18

411 14 4
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*


NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

1️⃣8️⃣

Tausayin shi ne ya kamata taji sam bazata iya fita ta barshi ba, kallanshi ta sakeyi taga sai rawar sanyi yake duk da ya kashe AC da fanka, d'akin ya d'auki wani mugun zafi, tuno yadda ya kula da ita tayi sanda bata da lafiya, ya bata kulawa sosai dai-dai da abinci a baki ya rink'a bata har wanka wasu lokutan yi mata yake yi, ya zata yi ita ta tafi ta barshi cikin wannan mawuyacin halin jikinta a sanyaye ta koma bakin gadon tace " Yaya baka buk'atar komai?

Wannan karon ko kan kasa girgiza mata yayi, d'akin tabi da kallo, bathroom ta shiga ta wanke shi tas ta goge ko'ina fes fes yadda kasan sabo wanda ba'a tab'a shiga ba, ruwan wanka me zafi ta had'a mishi cikin kwamin wanka, ta zuba mishi turaren wanka ta fito, saman gadon tahau ta yaye mishi blanket, ta d'ago shi dakyar dan yafi k'arfinta, da taimakonshi ta cire mishi riga kwantaccen gashin jikinshi tabi da kallo, yadda gashin yayi luf yana bala'in burgeta sosai.

Tana rik'e dashi ta raka shi har cikin bathroom kana ta fito a gaggauce kafin ya fito ta gyara d'akin komai ya zama need ta saka turaren wuta ta kunna humidifier k'amshin roses me sanyin dad'i ya soma tashi.

D'aure da towel a k'ugunshi ya fito ido ta zuba mishi tana kallan yadda gashin k'irjinshi ya sake kwanciya saboda danshin ruwa, ga gashin kanshi na d'igar da ruwa d'is-d'is, fuskarshi tayi yau ta rame, karo na farko da zuciyarta ta fara bugawa dominshi, karo na farko data ji wani abu me nauyi game dashi, a nutse ta kawar da kanta daga kanshi, wata irin rawa jikinshi ya d'auka, kallo d'aya yayi mata ya fahimci kamar da wani abu a tattare da ita, bayyi magana ba, yayi rolling sure ya feshe jikinshi da body spray kala-kala, kamar wacce kwai ya fashewa a ciki take tafiya zuwa wardrobe ta ciro mishi gajeran wondo da marron jallabiya ta mik'a mishi tana jin yadda bugun k'irjinta ya k'aru data kusance shi.

Muryarshi can k'asa yace " ban gajeren wandon kawai, bata bari sun had'a ido ba tace " Sallah fa?

Murmushi yayi yana komawa bathroom dan ya manta da batun sallah shiyasa bayyi alwala ba, sallaya ta shinfid'a mishi kana ta taimaka mishi ya zura jallabiyar sai da ya tada sallar kana ta fita, shayi ta had'a mishi me kauri daya sha madarar peak ta ruwa da 3 in 1 hot chocolate ta d'ora kan tray ta had'a mishi da biscuit full cream, tana gaf da shiga bedroom d'inshi Ammu da Babah na sakkowa daga sama, Ammu tace " Deen d'in ya dawo?

A sanyaye tace " yana d'akinshi ba inda yaje bashi da lafiya sosai Ammu!

"Subhanallahi meke damunshi?

Babah ya buk'ata, " zazzab'i, gaba Ammu tayi tana fad'in " muje naga jikin nashi, Babah yayi saurin cewa " zo ki fara bani abinci, " Alhaji Deen fa bashi da lafiya wanne abinci kuma?

Ido ya k'ifta mata yana fad'in " jeki kin ji Deeyanah.

Deeyanah ta wuce jikinta yana rawa, Babah ya kamo hannun Ammu yana fad'in " d'anki bashi da lafiya kin rud'e kin san a yanayin dayake zaki wuce matarshi ki shiga d'akin kai tsaye, murmushi tayi tana kallanshi tace " baka da dama Alhaji mutumin da bashi da lafiya ina shi ina fitina?

"Ke kika san wannan yaron yanzu ba ruwansu da wannan, kika ma sani ko rashin lafiya ta wannan fannin ce.

Yana kan sallaya har ta dawo, ta aje tray kan bedside ta taimaka mishi ya cire jallabiyar, ta zaunar dashi gefen gado ta d'auko tea da biscuit, kofin tea ya k'arba yana fad'in " tea ya isa! batayi magana ba ta mayar da biscuit ta aje, yanayin kurb'ar farko ya yamutsa fuska dan jinshi yayi kamar mad'aci saboda d'aci, dan dole yake shan tea, ko rabi bai sha ba amai ya taso mishi, kafin ya yunk'ura aman ya kwance mishi ya wanke mata fuska da jikinta gaba d'aya da aman har cikin rigarta.

Ido ya zuba mata yana kallanta had'i da karantar yanayinta, ya sani babu abinda ta tsana sama da amai muddin akayi amai a gabanta itama sai tayi take samun nutsuwa, muryarshi na sark'ewa yace " kiyi hak'uri!.

Babu alamun damuwa ko kyankyami a tattare da ita, ta kalle shi fuskarta d'auke da sassanyan murmushi tace " sannu Yaya.

Bathroom ta shiga tayi tsaye bata da kaya a bedroom d'inshi, ga bazata iya fita da kayan jikinta ba, a haka ma daurewa take yi tuk'uk'in aman sai taso mata yake tana mayar dashi dan kar yaji ta tana kakarin amai yayi mata wani zaton, dole tasata cire kayan jikinta ta zuba cikin kwandon kayan wanki, shower ta saki ruwan na zuba har kanta, dama kanta ba kitso ta zame reborn, da shower gel d'inshi tayi wanka, dakyar ta iya fitowa d'aure da towel, tana kame -kemen towel ta k'arasa gabanshi tace " Yaya kayi wanka ko?

" No! Bazan iyaba. Ya fad'a a wahalce.

"To muje ka wanke bakinka, ta tallafe shi takaishi bathroom, da sauri ta dawo ta yaye bedsheet ta canja wani ta jera pillows ta d'auko hypo ta goge inda yayi aman tas ta kunna humidifier flavors biyar ta zuba cikin humidifier sannan ta jona bona a soket ta zuba Arabian Oud amma still hancinta bai daina jiyo mata k'arnin aman ba, bathroom ta koma ta kamo shi, daga shi sai towel, ya cire gajeran wondon jikinshi, wani ta d'auko ta saka mishi ta kwantar dashi taja mishi bargo iyakacin k'ugunshi, tana satar kallanshi taga ko yana kallanta, taga shi bama ta ita yake ba, ta bala'in ciwon daya dame shi yake yi, hasken d'akin ta rage ta bar mishi bed lamp d'akin yayi so dump.

Yana kwanciya zazzab'in ya dawo jikinshi ya d'auki tsuma da kerrrrma, k'ofa ta nufa da nufin fita ta kasa fita tayi tsaye dan tana jiyo muryar su Ammu da Azrah a falo, tasan halin sharrin Azrah, ga jikinta babu kaya gashi ta jik'a gashin kanta sai d'igar da ruwa yake, idan ta fita ana iya cewa wankan tsarki tayi, kai bama zata iya fita haka ba, kayanta kam ko kashe ta za'ayi bazata iya mayar dasu jikinta ba, rasa abinda zatayi yasata runtse idonta, muryarshi ta jiyo tana sark'ewa " karki tafi ki barni please.

Maganar tayi mata wani irin nauyi a k'irjinta, bata tab'a jin muryarshi da irin wannan yanayin ba, take wani yanayi ya lullub'e ta zuciyarta ta shiga bugawa da k'arfi, k'ofar aka turo aka shigo Ammi na gaba sai Ammu da Babah, Abbi ne a k'arshe suna falo suka jiyo kakarin aman shi, gaba d'ayansu turus suka yi suna binsu da kallo, shi kwance ba kaya jikinshi sai bargon daya rufe k'asanshi dashi, yayinda ita kuma ke tsaye daga ita sai towel da alama daga wanka ta fito while gashin kanta na d'igar da ruwa, Ammu dake gaba ta basar ta juya ta fice, Abbi da Babah suka bi bayansu.

Ammi dake tsaye cike da mamaki tace " akace wai baka da lafiya?

Ido Deeyanah ta runtse tana maimaita tambayar Ammin " akace wai, wato bama ta yarda bashi da lafiya ba, " Allah ya kyauta tace tana ficewa daga d'akin, wani irin haushin Deen taji da bayyi magana ba, yafa gane kallon da ake yi musu, abin duniya ya taru yayi mata yawa ga kunya da takaici, ga bak'in ciki kamar ta mutu, ta d'ora hannu aka, ji take kamar ta kurma ihuu, jiyo maganarsu data daina yi ne ya tabbatar mata da sun bar falon, wato sun bar mata falon, yawu ta had'iye me zafi takai kallanta ga jallabiyar shi dake yashe k'asa da gajeren wondonshi data manta bata d'auke ba, sake runtse idanuwanta tayi da k'arfi.

Idon ta bud'e da tunanin ta saka jallabiyar shi, kanta ta girgiza tana fad'in " Kai! Ina.

Sadak'arwa tayi had'i da d'ora hannunta saman handle k'ofar, " dan Allah karki tafi.

Ta sake jin ya fad'a cike da bayyanan nan rauni, idanuwanta ta lumshe tare dayin hamdala cikin ranta dama neman hanyar zama take, dawowa tayi ta durk'usa ta d'auke gajeren wondo da jallabiya takaisu bathroom cikin kwandon kayan wanki.

Gefen bed ta d'osana ta zauna, bata dad'e da zama ba bacci ya d'auke ta, ta zube saman gadon, yayi guntun murmushi had'i da cewa " rigimammiya! Cikin ranshi.

Dama sanyi yake ji sosai har cikin kasusuwanshi ya mik'a hannu ya jawo ta ya rungume tsam da k'arfi sosai a jikinshi har saida tayi 'yar siririyar k'ara, duk da ya rufa da bargo ya kashe AC da fanka d'akin yayi zafi dan har gumi take yi amma shi saboda zafin zazzab'i wani d'umin yake nema, sosai ya shigar da ita jikinshi kamar zai mayar da ita cikinshi, yanayin rungumar da yayi mata yasa towel d'in jikinta kama gabanshi ko pant babu a jikinta, naked skin d'insu ta had'u amma shi duk ba ta wani abu yake yi ba, so yake ya samu sassauci.

Cikin ikon Allah ya d'anji relief zafin zazzab'in ya d'an ragu, nannauyan bacci me nauyi yayi gaba dashi, while ta saki jikinta ta sake shigewa cikin jikinshi......

JIDDARH...

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now