44

243 11 0
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

4️⃣4️⃣

Dariya Ajlaal yayi harda dukan table d'in dake gabanshi yace " ke dai kika fad'a ni ba ruwa na, baki na da goro, dogon tsoki mstwwwwww taja had'i da cewa " Allah kuwa sumi-sumi dashi kamar na Allah ashe mutumin banza ne d'an cikiyar sharri, inba cikiyar sharri ba meye nabin bayana fisabilillahi?

"Yanzu ya jawo min zuwa saloon d'in da banyi niyya ba, zayyi magana ta tsaya cak had'i da cewa " wai tsaya ma tayaya akayi kasan Deen yana bi na a baya?

"Wait! Wait! Karka ce min yadda kake bibiyata shima haka kake bibiyarshi?

Cikin basarwa yace " koma dai meye ba gashi yayi miki amfani ba, "ashe ma ni yayiwa amfani?

"Ah to wa yayiwa?

"Ni dai kin san babu uban da nake jin tsoro ko a gabanshi kika d'aga min cinya zan shiga wallahi, ido ta waro kamar tana gabanshi tace " a gabanshi fa.

"Wallahi am telling you, shi d'in banza ma, tun yi yana da sauk'i zan kwasheki tsaf, tab! ina ruwa na?

Ajiyar zuciya ta sauke had'i da cewa " ah lalle! suna waya har aka wanke mata k'afa da hannu aka gyara mata gashin kanta, yayinda har lokacin Deen na zaune cikin mota yana jiranta, bata bar wajen ba sai yamma lik'is.

Zaune ta iske shi saman sofa tayi mishi kallan gefen ido had'i da jan tsaki cikin ranta, ta wuce yabi bayanta da kallo.

Bayan sati d'aya, sosai rigima ta b'arke tsakanin Ajlaal da Deeyanah dan ya fututtuke idan bata zo ba shi zai zo dole, hannunta rik'e da tea cup ta fito daga kitchen "haba mana Ajlaal kana ganin fa halin da ake ciki, ko so kake a samu matsala asirinmu ya tonu?

"Asirin mu ya tonu ko kuma asirinki ya tonu?

"Naji koma meye ni dai kayi hak'uri ka d'an bari a alafa, " a lafi me?

"Wallahi hak'uri na ya k'are bazan iya ba, sati d'aya kenan fa bamuyi sex ba, zatayi magana ya katse ta da fad'in " kinga idan zaki zo ki zo idan kuma bazaki zo ba zaki ganni a gidan wallahi, bai bari tayi magana ba ya kashe wayar, wayar tabi da kallo cikin ranta tana tunanin mafita.

Dole ba yadda zatayi ta shirya ta fita dan bata san Ajlaal yazo gidan gudun wata rana kar a samu akasi, sai da ta tabbatar ya fita kana ta fito itama, tana gaf da isa gidan ya kirata a waya, " kai ka fiya gajen hak'uri wallahi gani nan gaf da gidan fa.

"Ba wannan ba, Deen yana biye dake a baya, zata taka birki yayi saurin cewa " karki tsaya ki cigaba da tafiya, zamu wahalar dashi, suna waya tana tuk'i while Deen na biye da ita a baya, idan tabi tanan sai ta b'ille can, haka taita wahalar dashi kusan awa uku, wata irin shammata tayi mishi ta b'ace mishi b'at a cikin motoci, ya nemeta sama ko k'asa ya rasa, ranshi a matuk'ar b'ace ya juya ya koma gida, ko mukullan motar bai cire daga jikin motar ba ya fito, yana cika yana batsewa yadda kasan zai fashe ya shiga part d'in su, ba k'aramin mamakin ganin zaune a falo tana kallo yayi ba.

Sosai kanshi yayi masifar kullewa, yama rasa ta ina zai fara, kamar zayyi magana sai kuma ya fasa ya shige ciki ya barta, tabi bayanshi da kallo tana dariya k'asa.

"Gobe ki sake fitowa zamu sake raina mishi hankali, tunda haka ya zab'a zamuyi ta wahalar dashi muna tamola dashi a titi, ni ne fa, nine Ajlaal har ya isa ya gwara kai na, wane shi maza bisa kanshi wallahi, waya suka cigaba dayi har dare kafin suka kashe.

Washe gari da safe wajen k'arfe 11:30am ta shirya cikin riga da siket na lace ta d'ora hijab akai, sai da ta tabbatar yana falo kana ta fito, yayinda kunnenta ke manne da bluetooth wireless, fuskarta wasai d'auke da fara'a tace " ina kwana yaya, dakyar ya bud'i baki ya amsa da " lafiya, ga breakfast d'inka can akan dinning na gama, "ok, kawai yace a tak'aice, tana kanne dariya ta fice, bai tambaye ta inda zata ba, hakan ya bata tabbacin zai biyo bayanta, d'aya daga cikin motocin gidan ta shiga Elantra dayake basa ware motoci kowa hawan kowacce yake yi, duk wacce yiwa mutum kawai hawa zayyi.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now