60

653 26 41
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

6️⃣0️⃣

A hankali ta d'ago kanta ta sauke idonta akanshi tana k'ara ganin girmanshi, tun da abin ya faru kowa gudunta yake yi, babu wanda ya tsaya ya saurare ta, ko sau d'aya tak babu wanda yaso jin ta bakinta ko abinda ya faru, a karon farko kuma mutum na farko daya saurare ta, ya kuma so jinta bakinta, kanta ta sunkuyar k'asa tana san hawaye su zubo mata amma babu ko d'igo, a fili ta sauke ajiyar zuciya tana sake d'agowa ta kalli Deen da Babah da kallo, duk da kallo d'aya tayi musu ta gane dolen da akayi musu shinfid'e akan fuskokinsu, kanta ta sunkuyar had'i da bud'e baki zata soma magana Deen yayi saurin mik'ewa ya kalli Babah yace " bari na amsa waya, Babah ya gane guduwa zayyi dan haka yayi saurin cewa " jeka!, dan kar Abbi ya hana shi, shima dole ce ta zaunar dashi.

Murmushin yak'e Deeyanah tayi kana ta soma bada labarin komai tun daga farkon had'uwarta da Ajlaal a makaranta har kawowa mafarin abun bata b'oye komai ba.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un lalle Deeyanah kin tafka babban kuskure kece babbar me laifi duk abinda ke faruwa ke da kanki kika jawowa kanki, kin shuka BAK'AR SHUKA... shiyasa duk abinda Allah yace a bari barin nashi shine mafi alkhairi, shi kuma Ajlaal yayi amfani da k'uruciyarki yaci moriyar kwakwalwarki ta mace ya dasa miki tsoronshi da firgici cikin ranki da haka yayi amfani ya cimma burinshi a kanki, yayi wasa da kwakwalwarki, ina ita RALEEYA DATA JEFAKI CIKIN WANNAN MUMMUNAR K'ADDARAR?

"Tana ina?

"Ina labarinta yake?

"Sau Dama k'awaye suna da tasiri a rayuwar mutum, sukan kai mutum su baro shi, kamar yadda RALEEYA ta cuce ki ta jefa cikin gagarumar masifar da fitarki sai Allah yaso, ta zuga ki, ta baki shawara kin d'auka, meyasa data baki shawarar baki nemi shawarar kowa ba?

"Gashi nan ke abinda kuka aikata yake farauta ita tana can tana rayuwa cikin jin dad'i da walwala ta barki cikin danasani da nadama, shi kam Babah wani irin haushinta da tsanarta yaji sun k'ara ratsa shi da kafi, musamman ma da yaji sanadin abin ya d'auka k'addararta ce tazo mata a haka, amma yanzu daya ji ita ta jawowa kanta haushinta yake ji sosai, a fili yaja tsoki had'i da mik'ewa ya kalleta yayi kwafa, kamar bazayyi magana ba sai kuma yace.

"Kin cuci kanki kin cuci rayuwarki, kin jefa wad'anda basu ji ba basu gani ba cikin masifar da kika jefa kanki, d'an itaciyar BAK'AR SHUKAR... da kikayi ke kad'ai gashi nan kin raba mana muna cin shi tare dake, gangancinki yayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarki da d'anki, Allah ma kad'ai yasan iyakacin wad'anda zaki zama ajalinsu, nayi takaicin haihuwarki, nayi nadamar aurawa Deen ke, dama ban haifeki ba, ke inama ban auri uwarki ba balle na haife ki, da nasan bak'ar daga zaki zama dana sa an zubar da cikinki tun kafin ki zo duniya, kin b'atawa zuri'ar mu suna har a tashi duniya, kin jefa mu cikin kunyar duniya har mu mutu, kin zubar mana da k'ima da mutumcinmu dan yanzu bamu da wani sauran mutunci a idon Jama'a, muna sanye da tufafi amma ana kallan mu tsirara, matar da tayi dakon cikinki har tsayin watanni tara, tayi nak'udarki, kika tsaga tsatsanta kika fito, ta shayar dake daga jikinta, ta reneki amma ki rasa dame zaki biyata sai da mutuwa Deeyanah bayan ita ta baki rayuwa?

"Allah ya d'auki ranki kamar yadda kika zama sanadiyyar mutuwar Aina'u.

Da sauri ta amsa mishi da " Amin Babah, Amin ya Allah, Ubangiji ya amsa rok'onka ya karb'i raina na huta dan nima na gaji da wannan bak'ar rayuwar, zayyi magana Abbi yayi saurin mik'ewa ya jashi zuwa waje, bai jima ba ya dawo, sai da ya d'an saita kanshi kana yace " wallahi ko abinda na mallaka a duniya zai k'are saina ga bayan Ajlaal da duk wanda ya d'aure mishi gindi, yadda ya saki kuka saina zubar da hawayenshi, yadda ya saka mu cikin halin bak'in ciki da damuwa shima saina saka ahalinsu kaf a cikin kwatankwacin halin daya saka mu, saina tona mishi asiri duniya tasan waye shi.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now