17

441 21 1
                                        

BAK'AR SHUKA...!

             NA

HAUWA A USMAN
       JIDDARH

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

1️⃣7️⃣

Kwana biyu kenan baiga giccinta ba, yana so ya tambaya amma kunya ta hanashi, dole ya daure Ammu na zaune a falo tana kallan Sunna Tv ya zauna kusa da ita yana fad'in " ina yini?

"Lafiya lau, ya aikin?

"Alhamdulillah, ya bata amsa kafin duk sukayi shiru babu wanda ya sake magana, " Ammu inaga fa next week zamu wuce dama neman visan Deeyanah ne ya bani wahala amma komai ya dai-dai ta da izinin Allah, ya fad'a yana tsokano maganarta.

Hankalinta ta mayar kanshi tana murmushi me kama da dariya tace " masha Allah! wacce rana zaku tafi?

"Maybe nan da kwana bakwai ko takwas, in sha Allah.

"Kace mu hau shiri da dake-daken yaji da kuka da kub'ewa ko?

Kanshi ya shafa yana murmushi, " ka sanar da Deeyanah?

Da sauri yace " a'a, dan anzo inda yake san aje.

"Ai ya kamata ka sanar da ita da wuri idan da shirin da zatayi tayi shi da wuri ba sai lokaci ya k'ure ba.

D'an shiru sukayi, Ammu ta nisa tana fad'in " ka shiga tana bedroom d'inta, guntun murmushi yayi batare dayace komai ba, sanin muddin tana wajen bazai iya tashi ya shiga bedroom d'inta ba yasata mik'ewa tabar falon, ai tana mik'ewa ya mik'e yayi wuf ya shige bedroom d'in har yana bigewa da k'ofa.

Kwance ya sameta k'asan tiles daga ita sai siket d'in undi tayi amai duk ta dame jikinta da aman, saurin k'arasawa inda take kwancen yayi, bai damu da yadda ta b'ata jikinta da amai ba ya d'ago ta ya rungume ta cikin jikinshi, bai direta a ko'ina ba sai ciki kwamin wanka, ya kai hannu ya zame siket d'in jikinta tare da sakar mata shower, ajiyar zuciya ta sauke had'i da k'ank'ame shi, tana ji tana gani babu yadda zatayi yayi mata wanka yayi mata brush ya nad'o ta a towel kamar Baby.

K'ofar bedroom d'in ya bud'e ya d'an lek'o ganin ba kowa yasa shi fita yana d'auke da ita a jikinshi bedroom d'inshi ya kaita ya kwantar da ita saman bed yaja mata blanket ya rufe ta ya fita, d'akinta ya koma ya gyara shi tas tas ya wanke mata bathroom ya kunna humidifier ya feshe ko'ina da Air freshener ya saka mata turaren wuta a buna ya isa gaban wardrobe d'inta ya d'aukar mata pant da bra sai doguwar rigar atamfa da hijab da plate shoe, da kanshi ya saka mata kayan ya rik'eta gam a jikinshi suka fita, Ammu na kitchen na girki Deerah na taya ta da aikin surutu.

A hankali cikin nutsuwa yake tukin har ya isa asibitin Sahal a kame ya fito ya d'auke ta, cikin kunnenshi ta rad'a mishi " ka sauke ni zan iya tafiya da kaina, kamar baiji abinda tace ba ya cigaba da tafiya da ita.

Bayan likitan ya gama jin duk bayananta ya nisa tare da kallan Deen yace " ciwon maran dake damunta alaji ne na wani abu da take ci ko take sha wanda jikinta baya so akwai possibility d'in  idan tayi sex ta daina, impact ma ciwon mararta bashi da maganin daya wuce sex sai dai a bata pain reliever kallan juna sukayi ita dashi tayi saurin duk'ar da kanta k'asa, magunguna ya rubuta musu ya mik'ewa Deen  yana fad'in " idan kunje gida a sami ruwan d'umi da towel me tsafta a d'an gasa mata marar.

Ta kula da yadda yake kanne dariya amma tayi banza dashi, yana tallafe da ita ya shigar da ita bedroom tare da zaunar da ita gefen gado ya fita, bai dad'e ba ya dawo d'auke da tea mai kauri ya bata, dakyar yana lallab'ata tasha tea d'in, ya fita, ya dawo d'auke da roba a hannunshi ya shiga bathroom ya sirko ruwan zafin ya fito da d'an k'aramin towel, ita tama manta da batun wani wai a gasa mata mara, ita fa tunda take bata tab'a jin inda ake gasa mara ba, anya likitan nan yasan me yake yi?

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now