*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh2️⃣9️⃣
Bata farka ba sai wajen k'arfe biyu na dare sosai kanta yayi mata mugun nauyi, a wahalce ta yunk'ura zata tashi zaune, saurin tallafe ta Ammi tayi tana fad'in "sannu Deeyanah, dakyar ta iya d'aga idonta da yayi mata nauyi ta kalli Ammi, da taimakon Ammi ta tashi zaune, sai a lokacin ta fahimci a asibiti take, shiru tayi tana k'ok'arin tuna abinda ya faru, tasan dai mararta ta rik'e.
"Ince dai babu inda zaki biya ko?
"Dan nayi amfani da abortion cream a jikin penis d'ina a koyaushe wannan abun na jikinki yana iya fita dan bazan iya jurewa sex dake da cikin wani a jikinki ba.
Maganganun Ajlaal suka dawo mata saurin shafa cikinta tayi taji wayau babu alamun komai, kanta ne ya kulle ta kasa fahimtar komai dan haka ta bud'e baki dakyar tace " Ammi meya kawo ni asibiti?
Ammi tsaye gaban fridge tana had'a mata tea ta juyo ta nufo ta d'auke da kofin tea a hannunta ta mik'a mata tana fad'in " b'ari kikayi mun rasa babyn cikinki.
Ido ta runtse da k'arfi hawaye na gangarowa saman kuncinta, koda yace mata ya shafa abortion cream bata yarda ba, "dama rashin imanin " Ajlaal har ya kai haka?
"Dama da gaske zai iya aikata duk abinda yake fad'ar zai aikata?
Bata tab'a yarda zai iya aikata abubuwan rashin imanin dayake fad'ar zai aikata ba, wani irin mugun tsoronshi taji ya shigeta lokaci d'aya, yadda kasan wacce ake kad'awa gangi haka jikinta ya d'auki rawa da kerrrrma kaf! Kaf! Kaf! Kamar me farfad'iya.
Kenan dayake cewa zai kashe iyayenta da Deen dama gaba d'aya zuri'arsu da gaske yake!?
A fili ta furta "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga uku.
"Kai Deeyanah sai kace ba musulma ba miye dan kin rasa d'an da baki haifa ba kike kin shiga uku!?
"Da kin san zaki samu Allah ya baki?
Bama tasan abinda Ammi ke fad'a ba tadai ga Ammi tsaye kanta bakinta na motsi, amma duk fad'an da takeyi babu abinda ta iya fahimta.
Tana cikin wannan halin wayarta tayi vibrating alamar shigowar text dan tuni ta mayar da wayarta vibrate ko kiranta akayi sai dai tayi Vibrating kawai, hannunta na rawa saboda saban tsoranshi d'aya shigeta ta d'auki wayar ta duba sak'on.
"Congratulations to me! For winning karki damu kinji Baby dakin warke zan bani wani cikin I love you my life.
Wata irin juyawa taji kanta yanayi ta zame ta kwanta, ita tama rasa tunanin da zatayi ta rasa mafita, to kodai ta kashe auren Deen inyaso taje ta auri Ajlaal d'in?
Sai dai kuma tasan muddin tayi haka ba ita ba iyayenta har a tashi duniya, haka idan iyayenta suka k'i amincewa aurenta da Ajlaal tasan zai iya kashe su, to idan kuma bata aure shi ba haka zata k'arar da rayuwarta cikin tsoro da fargaba suna aikata zinace-zinace?
Idan ta bijire tak'i aurenshi kota k'i bashi kanta tasan videon nan zai saki, mutuncin iyayenta, mutuncin gidansu, sunanta dana ahalinta zai b'aci har abada, haka zalika idan tace zata fad'awa ahalinta halin da ake ciki yayi rantsuwa sayya saki videon kuma ya k'arar da gaba d'aya zuri'arsu, wannan shi ake kira gaba kura baya zaki, ganin ta kasa cimma matsaya ga kanta na barazanar tarwatsewa yasata komawa ta kwanta lamo.
![](https://img.wattpad.com/cover/335142470-288-k870181.jpg)
YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...