15

409 23 2
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*
   

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

1️⃣5️⃣

"Kiyi hak'uri Deeyanah ki daina kuka nasan Deen yana sanki na tabbatar akwai dalilin dayasa shi yin haka.

"Bashi da wani dalili daya wuce kishin Ajlaal...

Azrah ta fad'a tana shigowa fuskarta a murtuke ta zauna kusa da Deeyanah.

"Kedai wallahi anyi sakarya marar wayo da fad'a zakiyi dashi akan makarantar ko me?

"Ke ko irin kissar nan ta mata ma baki iya ba?

"Ai kamata yayi daya ce kin gama makarantar nan har abada kiyi d'an murmushi had'i da kashe murya kice " sai yadda kace ranka ya dad'e.

"Amma saboda ke wawiya ce harda wani hard'e hannu a k'irji ke gaki marar kunya zakiyi fito na fito da miji akan shirmen banza.

Azrah ta fad'a tana d'an kai mata mangari, Azwah ta cafe da fad'in " ni wallahi na rasa inda Deeyanah takai wayewa da iliminta ace komai sai an koyawa mutum?

"Meye amfanin yawonki a social media?

"Meye amfanin wayar hannunki da bazata amfane ki da komai ba?

"Ki shiga Facebook akwai page na matan aure wanda aka bud'e dan cigaban mata had'i da wayarwa da mata kai, haka ma a WhatsApp akwai groups manya na manyan mata wanda zaki k'aru su gogar dake.

Azrah ta cafe da fad'in " ji dai group d'in CIWON 'YA MACE na Hauwa A Usman Jiddarh wallahi ana k'aruwa sosai, dole sai kin samu abinda zaki amfana.

"A Facebook yake ko?

"A'a a WhatsApp yake amma dai babban group ne gaskiya, babu b'angaren da ba'a tab'owa fa.

"Amma ana biya ko?

Azwah ta buk'ata, "A'a ko d'aya wallahi kyauta ne, "amma shine ko ki saka ni ciki ni dana samo abun arziki kona gyaran aure saina tab'o ki.

"Yi hak'uri mantawa nayi amma bari yanzu na tura number ki a saka ki.

"Number ta ko number mu?

"Number ku ke da wa!?

"Ni da sabuwar Amaryar mu mana, suka kwashe da dariya kafin suka juya suka shiga bata shawarwarin zaman aure had'i koya mata hanyar da zata bi ta karkato da hankalin mijinta kanta, sun dad'e sosai suna bata shawara kafin Azwah ta mik'e tana fad'in " bari na d'auko miki kayan 'yan Niger da Sudan dana yi order ki fara sha kina tsuma kanki tun yanzu.

Azrah ta kwashe da dariya tana fad'in " sai babbar Yaya magajiyar uwa Allah dai ya biya.

Tana jinta ta wuce tana dariya dan ta saba da shak'iyancin Azrah, cigaba tayi da bata shawarar.

"Ke kinga mazan yanzu sai kin zama fitacciyar mara kunya fitsararriya kin koma musu kamar tantiriyar karuwa kafin ki iya dasu idan ba haka ba kina ji kina gani zaki sha kayan haushi idan ma kinci sa'a ba'ayi waje dake ba.

"Bawai ina nufin rashin kunya da fitsara irin ta turo baki kota mayarwa da miji magana ba, ina nufin ta kissa, tayi magana cikin tsokana, sarai Deeyanah ta gane Tsokanar da Azrah keyi mata amma bata kula ta ba.

"Sai kin zama kamar 'yan Daudu kome yawon dandi ki koyi sassarafa takunki, ki koyi juya jiki had'i da juya k'ugunki da karairaye-karairaye kin koyi rangwad'a da tarairayar miji, dan mazan yanzu ba irin mazan da bane nada ko yaya suna iyayin maneji dake a yadda kike, mazan yanzu kam hmmm yadda kika dama haka za'a sha ta, idan kin kasa yi musu abinda suke so sai su fita waje su nema.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now