2

719 30 3
                                    

BAK'AR SHUKA...!

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

2️⃣

DEEN...

D'a ne ga Abdhulhakeem da Halimatu yana da yayye, maza biyu Abdhulrasheed da Abdulraheem, sai k'anwarsa Abeerah, yayyan Deen suke auran yayyan Deeyanah,
Deen yana d'aya daga cikin yaran da Ammah (Aina'u ) ta rik'e, kuma har gobe yana gidan, sosai Ammah da Babah (Abdhul Jalal) ke ji dashi.

Deen yaro ne kamili nutsutstse, mai hankali, shi mutum ne da yawan magana bai dameshi ba, yakance " sai mutum nada abin fada yake magana, shiko bai da abin fada,
haka yawan magana da surutu yana sawa ayi karya, karya kuma tana kawo raini, shi kuma mutum ne da bai kaunar raini, duk yadda kuke dashi kace zaka rainashi yanzu zai kawo k'arshen alak'arku, ko yayyanshi da abokanshi suna girmamashi,
bai cika yawan dariya ba dan ko yayi bata yi mishi kyau inji Deeyanah, haka ya cika takura mata musamman idan zata fita, tayi kwalliya kota yafa mayafi,
kowa a gidan ya gane yana san Deeyanah, haka itama tana sanshi, k'ifad'i irin nashi ya hana ya sanar mata, koya nasarwa da iyayansu.

Yana zaune a parlour saman sofa ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana karanta jarida, saboda ta tsokaneshi ta ci kwalliya kamar zata gidan biki,
ta yafa siririn mayafi, dan yadda yake nuna kishi a kanta yana burgeta sosai, tasha kiran mazan ajinsu suzo gidan tayi kamar tana zance,
yadda yake fututtukewa yana fada yana bata sha'awa, 'yan gidan suyi tayi mishi dariya, ta gabanshi tazo zata wuce tana gyara mayafinta, had'i da satar kallanshi,
baki ta turo ganin harta kai k'ofa amma baice mata komai ba, baima kalli inda take ba, jikinta a sanyaye zata fice, taji yace " ke!,
cak ta tsaya had'i da yin murmushi " baki san mutuncin kanki bane zaki fita haka tsirara?

Kamar gaske ta juya tana had'e fuska kamar yadda tashi take koyaushe, idonshi kan jaridar dayake karantawa, cikin yatsina fuska tace " tsirara fa kace?

Bayyi mata magana ba, ta d'ora da cewa " kalli fa ka gani da kaya a jiki na, batare daya kalli inda take ba, yace " idan aka barki zaki iya fita haka?

"Sosai kuwa, "jeki, yace a tak'aice, da sauri ta juya zata fice, tana k'ara taka takalmin k'afarta da k'arfi yana k'ara k'as-k'as,
idonshi ya runtse ya bud'e, tare da aje jaridar, yana jin k'arar takun takalminta har cikin kanshi, ga turaren data fesa mai bala'in k'amshi,
ya san halin mazan yanzu, zasu takurata kodan takunta mai d'aukar hankali, ko baka san tana zuwa ba k'amshinta da k'arar takunta zasu jawo hankalinka gareta,
kamar yadda tun kafin ta k'araso k'amshinta ya ziyarceshi, takunta kuwa tare suke dokawa da zuciyarshi, ganin ta kusa fita yasashi saurin cewa " please mana Deeyanah!,
saurin jiyowa tayi ta kafeshi da ido, yadda yayi magana yana huda zuciyarta kamar kifiya, kallan da tayi mishi yasashi ankarewa ya saki layi,
fuska ya tsuke had'i da daka mata tsawa yana fad'in " ke! baki da hankali ne?

" Dalla koma ki wanke fuskarki, ki saka hijab ki kuma canja takalmi, baki ta turo tana diddira k'afa tace " I'm 19yrs fa Yaya,
ina jami'a in 100 level in saka hijab haba Yaya is on...... tsawar daya daka mata yasa bata k'arasa maganarta ba, tayi ciki da gudu, yabi bayanta da kallo yana murmushi had'i da shafa kanshi
" wow! Wonder shall never end Son! yau kai ke murmushi da kanka?

Kanshi ya shafa yana rusunawa yace " ina kwana Babah?

" Lafiya lau, Alhamdulillah Romeo, murmushi yayi a karo na biyu yana shafa kanshi batare dayace komai ba, " hmmm yadai kamata ka magantu Son! wannan kame-kamen ba kai maka zayyi ba, ka fito ka sanar da ita kana santa, kar wani yayi maka kutse ayi maka shigar sauri,
" Ah haba Babah waya isa?

"Waya isa ya shiga tsanina da Manassah bayan had'in Allah ne mu, mutuwa kad'ai zata iya rabamu, murmushi Babah yayi yana rik'o Deen,
" kadai fad'a mata saboda yanayin rayuwa da zuciya, " zan sanar da ita in sha Allah Babah, so nake saina tafi course d'innan America,
" Allah ya tabbatar da alkhairi, " Amin ya Allah.

Da yamma bayan sun tashi lectures k'awarta *RALEEYA* ta kawota har gida, fuskarta d'auke da murmushi ta fito daga motar,
tana juyowa idanuwansu suka sark'e cikin na juna, yana tsaye ya hard'e hannuwanshi a k'irji, ya kafeta da ido, guntun murmushi tayi tana cije lips ta d'agawa Raleeya hannu had'i da kashe murya tace " bye my sai gobe I will miss you, tabi bayan motar da kallo tana murmushi, har motar ta b'ace tana d'aga mata hannu,
kasancewar motar tit ce yasa Deen bai gane macece a motar ba, take idanuwanshi sukayi jajir, jijiyoyin kanshi suka fito, ganin yanayinshi yasata tsorata,
ta rab'a zata wuce ta gefenshi, ya fincikota da iya k'arfinshi yana fad'in " uban waye ya kawo ki?

Bakinta na rawa, dan tayi muguwar tsorata tace " Raleeya ce, a zafafe yace " karya kike yi, motar Raleeyan ce ban sani ba, " wallahi Yaya itace, " zaki fad'a min wanne shegen k'aton banzan ne ya kawoki ko kuwa?

Yayi maganar yana girgizata da k'arfi, sosai inda ya rik'e yake yi mata zafi ji take tamkar yana b'alla mata k'asusuwa, kuka na k'ok'arin kwace mata tace " wallahi Yaya itace, " yaushe Raleeya ta canja mota?

Ya fad'a ranshi na k'ara b'aci dan sosai ya tsani k'arya, " jij....ji....jiya, tayi maganar a rarrabe kamar me kayan magana,
bayyi magana ba ya bud'e mota ya dannata ciki, ya zagaya ya shiga, yayiwa motar key ya fisgeta da gudu, " bani wayarki, hannunta na kerrrrma ta mik'a mishi,
dukda da gaskiyarta ta had'a uban gumi, hausawa na cewa mara gaskiya ko a ruwa yayi jib'i yau ita da gaskiyarta take yin gumin,
" idan har ba gaskiya bane sai ranki ya b'aci, ya k'arasa maganar yanayin parking a k'ofar gidansu Raleeya, sosai tayi mamakin yadda akayi yasan gidansu Raleeya, dukda tana da gaskiya bai hana cikinta murd'awa ba,
motar ya bud'e ya zagaya ya bud'e mata ya rik'o hannunta, sau biyu ya buga get d'in me gadi ya bud'e 'yar k'aramar k'ofa da nufin tambayar waye,
ganin Deeyanah yasashi washe baki yana fad'in " ah ah Deeyanah ce?

Bata iya amsa mishi ba saboda halin da take ciki, fuskar Deen a tamke yacewa me gadin " yi man magana da Raleeya, " to to, amma da kun shigo daga ciki,
ba musu ya jata suka shiga cikin dama neman damar shiga yake, suna shiga harabar gidan yaga motar, a fili ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido,
dan harga Allah yayi zaton namiji ne, wato tana sani tayi hakan, tayi ne danta tsokane ni, bai jira me gadi da Raleeya sun fito ba, yaja hannunta suka fita,
tafiya sukeyi shiru babu wanda yacewa wani k'ala, sai sheshshekar kukanta dake tashi, abin yayi mata ciwo, wai ita Deen ke zargi, why kake zargi na, why?

Tayi maganar cikin ranta, abinda bata sani ba, maganar ta fito fili ya ji, " kiyi hak'uri, ya furta a hankali, kamar daga sama taji Deen yana bata hak'uri,
cike da mamaki ta kalleshi, bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, amma ta basar ta cigaba da matsar hawaye tana shashsheka, rolling daradaran idanuwanshi ya juya had'i da kafe ta dasu yace " nace kiyi hak'uri ko?

Baki ta turo batare data ce mishi komai ba, yana yin parking ta bud'e motar ta fice ita a dole anyi mata laifi tana fushi, yabi bayanta da kallo yana murmushi.

Dr Deen cikekken likitan kwakwalwa ne, yayi karatunshi a ABU Zaria, kafin daga baya ya tafi Germany yayi masters dinshi acan, nan da kwana biyar zai tafi America yin wani course,
hankalinshi a tashe yake sosai na barin Deeyanah da zayyi, ga bai sanar mata yana santa ba, ya dai k'uduri niyyar da kafin ya dawo zai sanar da ita, yana da tabbacin bazai samu matsala da ita ba, da izinin Allah...........

Kwanaki biyar d'in nan jinsu suke kamar seconds biyar dan basu tab'a ganin gudun lokacin irin wannan ba, dukkansu sun shiga cikin mawuyacin yanayi,
duk Wanda ka kalla cikinsu kasan yana cikin damuwa, 'yan gidan sai dariya suke yi musu ciki-ciki ana tsokanarsu, lokaci ba wuya a wajen Allah, yauce ranar tafiyar Deen,
yadda sukaga rana haka sukaga dare, ko gyangyadi cikinsu babu wanda yayi, ya tsaf ya fito yana janye da trolley, jinkinshi sanye da man material shara-shara,
kayan sun karb'e shi, abinka da dogo fari me kyau, ganin gaba d'aya ahalinsu a harabar gidan yasashi k'ak'aro murmushin dole ya sanya a saman fuskarshi,
amma kallo d'aya zakayi mishi kasan a iya saman leb'enshi murmushin ya tsaya bai kai zuciya ba, ido ya fara wulk'itawa yana neman ta inda zai ganota, amma ko alamarta babu.

~JIDDARH~

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now