*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh4️⃣1️⃣
Tasha kwalliya duk da bamai yawa bace, simple make up tayi, jikinta sanye da doguwar rigar bubu ta leshi, ta kashe d'aurin d'an kwalli, fuskarta d'auke da yalwataccen murmushi ta mik'e ta tare shi, " sannu da zuwa me gida ran gida, 'yar hararar wasa ya jefa mata yana mik'a mata jakar hannunshi yace " ai kece me gidan yanzu dan kin zama hukuma sai rarrashi, " wace ni ranka ya dad'e, ta fad'a tana shigar da jikinta cikin jikinshi, hannunshi ya saka ya rungume ta tsam yana mayar da numfashi, a wahalce yace " nayi kewarki sosai k'aunata.
Dariya tayi ta d'an zame jikinta daga nashi, yayi saurin mayar da ita jikinshi yana fad'in " ki barni a haka na samu nutsuwar dana gaza samu tsayin lokaci, murmushi tayi me zurfi dayasa side dimples d'inta lotsawa ta zame jikinta daga nashi a hankali tana fad'in " kayi wanka kaci abinci ka huta tukunna, ta k'arasa maganar tana barin wajen, yayi saurin bin bayanta, a tsakiyar d'akin ya cimma ta, ya mik'a hannu ya jawota jikinshi ya mannata da k'irjinshi had'i da jan dogon siririn hancinta ya jefa idonshi cikin nata yana kallanta eyeball to eyeball, wani irin shu'umin kallo da murmushi ta jefa mishi mai narkar da mutum, " Ya Allah! Yace yana lumshe idonshi, ya bud'e idon ya sake kallanta, irin kallan nan nan k'asan ido yace " kina neman zauta ni Deeyanah.
Dariya ta sanya harda rufe baki tace " ko kuma mu zauta juna ba, zayyi magana ta sanya hannunta a k'irjinshi ta tura shi baya in a romantic way har ta kaishi cikin bathroom tace " Yallab'ai ka fara yin wanka, ta juya zata bar wajen ya rik'o k'ugunta, ya dawo da ita suka fuskanci juna yace " ki bari nayi wankan me dalili mana, ya k'arasa maganar had'i da kashe mata ido d'aya, sai da k'irjinta ya kusa fad'owa saboda tsabar tsoratar da tayi danta gane abinda yake nufi, tasan dama dole sai haka ta faru tun da shi ba k'arfe bane, da ranshi da lafiyarshi dole zai buk'aci mace a tsayin lokacin nan, kashe din Ajlaal ya fad'o mata.
"Ba Deen kad'ai ba Deeyanah, wallahi zan iya k'arar da duniya akanki, ba Ina nufin iya ahalinki kad'ai ba, ina nufin kowa dake cikin duniya, kinga har da nawa iyayen da ahalin duk suna ciki, ki kula sosai in ba haka ba zaki jawo yak'in duniya na k'arshe, dan a yadda nake jina nafi hitila bala'i, daga ranar da kika sallamawa Deen kanki kika bashi kanki wallahi kowa ya tsaya mishi bai k'ara kwana duniya.
Cikin kuka tace " haha Ajlaal shifa mijina ne, sadaki na ya biya fa, ai da tausayin rai duk wannan lokacin bai kusanci matarshi ta sunna ba ina kake san yakai buk'atarshi?
"Ina kake san yaje ya zazzage wutar sha'awar dake addabarshi?
"Ko so kake yi shima ya fad'a halaka kamar yadda muka fad'a?
Kafad'a ya d'age irin ko'a jikinshi d'in nan yace " shi yasan inda zai kai ta, kuma da kike cewa mijinki ne, sadaki ya biya, ni so nawa nace miki ki bani dama na zama mijin naki na biya sadakin naki amma kika k'i?
"Wai ka hauka ce ne Ajlaal?
"Hauka kake yi kome da kake cewa na aure ka, ina ka tab'a ganin anyi aure akan aure?
" Eh! Ina hauka Deeyanah, na hauka ce akanki sanki, ya fad'a cikin hargowa ya d'ora da " idan kin haramta abinda Allah ya halatta a tsakaninmu ai gashi nan kin halatta mana abinda Allah ya haramta mana, cikin mamaki hawaye nabin fuskarta tace " mena halatta mana d'in?
"Zina Deeyanah, kin hana muyi aure amma gashi kin bari munata zina, " duk abinda zaka ce kaje kace amma saina bawa Deen kaina, a haukace ya damk'o gashin kanta, idanunshi duk sun firfito waje saboda bala'i, bakinshi har kumfa yake yace " kije ki bashi kan naki, amma wallahi ki sani kafin alfijir ya keto na k'arar da duk mahaluk'in dake cikin estate d'in nan, " so kake ya fara zargin akwai wani abu?

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
EspiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...