28

301 14 1
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*
   

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

2️⃣8️⃣

" sanda nake yi miki bazai hana na gigita duniyarki na kuma tarwatsa rayuwarki ba muddin naga zan rasa ki sai dai muyi biyu babu kowa ya rasa a tsakaninmu.

Bai d'auki komai ba sai d'aya daga cikin mukullan motocinshi ya fita, duk da dare yayi sosai dan k'arfe 2:30am na dare hakan bai dame shi ba.

Tana kwance kan bed tana bacci hancinta ya shak'o mata k'amshin dako a gigin mutuwa taji shi zata gane kona waye, saurin bud'e idonta tayi aiko idonta ya sauka cikin nashi sosai yayi gaf da ita har numfashinshi na shiga cikin hancinta.

Cikin tashin hankali ta mik'e zaune shima zaunen ya tashi had'e da matsowa daf da ita ya zura hannunshi ta gefen wuyanta zuwa k'eyarta cikin gashin kanta ya matso da fuskarta dai-dai tashi ya goga hancinshi a kuncinta ya shak'i k'amshinta, hannayenta ta sanya a k'irjinshi ta hankad'ashi da k'arfi ta juya ta mik'e tsaye,  wani irin kallo yayi mata tun daga sama har k'asa  bakinshi bud'e yace.

"Wow! Wato irin wannan sexy night gown d'in ake saka mishi kenan?

"Amma idan za'a d'an b'alla min sai nayi ta fama, to wallahi gobe idan zaki zo ki taho min da wannan rigar baccin.

"Hannayen ta had'e tana jin wani malolo daya tokare mata mak'oshi, " dan Allah ka fita Deen yana toilet karya fito ya ganka.

"To ya gannin mana, in ya ganni sai me?

Muryarta na sark'ewa tace " ka fita please idan ya ganka anan komai yana iya faruwa!?

Komawa yayi ya zauna saman gadon had'i da tankware k'afarshi yace " ai nafi san koman ya faru.

Jin motsin Deen cikin toilet d'in ya sata saurin kallan k'ofar toilet, ganin kamar ana tab'a k'ofar ai bata san sanda ta rik'o Ajlaal ba, yayi wani layi irin na 'yan duniya yana dariya yace " calm down Beb!

" Zuwa nayi naji dalilin daya saki rufe wayarki tun bayan kwana biyu.

Tana turashi zuwa k'ofa tace " kaje zan kunna yanzu, bud'e k'ofar Deen yayi dai-dai da d'auke wuta, kissaing Deeyanah Ajlaal yayi a kumatu kana ya rad'a mata " ki tabbatar kin kunna wayar nan yanzu in ba haka ba na dawo, bata bashi amsa ba ta hankad'a shi waje, ido ta lumshe tare da sauke ajiyar zuciya a fili.

" D'auke wuta yau kuma a Estate d'in nan!?

A dururuce tace " gaskiya da mamaki kam!

Zai sake yin magana wutar ta dawo, kallo d'aya yayi mata ya gane a dabarbarce take ga gumi dake ta faman tsatstsafo mata!.

Bayyi mata magana ba ya nufi bed d'an tsayawa yayi ya shak'i iska kafin yace " new scent wannan saban k'amshin fa daga ina kuma?

Yadda kasan saukar aradu haka k'irjinta ya buga da mugun k'arfin cikin kame-kame tace " na'am magana kake!?

"Naji wani saban k'amshi ne, kamar kwanaki ma na tab'a jin irinshi a d'akin nan.

Saboda tsabar rud'ewa ji tayi k'afafunta na neman kasa d'aukarta.

"Eye!  tace a figice, kallan yadda duk ta rud'e yayi kamar zayyi magana sayya fasa, ya kwanta saman bed ya barta nan tsaye k'afuwanta na kerrrma, cikin sanyi taja jikinta zuwa bed d'inta harta kwanta ta tuna da batun kunna waya, tayi saurin mik'ewa taje ta d'auko wayar ta kunna, tana kunna wayar sak'onshi ya shigo.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now