*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh4️⃣7️⃣
Hannuwanta ta dunk'ule waje d'aya had'i da d'aga kanta sama tana fad'in " Allah kada ka tozarta ni, Ubangiji kaji tausayi na kaji k'aina ka rufe min asiri nayau kad'ai, ta fad'a jikinta na wata irin muguwar kerrrrma, tare da wani kamilin mutum Almajirin ya fito, mutumin ya mik'awa Deen hannu suka gaisa fuskarshi d'auke da murmushi yace " bawan Allah ban gane ka ba?
Martanin murmushin shi Deen ya mayar mishi kana yace nine mijin Deeyanah, ya k'arashe maganar yana kallan Deeyanah, murmushin yak'e ta k'ak'aro ta shinfid'awa fuskarta, " ah Deeyanah ce wai, ni bamma kula dake ba ai, shine zaku tsaya anan, meyasa bazaku shiga ba?
Mamakin mutumin dabata tab'a ganinshi a duniya ba ya cika da yadda yake mata magana tamkar tsofaffin abokan da suka san juna sama da shekaru, " ina ya sanni?
"Ya akayi ya san sunana?
Kashe mata tunani yayi ta hanyar cewa " bakuyi waya da ita bane?
A dururuce cikin kame-kame duk ta gama rikicewa ta had'a uban gumi tace " wa?
Fakaitar idon Deen mutumin yayi ka kashewa Deeyanah ido d'aya, a fili ta sauke ajiyar zuciya had'i da sanya gefen mayafinta ta goge gumin dake tsatsafo mata, tasan wannan bakomai bane sai aikin Ajlaal, tana k'ok'arin saita kanta tace " anya bamuyi waya da ita ba, halan bata nan ta fita?
"Wallahi ta fita tun yamma bata dawo ba amma nasan yanzu zaku ganta, ku shiga ku jira ta, ido ta zaro had'i da cije leb'enta tana kallan mutumin ido ya lumshe mata tare da nuna mata hannu alamar bakomai ta kwantar da hankalinta, duk wata dak'ik'a ta duniya tare take bugawa da zuciyarta ta kafe Deen da ido tana jiran taji amsar da zai bayar yadda kasan k'irjinta zai fad'o k'asa haka take ji, " a'a bakomai ba sai mun jira ta ba, ma dawo wata rana, nannauyan numfashi ta fitar a fili gami da lumshe idanuwanta, Deen ya yiwa mutumin sallama ya shige mota dan gudun kar Deen ya zargi wani abu yasa tayi saurin bin bayanshi.
Tuk'in kawai yake yi amma hankalinshi baya jikinshi, motar tayi tsit sai sautin kukan Deeyanah dake tashi tana shashsheka, while tana d'an satar kallanshi, sai da sukayi d'an nisa kana ta d'ago ta kalleshi sosai tace " abun har ya kai haka Yaya?
"Har ya kai daka fara zargina kana kokwanto akan gaskiya da amanata?
"Ina dukkan yardar da kayi min?
"Ina tarin alk'awarirrikan da mukayiwa junan.....
Kallan daya jefa mata ne yasata had'iye sauran maganar, harya bud'e baki zayyi magana sai ya fasa, kuka ta fashe dashi wiwi kamar k'aramar yarinya, bayyi mata magana ba ya gangara gefen titi yayi parking, idanuwanshi ya runtse da k'arfi yana jin yadda kanshi ke barazanar tarwatsewa, a hankali ya bud'e idonshi da suka gama rinewa ya sauke su akanta, wani irin haushin ta yaji yana fisgarshi kamar ya rufe ta da duka, kwantar da kujerar motar yayi ya kwanta batare daya furta koda kalma d'aya ba.
Cike da mamaki ta kalleshi ta tuna a baya idan tanayi mishi kukan wasa danta tsokane shi kusan haukace mata yake yi, yayi ta rarrashinta yana lallab'a ta kamar kwai, amma yau itace take kuka a gabanshi ko kallo bata ishe shi ba, bak'in ciki yasata watsa mishi harara tare da goge hawayenta tace " ka kaini gida, ba musu ya d'ago had'i da yiwa motar key ya fad'a saman titi, har suka isa gida babu wanda ya sake yiwa wani magana a tsakaninsu, yana yin parking motar ya bud'e ya fice ya barta cikin motar tana bin bayanshi da kallo, cikin sanyin jiki da wani irin mugun tsoronshi ta mik'a hannu ta d'auki wayarta daya bar mata anan ta bud'e motar ta fita, koda ta shiga falon babu ko alamunshi cikin falon, kamar wacce kwai ya fashewa a ciki taja k'afa ta shige bedroom d'inta.

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...