BAK'AR SHUKA...!
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarhNafa sanar muku bazan rink'a posting asabar da lahadi ba, daga ranar litinin zuwa juma'a kad'ai zan rink'a posting, dan Allah masu bina private suna yi min comment ku daina, group ne wajen comments so please idan zakuyi comments ku rink'a yinshi cikin groups.
2️⃣1️⃣
Tana zaune saman cinyarshi tana bashi abinci a baki, sai zuba mishi kissa take, duk tabi ta hana shi zama sakat, shi kam duk abinda tayi biye mata yake, bayan sun gama cin abincin sun nutsu yace " rufe idonki!
Wani irin kallo tayi mishi daya ratsa ruhinshi, " surprise ne ko?
Dakyar yace " kedai rufe mana, "tom! tace tana rufe idon, takarda ya dank'a mata a hannunta kana yace " bud'e! cikin rashin fahimta tabi takardar da kallo, da ido yayi mata alamar duba, a nutse ta soma karanta takardar, ihuuu tayi ta rungume shi, kiss ta shiga jera mishi ta ko'ina a fuskarshi, " nagode! nagode! nagode K'auna ta, thank you so much Dee!, ina sanka, I love you, cikin basarwa yace " na sani! tana dariya tace " bakomai yau kam bazanji haushi ba, na sani ramawa kayi.
"Deeyanah! ya kira sunanta a hankali, jin yadda ya kira sunanta yasata nutsuwa, zaki fara karatu a k'asar da addininmu da al'adarmu suka sha bam-bam, muna bambamce-bambamce mai tarin yawa tsakaninmu dasu, ina da kishi Deeyanah,
ina da matsanancin kishin da zan iyayin komai akanki, ina iya bada rayuwata akanki, ki kula kada kija abinda zai haifar mana da matsala a tsakaninmu, " in sha Allah zan kiyaye Yaya, kanshi ya d'aga mata tare da cewa Allah ya bada sa'a, ta amsa da " Amin ya Allah!." To a bani tukwicina! ture shi tayi tana murmushi tace " wai kai yaya baka gajiya da sex ne?
"Kai da ayi ta abu d'aya, kwashe yayi da dariya sosai sai da yayi me isarshi kana yace " aiko bazan tab'a gajiya dake ba har abada, bama na fatan Allah ya kawo ranar da zan gaji dake, kedai kiyi ta bani ina kwasa kawai idan banyi sex ba me zanyi?
"Daga shi sai sallah sune suka zame min dole.
Idonta kanshi tace " Dee! ni ko me zanyi maka ka tsane ni, kai tsaye yace " cin amana Deeyanah, daga ranar dana san kina cin amanata da wani daga ranar kar ki raba d'aya biyu zan tsaneki tsana ta har abada, zanyi miki nisan nisa, nisa na har abada, daga ranar nayi miki alk'awarin bazaki sake gani na ba har abada...
"Dakata duk me ya kawo haka?
"Ina kishi Deeyanah, ina matsanancin kishin da nake jin zan iya kashe koma waye a kanki.
"Kwantar da hankalinka hakan ma bazata tab'a faruwa ba har abada ni taka ce kai kad'ai har rai da mutuwa in sha Allah.
Ranar da zata fara zuwa makaranta shigar musulunci tayi, doguwar riga ta saka marar shape da d'an madaidaicin hijabinta, sai da ya biya ya aje ta a makaranta, har zata shige aji yace " Deeyanah ina sanki, kada ki manta ina da kishi ki kula sosai, murmushi tayi mishi had'i dayi mishi kiss.
Gaskiya Deen dayace akwai banbanci mai tsayin gaske a tsakaninmu damu dan kuwa taga abinda ya girmi kanta, dan haka taji gargad'in Deen ta kuma yiwa kashedinshi guri cikin kanta ya zauna daram ta kame kanta sosai, musamman kullum idan zai kawo ta makaranta sayya fad'a mata yana da kishi.
Tana zaune saman sofa while yana zaune k'asan carpet yana yanke mata farce, " Dee! ni ko zan so naga kishin nan naka da ake tayi min gargad'i kanshi, ido ya zuba mata na tsayin lokaci kana yayi murmushi had'i da girgiza kanshi batare dayace komai, " wata rana zan tsokano kishi nan dai na ganshi da ido, " kada ki soma! karma kiyi fatan ganin haka,
zatayi magana amai ya taso mata, da gudu ta mik'e ta shige bedroom d'inshi ta fad'a toilet daga tsaye ta soma kelaya amai, yana tsaye kanta yana jera mata sannu, wanka yayi mata kana ya wanke bathroom d'in, tana kwance saman 3 sitter ya k'araso kanta.
YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...