32

330 19 2
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*
   

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

3️⃣2️⃣

Mik'ewa yayi da ita a jikinshi ya shiga bathroom ya cika musu kwamin wanka da ruwa suka shiga, sai da suka b'ata lokaci sosai wajen tab'e-tab'e da latse-latsen juna gami da watse-watsen ruwa sannan yayi mata wankan tas ya sillota a towel ya fito d'auke da ita a hannunshi kamar jaririya.

Har ya gama shirya ta tana zuba mishi sangarta da shagwab'a, ya saka mata takalmi suka fita, Amala delight suka nufa acan d'imma da kanshi ya bata abincin a baki, kafin suka nufi wani k'aton mall dake kan zaria road ta jibgi k'anan kayan sawa sosai da duk abinda zata buk'ata, ya biya suka dawo gida, bedroom guda ya ware mata nata na kanta a cikin gidan, tare suka shirya kayan a cikin wardrobe.

" Bacci nake ji, ta fad'a cikin salon d'aukar hankali.

Yayi murmushi had'i da mik'ewa ya d'auke ta sai kan bed yana fad'in " bacci kodai abun ne ke motsi yana buk'atar a d'an, ya k'arashe maganar had'i da kashe mata ido d'aya, " sai kace wata harija, yanzu fa muka gama ai sai nace ba lafiya ba.

"Kinga imma shine ki fito kiyi bayani kar ki cuci kanki ni dai kin San bana gajiya namijin gaske ne.

"In shi d'inne me zai hana ni fad'a!?

"Kaga ni kashe min light, light d'in ya kashe ya dawo zai kwanta ta kalle shi tace " kazo ka hanani bacci ko?

"Nop wane ni, baccin dai nima zanyi, " tam naji amma banda 'yan tab'e-tab'e, "okay Ma'am, yace had'i da rungumo ta jikinshi tsam kamar wani zai kwace mishi ita, suka tsunduma duniyar baccinsu cikin kwanciyar hankali.

Basu tashi ba sai 5:30pm na rana a gurguje ta mik'e ta shirya ta fice ko sallah bata tsaya tayi ba, har bakin motarta ya rakata yayi mata kiss a goshi, yana tsaye harta fita, dayake get d'in me control da remote ne, da remote ya rufe, ya koma ciki.

A harabar Estate ta hangoshi yana niyyar shiga mota, ganin ta shigo ya sashi d'an dakatawa ya fasa shiga motar, ya zuba mata ido yana yi maka kallan tuhuma yace " daga ina kike?

Tana k'ok'arin had'a nutsuwarta tace " saloon!

Ido ya tsareta dashi yana karantar yanayinta, kanta ta sunkuyar dan kallan da yake yi mata yana neman rikitata ta fad'i abinda ba shi kenan ba, kanshi ya kawar had'i da shiga motar yana maimaita a'uzubiyya cikin ranshi saboda abinda shaid'ai ke bijiro mishi dashi.

D'an siririn tsaki taja tana watsawa motar dayake ciki harara ta wuce gidan, "Momy kina ina tun d'azu nake nemanki.

Murmushi tayi tare da shafa kanshi tace " d'an Ammi kasuwa naje, " kacuwa! To Momy ina chocolate d'ina, hannu ta sanya cikin jakarta ta d'auko chocolate harta mik'a mishi sai wani tunani yazo ranta.

"Gashi ki kaiwa Deedee!.

Maganar Ajlaal ta dawo mata, tasan Ajlaal baya k'aunar ahalinta kaf musamman Deen, d'aukar  Deedee tayi ta isa bakin fridge ta bud'e ta d'auko Chocolate ta bashi, ya amsa tare da cewa "thank you Mom!, ya soma k'ok'arin sakkowa ta direshi tana dariya tace " an samu abinda ake so za'a gudu wajen Ammu.

Wayar hannunta ta soma haske tayi murmushi had'i dayin picking tace " Noor Hayati ya akayi!?

Ajlaal yace " meyasa kika fasa bashi chocolate d'in dana siya mishi?

'Yar dariya tayi kana tace " haka nan kawai, "hmmm kedai kika sani, "bari nayi sallah zan kira ka, "ok, had'i da kashe wayar.

***********************************

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now