*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh2️⃣5️⃣
Cikin bacci sama-sama taji kamar ana shafa mata fuska, a hankali ta bud'e idanuwanta da dama ba wani baccin kirkine a cikinsu ba karaf idanuwanta suka sark'e cikin na Ajlaal saurin mayar da idanuwanta tayi da runtse da k'arfi tana fad'in " A'uzubillahi minashshaid'anir rajim! Allahumma ajirni fi musibati!
Dan a tunanin ta mafarki ne ko kuma tayi mummunan gamo!
Dariya yayi sosai had'i da shan yaji shhhh kafin yace " nine shaid'anin da kike neman tsari da ni?
Saurin bud'e idanuwanta tayi dan jin muryarshi ta daki dodon kunnenta idanuwanshi ya lumshe had'i da turo bakinshi ya jefa mata kiss, saurin kallan gefen da Deen ke kwance tayi taga wayam baya nan.
" Wa kike nema 'yan matana!?
So take tayi magana amma bakinta yayi nauyi sai leb'enta dake motsi kamar an d'ora musu garwashin wuta.
Fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi yace " fad'i!
Shiru d'akin yayi, babu abinda jikinta keyi sai rawa gami da kerrrrma " fad'i abinda kike san fad'a mana!
Yayi maganar idonshi kan wuyanta, still kasa magama Deeyanah tayi ya matso gaf da ita tare da cusa kanshi wuyanshi yana shinshinar k'amshin jikinta, sai a lokacin taji wani irin k'arfi yazo mata, tasa hannayenta duka biyun ta hankad'a shi baya, yayi dariya tare da mik'ewa tsaye, itama tayi saurin dirowa daga kan gadon ta mik'e cikin dakewa ta nunashi da yatsa ta bud'e baki zatayi magana ya rik'e yatsan data nunashi dashi ya jefashi cikin bakinshi ya soma tsotsa yana lasa kamar ya samu alawa.
Tayi saurin fisge hannunta tana jefa mishi wani irin kallo ya fisgota ya mannata da bango kafin ya matseta jikin bangon ya lumshe ido yana shinshinar gashin kanta yace " karki tambayeni abinda ya kawo ni ko ta ina na shigo ko ya akayi na shigo dan ina da hanyoyin shigowa da yawa ke ko kark'ashin k'asa kika shiga saina nemoki duk inda zaki shiga a duniya saina bincikoki Deeyanah, abinda kuma ya kawo ni shine na fad'a miki ki karb'i wayar da kwartanki ya kawo miki dan mu rink'a magana Inba haka ba wallahi kullum saina zo gidan nan, ido ta zaro cike da mamakin yadda akayi yasan Deen ya bata waya tak'i karb'a.
Dariya yayi yace " kina mamakin yadda akayi na sani?
"Nasan kinki karb'ar wayar ne saboda ni, dan zaton k'aramar kwakwalwarki idan baki da waya bani da wata hanya da zan same ki ko?
Cikin tsoro ta kalleshi dan kuwa haka ta aiyana cikin ranta to ya akayi Ajlaal yasan abinda ta yanke cikin ranta.
Yayi murmushi yace " ai nayi zaton daya tambayeki abinda yake damunki zaki sanar dashi gaskiya, ita kam yanzu abun nashi ya soma bata tsoro anya Ajlaal ba Aljani bane?
Kallan d'akin ta soma cike da tsoro da matsananciyar fargaba, bakinta ya tsotsa sosai kafin yace " ki karb'a, idan baki karb'a ba hakan yana nufin kina san kullum na dinga zuwa, yana kaiwa nan ya juya ya fice batare data iya furta koda kalma d'aya ba.
Tana jikin bangon Deen ya shigo, ta kalli agogon bangon dake dak'in taga k'arfe 3:40am na dare ajiyar zuciya ta sauke a hankali tasan sallahr dare yayi, ya kalle ta kamar zayyi magana sai kuma ya fasa.
"Ina wayar nan?
Da mamaki k'arara a fuskarshi ya kalleta magana yayi niyyar yi sai kuma ya fasa ya fita ya d'auko mata ya dawo ya mik'a mata ya koma ya kwanta saman gadon, tana tsaye ta bud'e wayar IPhone 14pro ta junata a caji tana saka ta a caji ta kunna kanta, second 10 da kunna wayar sak'on Ajlaal ya shigo.

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...