26

324 18 4
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*


NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

2️⃣6️⃣

" Wallahi idan k'afarki ta sake tako d'aya daga inda kike saina saki videon nan ga duniya ki zama macen Bahaushiya musulma 'yar arewa cin Nigeria ta farko da zata fara yin videon iskanci, saina d'orashi a duk wata kafar sada zumunta da kika sani wahil azim.

A fusace ta juyo tace " sake shin wa duniya mana sai me ai kaima kana cikin video kaga kai kuma saika zama namijin Bahaushe musulmi d'an arewa cin Nigeria na farko da zai fara yin videon iskanci.

Dariya yayi sosai harda rik'e ciki yace " da alama baki kalli videon sosai ba, ai fuskata bata fito ba kwata-kwata sai da na saka protection na rufe fuskata tsaf, takowa tayi gabanshi gaf da gaf har suna iya jiyo numfashin juna tace " idan fuskarka bata fito ba ai tsiraicinka ya fito.

Kafad'a ya d'age had'i da d'age gira d'aya yace " sai me dan tsiraici na ya fito?

" Idan zaki bi duniya rataye da Al-Qur'ani kina cewa nine babu me yadda saboda babu wanda yasan tsiraici na, k'asa-k'asa yayi da murya yakai bakinshi saitin kunnenta yace " sai ke kad'ai kika san tsiraici na ke kikayi disvirgin d'ina, ya k'areshe maganar had'i da kashe mata ido d'aya.

"Idan na fito na k'aryataki Ina da damar da zanyi shari'a dake nace kin b'ata min suna akan wannan kina iya zuwa gidan yari tunda baki da wata hujjar da zata tabbatarwa da duniya cewar ni d'in ne da gaske, yayi maganar yana zagayata.

Durkushewa tayi a k'asa had'i da fashewa da wani irin rikitaccen kuka tana fad'in " wannan wacce irin bak'ar k'addara ce?

" Meyasa sai ni ta fad'awa?

" Me nayi, wanne laifin na aikata?

" Allah na tuba ka yafe min, Astagfirullah Astagfirullah na wa'itubi alaik, na tuba ya Ubangiji ka yafe min idan wani laifin na aikata.

Kneel down tayi ta durk'usa bisa gwiwowinta ta had'e hannunta tana fad'in " kayi hak'uri dan zatin Allah kabarni, kayi min hak'uri idan nayi maka wani laifi bisa rashin sani.

Baki ya tab'e yace " kidaina wahalar da kanki wajen bani hak'uri dan idan duniya zata tashi idan sama da k'asa zasu had'u babu mai rabani dake a wannan lokacin a wancan lokacin dai an rabani dake but not now Deeyanah babu mahaluk'in daya isa ya rabani dake a wannan karon, ke tawace ni kad'ai Deeyanah.

Cikin matsanancin kuka tace " me nayi maka Ajlaal?

"Meyasa kake azabatar dani ta wannan hanyar why Ajlaal?

" Love!

"It's Love Deeyanah.

"Ina sanki fiye da kowa da komai, zan iya kashe duk wanda yace zai shigo gabana akanki, kamar yadda kika ji nace zan iya kashe kowa akanki Ina nufin kowa ban cire miki kowa ba, a yadda nake ji akanki zan iya yak'ar duniya da abinda ke cikinta akanki, Ina sanki fiye da kaina zan iya bada raina akanki.

"So hauka ne Ajlaal!?

"Dan kana so na saika tarwatsa min gobe na?

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now