14

375 19 0
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh

1️⃣4️⃣

Shigowar Azan yasa Ammu mayar da kallanta gare shi had'i da cewa " meya faru a waje?

Labarin duk abinda ya faru ya bata, tayi murmushi had'i da cewa " Deen sarkin kishi, kusa da Ammu Azan ya zauna suka cigaba da hira.

Jin an kira sallah yasashi sauke ajiyar zuciya a zahiri tare da sakinta ya mik'e ya shiga bathroom, alwala ya d'aura ya fito, ganin inda yabar ta wayam bata nan sai warin takalminta yasa shi sakin murmushi a bayyane had'i da girgiza kanshi ya fice yana gyara hannun rigarshi, koda ta fita tayi sa'a falon ba kowa dan haka ta shige bedroom d'inta da gudu, bata san dalilin dayasa take mugun jin tsoronshi yanzu ba.

K'arfe goma sha d'aya na safe ta fito jikinta sanye da riga da siket na atamfa tayi parking gashin kanta da rebon kalar atamfar tayi d'aurin d'an kwallin ture kaga tsiya, tayi kyau sosai, " ina kwana Ammu!?

Ta fad'a tana niyar zama kan d'aya daga cikin kujerun falon, "Lafiya lau, kije ki gyarawa Deen d'akinshi, fasa zama tayi ta mik'e tsaye tana bin Azrah dake zaune kusa da Ammu da kallon tuhuma tasan wannan duk shirinta ne, Azrah dake kanne dariya tace " kin yiwa mutane tsaye aka, idan kin gama gyarawa ki kunna humidifier ki saka turaren wuta.

Baki ta turo had'i da cewa " wai ni ya ake min haka a gidan nan ne?

"Duk abin an janja min, fisabilillahi duk ma'aikatan gidan nan a rasa wanda za'a sa gyaran d'akin Yaya sai ni?

"Da can wake gyara mishi?

"Dawa kike?

Ammu ta fad'a tana tsuke fuska, " nidai gaskiya ba'a kyauta min, ta fad'a tana barin wajen, babu abinda ya samu d'akin a gyare yake tsaf, amma gudun b'acin ran Ammu yasata yaye bedsheet d'in gadon ta canja wani, ta goge ko'ina ta share, d'akin sai kyalli yake, tun kafin ta saka turaren wutar d'akin ya soma k'amshi, bathroom ta shiga nan ma ta gyara ko'ina, fita tayi ta shiga bedroom d'inta ta d'auko bunar turaren wuta, ta d'ebo turaren ta fito.

"Ayi maza a samu ladan aure 'yar albarka.

Azrah ta fad'a tana dariya bata kulata ba ta wuce abinta ta shege bedroom, Deen dake tsaye yayi murmushi yana bin bayanta da kallo tayi kicin-kicin da fuska, " kin fa dame ku.

Deen ya fad'awa Azrah yana zama kan sofa.

"Na dame ku ko kuma ina yi maka aiki.

"Aikin me?

"Aikin daka kasa yi mana, cikin rashin fahimta ya kalli Ammu kafin ya mayar da kallanshi kanta.

"Aikin samun kusanci da ita, koba haka bane Ammu?

"Ni! ba ruwana wannan maganar ku ce, mik'ewa yayi cike da kunya yabar falon, ganin yayi hanyar bedroom d'inshi yasa Azrah cewa " lah! Yabi matarshi!

Dariya yayi had'i da juyowa ya nufi k'ofar fita daga falon, " zo wuce rabu da ita kaji! Ammi ta fad'a tana dariya.

Bayan ta gama gyaran ta fito inda ta barsu nan ta same su zaune, ta zaune gefen Ammu ta had'e rai dan kar Azrah ta sake yi mata magana dan taji duk yadda sukayi da Deen.

"Deeyanah daga yau kullum ki rink'a shiga kina gyara mishi bedroom d'inshi.

"Ammu!.

Ta fad'a tana turo baki, "dan ubanki ba mijinki bane?

"Idan bakiyi mishi ba wazayyi mishi?

"Masu aiki!

Ta kuma fad'a tana sake cono baki, "sakarai wacce bata san kanta ba, ke baki kishin mijinki ne?

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now