7

419 25 0
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh

7️⃣

A zabure Abba yace "Kar dai kace min Nakowa?

"Shi Abba cewar Ajlaal , "to ikon Allah wannan ba sai anyi wani bincike ko b'ata lokaci ba, zan nemi mutane sai muje, murmushi Ajlaal yayi yana shafa kanshi yace " nagode sosai amma dan Allah aje da wuri,
" zamuje da wuri amma sai kayi min alk'awarin zaka koma kamar da zaka koma Ajlaal Basaan d'in dana sani zaka koma level 4 d'inka,
" in sha Allah Abba, har Ajlaal yakai bakin k'ofa Alhaji Basaan ya kira sunanshi cikin taushin murya "Ajlaal..!,
jin yadda ya kira sunanshi yasashi juyawa cikin nutsuwa, " Lokaci da rayuwa suna da matuk'ar mahimmanci dan idan daya daga cikinsu ya kufce maka bazai taba  dawo maka ba, kayi kokari ka amfanesu, ba shekara ba, ba wata ba, ba sati ba, ba kwana ko yini ba, ba awa ko minti ba dai-dai da dakika daya idan ta wuce daga rayuwarka bazata kara  dawowa ba harka koma ga Allah, dan haka kasan me kayi a kowacce rana ta rayuwarka da zai amfane ka Duniya da Lahira,
fata, buri da mafarki duk abu d'aya ne, kuma kowa yana da nasa, yawan burikanka yawan jajircewarka,  karka bari shirme da shiririta su cinye kaso mafi yawa a rayuwarka,
ya kamata kayi abinda zaka amfana kuma al'umma zasu amfaneshi, wanda zaka ci moyarshi duniya da lahira,
murmushi Ajlaal yayi tare da jinjina kanshi yace " nagode sosai Abba in sha Allah zanyi amfani da abinda ka fad'a min.

Daya shigo makaranta farkon abinda yake fara yi shine nemanta, in banda ma tayi mishi gargad'i da fad'in " karka soma gangancin zuwa gidan mu duk ranar daka sake kaje gidanmu nasan daga ranar bazaka sake ganina a rayuwarka ba dan cire ni za'ayi daga makaranta ayi min aure.

Murmushi yayi yace mata " dako saina addabi ahalinki da mijin daya aureki, da kice mace ta farko a duniyar musulunci da zata fara kasancewa matar maza biyu dan kuwa ko kinyi aure ke tawa ce ni kad'ai Deeyanah, tana d'aukar kalamanshi da wasa dan haka bata tab'a basu mahimmanci ba.

Yauma yana shigowa department d'insu ya wuce tana zaune cikin aji ana yi musu lecture's yayi sa'a tana dai-dai window dan haka yaje jikin windon ya tsaya yana kallanta, cikin sa'a ta d'ago ta kalli windon suka had'a ido, tayi mishi murmushi shima ya mayar mata da martanin murmushi, a hankali cikin rad'a-rad'a yace " yaushe zaku fito?

Itama cikin rad'a-rad'ar ta bashi amsa da " nan da minti 30, dayake dama ya saba idan zata kwana tana lectures sayya jirata duk dad'ewar da zatayi baya damuwa, ya koma gefe ya zauna yana jiranta.

"Deeyanah me nace?

Malaminsu ya tambaye ta saboda ya lura da abinda take yi, " na'am Malam! Ni?

"Eh! Ke me nake cewa yanzu?

Kame-kame ta soma yi, "fito nan, Malamin ya fad'a yana kafe ta da ido, cikin sanyin jiki ta fito gaban allo, alli ya mik'a mata yace " ungo maza k'arasa mana bayanin tunda naga kamar kin riga kin sani, bata karb'i allin dayake mik'o bata ba tace " kayi hak'uri dan Allah Malam.

"Dama soyayya da kula-kulan maza iyayanki suka turo ki yi makaranta?

"Arahar taki har takai haka?

"Gaskiya banyi zaton kina da sauk'in samu haka ba wall......

Tasssss! Tassssss! Ajlaal ya d'auke shi da gigitattun marika masu k'arfi, ya shak'i wuyanshi yana huci ya d'aga shi sama " idan mahaifiyarka ko matarka da 'yarka ta cikinka da k'anwarka aka fad'awa ya zaka ji?

" Suma fa 'ya'yan wasu ne, k'annan wasu sannan wata rana zasu zama matan wasu har su kai ga zama iyayen wasu, ya buga shi da k'asa zai rufe shi da duka Deeyanah tayi saurin shiga tsakiya tana zubar da hawaye tace " ka kyale shi dan Allah.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now