57

320 21 3
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

5️⃣7⃣

A wayewar kwana na hud'u anayin sallar isha tazo ta dasa kuka da magiya a k'ofar d'akin amma shiru, babu yadda ba'ayi da ita ta tashi ba amma ta kafe, dole tasa aka kyale ta a wajen, a k'ofar d'akin ta kwana har garin Allah ya waye tana nan zaune ko k'ifta idanuwanta batayi ba balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare, a bathroom d'in falo tayi alwala ta fito ta dawo k'ofar d'akinshi tayi sallah, haka da azahar tayi, duk abinda tayi idon kowa na kanta, tausayinsu ya kama kowa amma banda Babah dan ya tabbatar akwai wani gagarumin al amari a binne, sallah kad'ai ke tada Deeyanah daga k'ofar d'akinshi.

K'arfe uku na dare ruwan shan shi ya k'are ga matsananciyar k'ishir ruwa data adda be shi, cikin mutuwar jiki ya mik'e ya bud'e d'akin, yana fitowa yayi tuntub'e da ita, kallo d'aya yayi mata ya kauda kanshi babu d'igon tausayinta cikin ranshi saima zunzurutun k'iyayyarta dake ratsa shi, yi tayi kamar tana bacci, yasa k'afa ya tsallake ta, yana barin wajen tayi wuf ta mik'e ta shige bedroom d'in, store ya shiga ya d'ebo ruwa carton biyu da maltina carton biyu da carton d'in madara peak ta ruwa dan su kad'ai yake iya sha, ruwan da madara ya fara d'iba ya fito dasu, dayaga bata wajen bai d'auka ta shige bedroom d'in ba, yayi zaton gajiya tayi dan haka ta tafi, koda ya shiga d'akin ma bai ganta ba, ya ajiye ya koma ya d'auko sauran ya dawo, k'ofar ya mayar ya rufe da key hasken d'akin ya kashe ya koma saman bed ya kwanta idonshi yana kallan pop, dan rabanshi da bacci har ya manta tuni bacci ya k'auracewa idonshi.

Fitowa tayi daga inda take labe ta zare key d'in kana ta kunna hasken d'akin, d'agowa yayi cike da mamaki, yana d'ora idonshi a kanta yaji wani k'ululun bak'in ciki ya tokare mishi mak'ogwaro, d'an sauk'in daya samu kwana biyu take ya gushe, fuskar nan kamar wanda aka saukarwa da sak'on mutuwa, babu d'igon annuri, tashi yayi zaune yana tsare ta da idanuwanshi jajaye, saban tashin hankali da tsoronshi ne suka saukar mata lokaci d'aya, tsare tan da yayi da ido yasa ta dabarbarcewa, jikinta na kerrrma ta nufe shi, kallan karki soma zuwa inda nake yayi mata, amma ta cigaba da nufarshi, gabanshi ta zube had'i da d'ora hannunta saman cinyarshi tana kuka wiwi, ai ji yayi kamar ta nana mishi k'arfen daya shekara a cikin wuta, zabura yayi ya mik'e had'i dasa k'afa yayi ball da ita yana huci yace " wallahi karki soma rab'a ta, bata damu da fashewar da bakinta yayi ba, kota kan jinin dake zuba bata bi, ta mik'e tana fad'in " dan Allah, dan Allah Yaya ka saurare ni.

"Bazan saurare ki ba, bazan tab'a saurarenki ba har a tashi duniya dan baki da abinda zaki fad'a min, baki da abin cewa, hawayen bak'in cikin suka taru a idonshi, bayyi k'auron hanasu zubowa ba.

"Kin san k'arfin sha'awata, kin fi kowa sanin yadda nake san sex, amma kika hanani kanki duk da haka na jure har tsayin shekaru uku ban fad'awa kowa ba, Allah shine shaida ko hannun mace ban tab'a rik'ewa ba, na kama miki kaina na killace da yak'inin kema zaki killace min kanki, a kullum zuciyata tana k'ok'arin zarginki amma ina dannewa ina baki uzirin akwai dalilin daya saki kike yin hakan, duk daren duniya k'ofar d'akina a bud'e take har garin Allah ya waye ina sa ran wata rana zaki zo, hawayenshi ya goge had'i da had'iye abinda ya tokare mishi mak'ogwaro.

Wallahi Yaya ba asan raina abin ya faru ba, kidnapping d'ina yayi, daga nan ta bashi labarin farkon sake fad'uwarsu lokacin da zata je asibiti da lokacin daya turo mata video, "idan zaka iya tunawa a lokacin har kwanciya nayi a asibita na shiga matsananciyar damuwa.

"Babu irin tambayar da ban yi miki akan ki sanar dani damuwarki ba amma kika k'i, har rok'onki nayi.

"Tsorata ni ya rink'a da video da kuma zai kashe kowa nawa yayi, ta fad'a cikin matsanancin kuka.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now