi na tsananta fad'uwa, sai da ta runtse idanuwanta da k'arfi dakyar ta motsa bakinta ta had'a kalaman " NA CUCE KA, NACI AMARKA Yaya, daga nan ta kwashe komai tasss tun daga farko har k'arshe ta fad'a mishi.

Ji yayi an fisgeshi an d'aga shi sama an buga shi da k'asa da k'arfi, kamar zararre ya kwashe da dariya yace " Deeyanah kenan a sani na baki da k'awaye balle ince sune suke zagaki ki rabu dani, idan har rabuwa kike san yi dani basai kin biyo ta wannan hanyar ba, dakin sanar dani da zan sawwak'e miki kuma na d'orawa kaina laifin idan ma iyayenmu kike ji, bazan bari kiyi laifi ba zan wanke ki a idonsu, cikin kuka ta kama kafad'unshi ta girgizashi tana fad'in " da gaske nake Yaya wallahil azim babu k'arya a magana ta.

Murmushi ya sake yi a karo na biyu yace " kice dai kawai kin daina so na Deeyanah ko kuma dama tun farko bani kike so ba matsa miki akayi batare da an tambaye ki ra'ayinki ba, zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu ya mik'e yana fad'in " a gida d'aya aka haife mu muka girma, a d'aki d'aya aka rene mu, mutane d'aya ne sukayi mana tarbiyya Deeyanah idan har ke mace zaki iya aikata wad'annan abubuwan a tarbiyyar da aka bamu to ni namiji da yanzu ba'a san inda nake ba, ki rink'a tunani kafin ki zartar da abu ki tuna da mutuncin iyayenmu dana ahalimu dana gidanmu, koda ace kina san rabuwa dani bai kamata kiyiwa kanki irin wannan mummunan sharrin ba, zan baki kwanaki biyu kiyi tunani idan kinga kina san rabuwa dani shikenan, amma ki sani ina sanki, ina matuk'ar k'aunarki.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now