50

329 22 6
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

5️⃣0️⃣

Direct bedroom d'inta ta wuce ta shiga bathroom ta sakarwa kanta shower batare data cire kayan jikinta ba, har lokacin jikinta b'ari yake, ta dafa bango tana cigaba da kukan, takai awanni biyu ruwan shower na sauka kanta  kana ta mik'e tsaye daga zaman dirshan d'in da tayi a k'asa, kayan jikinta ta cire tsaf ta zuba su a shara gaba d'aya kyankyamin kanta da jikinta da komai ma take yi, har kayan jikinta da bathroom d'in da gaba d'aya bata san ganin komai, dan duk abinda ta kalla hotan irin abinda sukayi da Ajlaal ke dawo mata cikin kanta, ido ta runtse da k'arfi hawaye na zubo mata, cikin zafin rai ta bud'e idanuwanta da suka gama rinewa zuwa ja, da wani irin zafin rai ta nufi inda take aje soson k'arfen wanke masai tasa hannu ta damk'e shi, da wani irin k'arfi ta soma dirzawa jikinta da iya k'arfinta.

Tana kuka tamkar ranta zai fita tana dirzar fatar jikinta jini na zuba da fushi take dirzar fatar kamar zata b'aye fatar jikinta, duk tabi taji ciwo amma hakan bai dame ta ba, ta dad'e tana wankan kana ta sulele tana kuka, tayi wankan tsarki yafi sau 20 gani take har zuwa lokacin daud'ar zina bata bar jikinta ba, gani take duk yawan wankan tsarkin da zatayi bazata tab'a samun tsarkin jiki dana ruhi ba, sai da ta gaji dan kanta kana ta hak'ura ta fito daga wankan, tana d'ora idonta akan gadon dake d'akin, ta ganta kwance Ajlaal na saman ruwan cikinta suna aikata zina, ido ta runtse da k'arfi had'i da kawar da kanta gefe tace " turrrr dani, kaico na, tun yanzu tun kan aje ko'ina mugun abinda na aikata ya fara farautar rayuwata, ya fara barazana ga farin ciki na.

Durk'ushewa tayi tana kuka wiwi tare da dukan k'irjinta tana fad'in " na tarwatsa gidana, na tarwatsa ahalina, na fasa gidana, na wargaza farin cikin mijina dana d'ana, na b'ata aure na, na b'ata sunan zuri'armu gaba d'aya, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga uku na lalace, Allah na tuba ka yafe min, Astagfirullah Astagfirullah Astagfirullah, ta k'arashe maganar da wani irin kuka.

Ji tayi ta tsani gaba d'aya gidan komai ya fice mata a ranta ta tsani kanta, duk wata kusurwa ta gidan data kalla hoton ta da Ajlaal take gani suna aikata masha'a, har aka kira magriba tana nan zaune ta had'a kai da gwiwa tana ta faman risgar kuka wiwi tun muryarta na fita har yakai ya kawo muryarta ta dishashe idanuwanta sun kumbura suntum, dakyar ta rarrafa ta shiga ban d'aki ta d'auro alwala, ta fito ta shinfid'a sallaya ta zira doguwar riga ta tada sallah, tana tada sallar saban kuka ya kwace mata, dan sai yanzu taji tana jin kunyar Ubangiji, ta tayar da sallah yakai sau biyar kuka yana sata sallamewa sai haka ta hak'ura tayi sallar hawaye na zuba, da takai sujjada me memakon karatun sujjada sai Allah na tuba ka yafe min take maimaitawa.

D'ogowa tayi ta sake sabuwar sallah amma tana kai goshinta k'asa kuka ya kwace mata, dole tayi control kukan tayi sallar, data sallame sallar sake komawa tayi sujjada takai goshinta k'asa ta soma addu'a " Ya ALLAH! kasanya mu cikin bayinka tsarkaka masu dace da ni'imar ka, gafarar ka, rahamar ka, bud'i da wadatar zuci, da tsarkin zucciya, da shiriyar mu baki d'aya, ya Ubangijin talik'ai ya majib'ancin lamura, kai ne Afuwu me afuwa, kai ne Rahamanu me Rahama, kai ne mad'aukakin sarki wanda ba'a haifa ba kuma bai haifa ba, Allah ka yafe min, ka tsarkaken zuciya ta, kayi min afuwa da sassauci, kayiwa ruhina salama, ina jin kunyarka ya Ubangiji, ina jin kunyar girman laifi na, ina jin kunyar neman afuwa agare ka, Astagfirullah Astagfirullah! Astagfirullahna wa'atubi ilaik, ta k'arashe da wani irin kuka.

Ranar kam cur Deeyanah ta kwana saman sallaya tana neman yafiya da afuwar Ubangijinta, ko gyangyad'i batayi ba, duk iya satar bacci da ake fad'a yau kam ko kusa da ita bai zo ba balle ya sace ta, bayan ta idar da sallar asuba cigaba da zama tayi akan sallayar tana jan La'ilaha Illa antassubahanaka innikuntu minal zalimin har garin Allah ya waye.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now