52

337 20 2
                                        

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

5️⃣2️⃣

Tsaye ta iske shi a harabar gida da sauran family duk anyi cirko-cirko ana tunnin sace ta akayi, tana shiga duk ayo kanta tana wani irin kuka ta fad'a jikin Ammi, " lafiya meya faru?

"Meya same ki?

"Ammi.....! ta fad'a da wani irin kuka me k'arfi dake fitowa daga can k'ark'ashin zuciyarta so take tayi magana amma kuka ya hanata, duk sunyi tsaye kanta cikin damuwa da tashin hankali, "kaita gida mayi magana daga baya, Abbi ya fad'a yana kallan Deen, kanshi ya d'aga alamar to kana ya sunkuya ya d'auke ta cak yabar wajen da ita, in banda kallanshi da kuka babu abinda take yi, saman gado ya shinfid'eta yaja mata bargo ya rufe ta zuwa k'irjinta ya juya zai fita caraf tayi ta rik'e hannunshi cikin sheshsheka tace " d....a...n A.....ll...ah kar...ka tafi.....ka zau....na dani na.....wa....ni, d'an....lo...ka...ci, guntun murmushi yayi mata tare da zame hannunshi daga cikin nata kana ya zauna saman sofar dake d'akin yana danna waya, idanuwanta kanshi ta kasa d'auke ido daga kanshi, yana sane da kallan da take yi mishi  while yana jiyo sautin kukanta dake fita a hankali a haka bacci ya kashe shi, ita kam bata runtsa ba kwana tayi tana tunanin irin soyayyar da ahalinta keyi mata amma ta saka musu da bak'in batulci.

Wasa-wasa abu ya wace sekanni, awanni, satittika har aka kai wata d'aya, duk yadda Ajlaal ke tunanin  abun ya wuce nan dan babu yadda bayyi da ita ba amma tak'i sake yarda dashi, ya rasa yadda zayyi da ita abun duniya ya tattaru yayi mishi yawa.

A b'angaren Deeyanah kuwa ta koma kamar tsohuwar data gaji da duniya, bata iya cin komai sai ruwan tea da drinks shima ba sosai ba, ta rame ta k'ek'ashe bata da aiki sai kuka, tun babu wanda ya sani har kowa ya sani, babu irin tambayar duniyar da ba'ayi mata ba akan meke damunta kullum amsarta d'aya ce babu komai, duk gida an tattara an zuba mata ido, ga bp d'inta da yayi mugun hawa.

Tana kwance saman gado, aka kira sallar la'asar ta mik'e da d'an hanzari jiri ya d'ebeta tayi baya ta fad'a saman gadon d'an shuuuuu taji cikin kanta da kunnenta, zama tayi saman gadon tana ganin komai bibbiyu yana juya mata, bango ta dafe ta mik'e tana bin bangon tana tafiya while tana gani dishi-dishi jiri na d'ibarta har takai k'ofar shiga bathroom d'in ta d'aga k'afarta zata shiga bathroom d'in jirin ya d'ebe ta, ta fad'i daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba, babu wanda ya shigo har magariba, Deedee ne ya shigo wajenta, ganinta a kwance k'ofar bathroom yasa shi k'arasawa wajenta ya durk'usa gabanta yana girgizata tare da kiran sunanta,  jin shiru yasa shi fita da gudu, d'akin Deen ya shiga yana haki, " Daddy kazo Momy ta fad'i tak'i tashi.

Jikinshi na rawa ya fito da d'an gudu, " Deeyanah ! ya fad'a yana jijjiga ta amma shiru, sai jini daya fara fitowa daga hancinta kad'an-kad'an, jikinshi na b'ari ya sumgume ta sai asibitin dake nan cikin estate d'insu, anyi mata gwaje-gwaje da aune-aune inda aka gano zuciyarta ta soma kumbura.

Gumi likitin ya goge kana ya soma magana yana kallan Abbi da Babah sa Deen da yayyan Deeyanah yace " wai meke damun yarinyar nan ne?

"Gaskiya ya kamata ku bincika kusan damuwarta da kuma matsalarta dan abun ya fara girma gaskiya, yarinya k'arama da k'ananun shekaru amma ace tana tattare da irin wannan damuwar dake neman haifar mata da bugawar zuciya, a zahirin gaskiya abun yafi k'arfi shekarunta dan haka ya kamata kusa ido akan wasu abubuwa fa, da fari bawan jini yanzu kuma kumburin zuciya?

Kallan da Abbi yayi mishi ne ya fahimtar dashi shi ake zargi akan damuwarta, dakyar ya iya had'iye yawun daya tsaya mishi tsakanin baki da mak'ogwaro, likitin ya d'ora da " a halin yanzu takai matakin da dole sai mun d'orata akan magani ta fara shan maganin, kuma koda ta fara shan maganin dole fa sai an saka ido kuma anyi mata maganin damuwarta in ba haka ba komai yana iya faruwa at any movement so take note please.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now