*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh4️⃣6️⃣
Washe gari yana tashi yayi wanka ya shirya ya fice, minti 18 ne ya sada shi da gidansu, suna jin tsayawar mota suka fito harabar gidan, Mama nata rawar jikin ganinshi bakinta yak'i rufuwa, yayinda Abbah ke tsaye ya zuba mishi ido ganin yadda yayi wani fresh dashi, Mama na rik'e dashi har falo, kallanshi Abbah yayi sosai ya fitar da numfashi yace " Ajlaal!, yadda ya kira sunanshi ba k'aramin karya mishi zuciya yayi ba, a hankali ya d'ago ido ya zubawa Abbah ido.
"Ka sani babu da wani d'an sai kai, kai kad'ai Allah ya bamu balle idan babu kai muce akwai wani Wanda zai d'ebe mana kewa, gashi girma ya kamamu mu duka, lokacin da muka fi buk'atar ka a kusa damu, lokacin da muke buk'atar taimakonka, lokacin daya kamata ace ka karb'i ragamar dukiyata amma a lokacin ne zakayi nesa damu kayi watsi da al'amuranmu akan mace?
Kanshi k'asa yace " wallahi Abbah ba haka bane, " to yaya ne Ajlaal, ai ko babu amfanin da zakayi mana zamu so ganinka kusa damu.
" Kayi hak'uri in sha Allah zan gyara.
" Aikin kenan ayi hak'uri kullum abinda kake fad'a kenan.
" Wannan karon nayi maka alk'awarin zan rink'a zuwa kullum ina ganinku, " to mai zai hana ka dawo kusa damu gaba d'aya?
Kafin Ajlaal yayi magana Mama ta watsa mishi uwar harara tana fad'in " dan Allah karka dameshi, karka matsawa yaron nan ka barshi yaji dad'in lokacinshi ya morewa rayuwarshi haba, tsit Abbah yayi bai sake cewa komai ba, kallanta ta mayar ga Ajlaal cikin zak'uwa tace mishi " wacece yarinyar da kayi maganarta?
Cikin mamakin da Abbah ya kasa danneshi yace " unbelievable Ajlaal ne ke maganar mace?
"Wannan wace me sa'ar ce?
Kallanshi Mama tayi ta watsar irin ba'a saka bakinka ba d'innan ta mayar da kallanta ga Ajlaal tace " ya sunanta?
A shagwab'e yace " Mama!
"Eh! Wallahi a matse nake kayi aure naga 'yan jikokina, " ki bari tukunna da d'an sauran lokaci kad'an.
"Wanne lokaci ne ya rage?
"Kaga a bari ya huce shike kawo raban wani, da zafifi kan bugi k'arfe.
"Karki damu Mama wannan bazai huce ba balle ya kawo raban wanin, ita d'in tawace ni kad'ai, an riga an rubuta ni kad'ai ne mamallakinta, wannan karon bazan tab'a bari wani ya sake shiga tsakanina da soyayya ta ba, dariya Mama tayi tare da cewa " kayi komai danka mallaketa yak'i a soyayya ai halak ne, Abbah nasan yayi magana amma wani nauyi na hanashi.
Gidan ya yini bai bar gidan ba sai dare, sun sha hira, yana fitowa daga gidan yayi dialing number ta, bugu d'aya ta d'aga wayar tare da kara wayar a kunnenta batare datace mishi komai ba, yasan fishi take yi dashi dan haka tak'i yi mishi magana, idanuwanshi ya lumshe, had'i da sauke ajiyar zuciya a hankali, cikin taushin murya yace " kiyi hak'uri, soyayyarki ce tasa ni aikata duk abinda na aikata Deeyanah.
Cikin kunnenshi ta fitar da numfashi kana tace " ya wuce, murmushi yayi kamar tana ganinshi yace " yaushe zamu had'u na sake bada hak'uri sosai?
Kafin tayi magana yace " au na manta ashe fa Boss yace shi zai rink'a kaiwa unguwa da kanshi duk inda za'a aje ko?
Murmushi tayi me sauti dan tasan akwai abinda yake nufi, " fad'i kawai ina jinka! ta fad'a tana dariya,
" tunda haka ya zab'a ya zamuyi?"Tunda shiya zab'i ya zame mana driver ai hikenan, ya fad'a yana dariya, itama dariyar tayi tace " kaga a matse nake fa kwana biyu bamu had'u ba yaushe zanzo a d'an sosa min?

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...