*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh2️⃣2️⃣
*CIGABAN LABARI*
A matuk'ar tsorace ta mik'e tsaye duk ilahirin jikinta na rawa da tsuma, sakamakon ganin gawar me doya da kwai, dame shagon daya bata ruwa, da mutumin daya sai mata doya,
duk da zuciyarta ta gama k'ek'ashewa bai hana hawayenta zuba ba, hankalinta ya kai k'oluwar tashi, rasa abinda zatayi yasa ta d'ora hannu aka ta durk'ushe k'asa,
tayi shiru, ta kasa kukan fili saina zuciya, sautin dariyarshi ta daki dodon kunnenta, " bakiga komai ba yarinya,
bazaki aikata alkhairi ki lalace ba saboda alkhairi dank'o ne baya fad'uwa k'asa banza, haka kuma bazaki k'ulla sharri ki gama lafiya ba, saboda sharri d'an aike ne duk nisan da yayi sayya dawowa meshi,
kin cuceni kin lalata min rayuwa, kin rabani da duk wani farin ciki da jin dad'i na,
busassun idanuwata da suka dad'e da bushewa ta d'ago ta kalleshi ido cikin ido, duk da bata k'aunar ganin koda sawayenshi ne,
" na sani na kuma yarda ni me laifi ce ko awajen Allah, shi Ubangiji gafurur Rahim ne, shi mai yafiya ne,
inata Istigfari da neman yafiyarshi, sai kaine baka yafiya?"Meyasa bazaka manta da abinda ya faru a baya mu fuskanci gaba ba?
"Meyasa bazaka yafe min ba, bayan na tuba, na karb'i kuskure na, na baka hak'uri na nemi yafiyarka?
Hannayenta ta had'e waje d'aya tana rok'onshi tare da bashi hak'uri, amma a banza sai dariyar dayake kyalkyalata mata,
ganin bashi da niyyar hak'ura yasata mik'ewa taja k'afarta tayi gaba ta barshi anan, hannunta rik'e da zaninta dake neman fad'uwa,
duk wata gajiya da yunwar da take ji sun tafi, tana d'angyashi tayi tafiya me nisan gaske, kana ta samu waje ta zauna ta zubawa k'asa ido tana hawaye had'i da tuno *D'ANTA*, a fili ta furta sunanshi " *DEEDEE* yaron dayaci sunan Babah, suka had'a sunansu waje d'aya ya bada *DEEDEE* * Deeyanah & Deen**WAIWAYE....*
Deedee ya taso cikin gata da kulawa, kowa cikin dangi na sanshi, ga Deedee da shiga rai,
suna zuwa hutu jefi-jefi, saboda acan Deen yake aiki bayan ya gama abinda ya kaishi suka rik'e shi saboda kwazonshi,
shekarun Deedee uku Deeyanah ta sake samun ciki,
lokacin sun kusa shekara biyar da aure, watan ciki Deeyanah hud'u suka zo gida hutu,
Murna wajen dangi da 'yan uwa ba'a magana, cikin dare matsanancin ciwon mara ya tasarwa Deeyanah , ta kasa bacci,
sai juye-juye take ta kasa kuka, ta kasa tashin Deen ta fad'a mishi, saboda tasan yana da meeting me matuk'ar mahimmanci gobe,
tana cikin wannan hali sai faman nishi take ya farka, a tsorace ya diro daga kan gadon, jikinshi na rawa ya k'arasa inda take,
ya d'agota had'i da fad'in " lafiya?"Meke damunki?
Da hannunta ta nuna mishi mararta while tana jujjuya kanta saboda azaba, jallabiya ya zira da sauri, ya sunkuya da nufin d'aukarta,
da hannu tayi mishi alamar a'a, " please ki bari mu tafi asibiti, agogo ta kalla 2:30am na dare, shima agogon ya kalla danya gane nufinta,
" na sani dare yayi, amma bakomai, dakyar tayi k'arfin halin cewa " ka bari ya lafa, zanyi bacci gobe maje, " kin tabbatar LOML! kanta ta d'aga mishi alamar eh,
tallafe ta yayi ya kwantar da ita akan gado yaja mata bargo ya rufeta, cikin ikon Allah bacci me nauyi yayi gaba da ita,
da wuri ya tashi ya had'a mata ruwan wanka, ya dafa mata tea, dama Deedee yana part dinsu Babah, da salati a bakinta ta tashi, idonta ya sauka akanshi, suka sakarwa juna k'ayataccen murmushi,
" harka tashi?Tayi maganar tana murza ido, " ba dole na tashi da wuri na shirya zuwa asibiti ba, " asibiti kuma?
Kallan da yayi mata yasata yin dariya tace " au ashe fa bani da lafiya ko?
Ta fad'a cike da tsokana, " au ashe ne ma ko?
" Kodan bake ke jin zafin ciwon ba?
" Oh! haka ne fa ko?
"Zafin a jikinka yake shiyasa bana ji, hancinta yaja yana dariya yace " tashi kiyi wanka muje kiga likita, " meeting d'inka fa?
Kanshi ya dafe yana koikwayon muryarta yace " au ashe fa ina da meeting ko?
Sosai ya bata dariya danta gane ramawa yayi, " Allah naji sauk'i kayi tafiyarka ba damuwa,
" kinga tashi ki shirya mu tafi, yayi maganar yana d'agota, cikin shagwab'a tace " Allah na samu sauk'i, kayi tafiyarka, turata yayi cikin ban d'aki yana dariya,
ta gama shiryawa tsaf, cikin shirinshi ya kalleta ya lumshe ido had'i da rausayar da kanshi, cikin sanyin murya yace " masha Allah, Ubangiji yayi halitta a wajen nan,
ta cikin mudubi ta kalleshi a nutse tace " Yaya kayi tafiyarka meeting d'inka wallahi jikina da sauk'i, idan ka matsa sai naje da kaina kai kayi tafiyarka,
ido ya zaro yana takowa gareta yace " na barki kiyi me?"Allah Dee! da gaske nake, damma ka matsa ne zani, amma badan haka ba, da babu inda zani, dakyar ta shawo kanshi ya yarda zaje meeting ta tafi asibitin da kanta,
har bakin mota ta rakoshi tana d'auke da briefcase d'inshi, ya shiga ya zauna a mazaunin driver ya kalleta yana murmushi yace " kodai zakije ki d'auko hijab na kaiki da kaina inyaso saiki dawo,
motar ta rufe mishi tana dariya ta juya da gudu zata koma gida danta san idan ta biye mishi saisu kwana anan,
bayanta yabi da kallo yana murmushi, kanshi ya girgiza tare da yiwa motar key, harya kai bakin get zai fita ya tsaya had'i da kwala mata kira,
" Deeyanah!, ta juyo tana dariya, ya d'aga mata hannu yana murmushi yace " ki kula da kanki please, an na baki amanar kanki, dan haka nan yaji jikinshi wani iri shiyasa hankalinshi yak'i kwanciya,
tana dariya ta shige part d'insu.Hijab ta saka ta zari handbag da key d'in mota ta fice, part d'in iyayensu ta shiga ta gaidasu, ta sanar dasu zata asibiti bata jin dad'i,
ganinta da Hijab yasa Deedee sanya kuka yana fad'in " Momy zan biki, kanshi ta shafa tana murmushi ta kasa cewa yazo su tafi tare, saboda kunyar iyayensu,
ganin basu ce ta tafi dashi ba, gashi yana kuka yasata zama, ta kasa tafiyar, " kikace asibiti zaki?Cewar Babah, Ammi data gane meyasa tak'i tafiya tayi murmushi tana cewa " barta fasawa tayi saboda d'anta yana kuka bazata iya tafiya ta barshi ba, da sauri ta mik'e ta fice tana dariya cike da kunya, suma dariyar suke mata, Babah yace " rabu da ita zo ki d'auki d'anki,
tana cigaba da tafiya tace " a'a nifa ba haka nake nufi ba, ta k'arasa maganar tana shigewa mota, ta fice, tunda ta hau titi gabanta ke faman fad'uwa, a fili ta furta " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ,
" K'iiiiiiii motarta ta tsaya, tayi yin duniya amma tak'i tashi, ta fito daga cikin motar tana jan tsoki, jakarta ta bud'e ta fito da waya zata kira,
Yana tuk'i cikin kwanciyar hankali, wanda a zahiri hankalinshi ba'a kwancen yake ba, tun bayan rabuwarshi da ita ya rasa sukuni da walwala,
Shekaru biyar kenan rabunshi da ita, jin shekaru biyar d'inan yake kamar shekaru dubu biyar, yana rayuwa ne a tsaye amma ta ciki mutuwa yake yi a kowacce dak'ik'a, wayarshi dake ta faman ruri ya kalla kafin yaja d'an gajeren tsaki d'aga idon da zayyi idonshi ya sauka a kanta, kamar daga sama ya hangota tsaye jikin mota tana latsa waya, wucewa yayi had'i da girgiza kanshi dan idan da sabo ya saba da ganin gizonta, idanuwanshi sun dad'e da ribatuwa da ita, mudubi ya kalla yaga still tana tsaye, "kodai da gaske itan ce?Ya tambayi kanshi, bai san sanda ya taka mahaukacin burki k'ukk'uuuuuuuuu ba saida gabanta yayi mummunar fad'uwa dataji k'arar burkin, jikinshi na rawa ya fito, bakinshi na rawa ya furta " Dee.....ya...nah!, yayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana,
wata irin mahaukaciyar fad'uwa gabanta yayi, cikin kid'ima da tashin hankali taja baya tana fad'in " Aj....lal.......JIDDARH...
YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
EspiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...