*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh3️⃣8️⃣
Suna zaune a babban falon gidan ana kallon tsohon film d'in Marigayi Rabilu Musa d'an Ibro mai suna Namamajo su Abbi sai dariya suke yi, Deeyanah na zaune kan dinning tana shan tea while wayarta na hannunta tana chart Deedee ya rugo da gudu wajen " Momy dan ta, murmushi tayi mishi had'i da cewa " da zafi sosai, " to Momy bani wayanki nayi game, sai da gabanta ya fad'i dan chart take yi Ajlaal, tayi murmushin yak'e tace " a'a bazan baka wayata ba jeka wajen Abbi ko Ammi su baka tasu dama da ita ka saba yin game d'in, "Momy ni taki nake so, ya fad'a yana kwab'e fuska zayyi kuka,
" wayata babu game ko d'aya Deedee kaje Ammu ta baka tata kayi, kuka ya saka harda buga k'ofa irin na shagwabb'un yaran masu kud'i yace " ni dai taki nake so, yayi maganar hannunshi kan wayarta, bata san sanda ta d'auke shi da mari ba, had'i da tura shi baya ya fad'i ba, dai-dai akan idon Ammi.Tasowa tayi cikin b'acin rai tace " me yayi da zaki dake shi?
Yaran da tsakaninki dashi haihuwa ce kawai, sai dai ki kalleshi da ido bayan nan wata tsiyar kike tsinana mishi?
" Ammu damu na yayi nace mishi ya bari yak'i bari, cikin kuka Deedee yace " waya nace ta bani nayi game fa, cikin masifa da bambami Ammi tace " wata tsiyar ce a cikin wayar taki da kike b'oyewa har haka?
"Daga yace ki bashi waya yayi game sai duka dan zalunci?
" Ya Isa haka dan Allah, Abbi ya fad'a idonshi kan Tv, "Alhaji na lura kwata-kwata baku kula da canjawar da yarinyar nan tayi ba, abubuwa take yi a nannad'e kamar munafuka, duk suffofin munafurci da rashin gaskiya sun bayyana a tattare da ita.
"Subhanallahi! Haba Aina'u meke damunki haka?
" 'Yarki ce fa ta cikinki kike fad'ar abinda ko wani kikaji zai fad'a akanta sai inda k'arfinki ya k'are, Babah ya fad'a ranshi a matuk'ar b'ace, zata sake yin magana ya d'aga hannu tare cewa " ki fad'i alkhairi ko kiyi shiru, bata sake magana ba ta watsawa Deeyanah harara had'i da d'aukar Deedee tabar wajen gaba d'aya.
Deeyanah ta mik'e hannunta rik'e da kofi zata mayar kitchen taji wayar Ammi ta d'auki sowa, bata kula ba tasa kai zata wuce kitchen tana gaf da shiga kitchen d'in ta jiyo Ammi na fad'in " lafiya k'alau Deeni ya nan wajen naku?
Bata san amsar daya bata ba ta shige kitchen d'in dan ita har mantawa take yi dashi idan ba irin haka ta kama ba, ko dalili yasa ta tunoshi, ta aje kofin tana shirin fitowa ta jiyo muryar Ammi na fad'in " ai har an sallamomu daga asibitin ma, duk da bata ji abinda yace mata ba amma ta fuskanta dan ko ba'a fad'a mata tasan cewa yayi waye bai da lafiya, mamaki k'arara a fuskar Ammi tace " ban gane waye bashi da lafiya ba?
Daga d'aya b'angaren kuwa mik'ewa yayi daga kwancen da yake yana fad'in " wallahi Ammi ban san wanda bashi da lafiya ba, bakinta bud'e tana kallan Deeyanah dake fitowa daga kitchen tace " matarka aka kwantar a asibiti har kwana biyar.
Cikin Mamaki yace " Deeyanah?
"Kana da wata matar ne bayan ita?
Ido Deeyanah ta runtse da k'arfi had'i da cije leb'enta na k'asa tace " wayyo Allah, dan ta tuno ranar da take chart a asibiti da Ammi tayi mata magana tace mata Deen take fad'awa bata da lafiya, kanta ta dafe tana tunanin k'aryar da zata yiwa Ammin dan gusar da hankalinta daga zargin wani abun na daban kamar yadda Ammu ke yi.
"A'a! Ammi kawai dai ina mamakin meya hanata sanar dani ne, itama Ammi tunowa tayi da Deeyanah tace mata ta fad'awa Deen, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tace " Allah ya rufa asiri to, ya amsa da " Amin ya Allah, suka kashe wayar, idon Ammi kanta tana jefawa Deeyanah kallan tuhuma tace " zo nan!
Yadda kasan tana tafiya akan iska haka ta nufo inda Ammi while gabanta na wata irin muguwar fad'uwa k'afuwanta har 'yar rawa suke yi mata, tana zuwa ta zube gaban Ammi, kunnenta ta rik'o ta murd'e sosai har dai da Deeyanah tayi k'ara ta runtse idanuwanta saboda zafin data ji, " fad'a kuka sake yi ko?
Ammi ta tambaye, " wash kunne na.
Ta fad'a kamar zatayi kuka, sassauta rik'on da tayiwa kunnen tayi tare da cewa " tambayarki nake yi baki bani amsa ba, "me kika ce Ammi ai banji ba, " nace fad'a kukayi?
Murmushi Deeyanah tayi danta samu hanyar renawa Ammi hankali, idan bata nunawa Ammi fad'an sukayi ba da matsala gwara ta fad'a mata sunyi fad'a zaifi, " Ammi to ai lefinshi ne, "kinga koma meye ya had'aku ba saina ji ba, bana kuma san kowa yaji balle har wani ya samu damar shiga tsakaninku, duk duniya babu wanda ya kaiku kusanci da juna, nina haifi Deen amma koni ban kaiki kusanci dashi ba, dan yanzu kin fini saninshi, kin san abinda ni ban isa in sani ba, kece mace kece zakifi saurin bada k'ofa da b'arakar da wani zai shiga tsakaninku dan haka kiyaye shi aure d'an hak'uri ne sai a cuce ka amma dole kana ji kana gani kayi kamar baka sani ba, muma nan da kika gammu duk hak'uri muke yi ana b'ata mana muna shanyewa ke mace kullum kece a k'asa, cikin sanyi ta d'agawa Ammi kai tare da cewa " in sha Allahu zan kiyaye, Ammi tayi murmushi had'i da sakin kunnen.
Duk abinda ke faruwa Ajlaal yana jinsu ta ware less earpiece d'in da Deeyanah ta sanya a kunnenta, dan matuk'ar basa tare da juna to suna manne da Bluetooth a kunnenta koyaushe suna aikin waya, " kaga dai Ammu ta fara zargin wani abu dole mud'an canja taku, dan ma Allah ya taimaka Ammi nada fahimta ai da abun ya k'ara cab'ewa, " kin ga kawai mu fito muyi musu bayani dama nina fara gajiya da wannan rayuwar b'oye-b'oyen da muke fa, idanuwanta waje ta zazzaro su tace " me zamu fad'a musu d'in?
Kamar baya san yin magana yace " muna san junanmu mana, kina so na, kuma ke kanki shaida ce akan irin san da nake yi, so why not bazamu fito da soyayyarmu fili dan muci ribarta ba, meye amfanin soyayya idan babu aure?
"Gaskiya ni dai a'a, a nutse kamar yana kallanta yace " meye a'a d'in Deeyanah?
"Bakya so na ne, ko bazaki iya aure na ba?
"Tab tashin hankali, ta fad'a tana fitar da numfashi kafin ta d'ora da "Ka rufa min asiri karma ka soma tunanin fito da maganar nan yanzu.
"Hmmm naji to!, tace " yauwa, tana sauke numfashi, sai da ya gyara zama yace " yaushe zamuje gidan Aunty me kayan mata mu siyo ne, d'an shiru tayi kafin tace " ka bari sai nan da next week dan yanzu ma idan nace zan fita baza'a barni ba cewa za'ayi daga dawowata daga asibiti zan fara fita, " ok ba damuwa Allah ya kaimu.
Shi ko Deen da tunani Ammi ta barshi, ya rasa meyake damun Deeyanah ya rasa dalilin sauyawarta da yawa haka, wasu lokutan yasha tambayar kanshi ko shine ya sauya ba ita ba, ko shine keda matsalar data sanya ta sauyawa dole, yasha bincikar kanshi ta fannoni da dama, yasha tambayar kanshi menene gazawarshi a matsayin miji ko uba amma ya rasa yana san ya sameta suyi magana face to face ta fahimta amma tak'i bashi dama balle lokaci, so da dama yana fahimtar idan ya kirata a waya tana amsa mishi a dak'ile kamar ma ya matsa mata shiyasa ya daina sai lokaci zuwa lokaci, Families sun sha tambayarshi yaushe zai dawo har ta kai ga sun fara matsa mishi kan ya dawo kusan kullum sai sunyi mishi maganar dawowa dai-dai da Deedee duk sanda zasuyi magana dashi sayya cewa " Daddy ka dawo Ina san ganinka I missed you, amma banda Deeyanah ko sau d'aya bata tab'a cewa ya dawo ba, bata tab'a nemanshi ba, bata tab'a cewa tayi kewarshi ko kewar wani abu nashi ba, ai ko irin maganganun sex da irin yadda tayi kewar sex da sauran su tayi mishi amma shiru, ganin tunanin bazai kai mishi ba ya sashi mik'ewa ya shiga bathroom ya d'auro alwala ya tada sallar mafila kasancewar su can tsakar dare ne.
****************************************
Ajlaal da Deeyanah kam likkafa taci gaba dan har cikin Niger suke shiga neman maganin mata, sune Sokota, Zamfara, Katsina kai har Neja k'asar nufawa suke tsallakawa sai dai duk inda zasu je a jirgi suke zuwa dan basa kwana ranar suke zuwa su dawo ranar, babu abinda suka aje sai sex su dai ayi sex kawai aji dad'i, kullum suna manne da juna kamar cingam, sun yiwa junansu mummunan sabo da juna ta yadda ko bacci basa iyawa sai rungume da juna.
Wannan kenan.....
Cigaban Labari.....

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...