49

233 18 5
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

4️⃣9️⃣

Hankalinta kwance take tuk'in tana bin wak'ar Ranar Aure na ta mawak'i Umar me Sanyi da gidan radio suka saka, takai hannu ta k'ara volume, tana rausaya kanta alamar tana bala'in jin dad'in wak'ar, ana gama wak'ar gidan Radio suka sak'o wa'azin Malam Ibrahim Daurawa me taken ILLAR ZINA, wata irin muguwar fad'uwa gabanta yayi, Malamin yayi gyaran murya yayi sallama kana ya fara magana " in Allah ya yarda yau zamuyi magana akan illolin zina, zamu tab'o har b'angaren matan auren dake ZINA DA AURENSU, dammmm! dammmm! dammmm! gabanta ya shiga dokawa da tsananin k'arfi.

" Tsira da amincin ALLAH sutabbata ga ANNABIN dababu wani bayanshi

Salati da tsira da amincin Allah su tabbata bisa Jagoran Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu (ﷺ)tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Maɗukaka.

ILoLin zina da kuma Hukuncinta

Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi
(ﷺ) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai
Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Shirka da Allah,
Alhali shine ya halicce ka, " Sai aka ce sai wanne? Sai ya ce "Sannan kashe ɗanka don
kada ya ci tare da kai." Sai aka ce "sannan sai  wanne ? " Sai ya ce "Ka yi zina da matar
makwabcinka,  (Bukhari) yadda ruwaito.

Allah Maɗaukakin sarki ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya taɓa aure ko yana da aure a jefe shi, namiji ko mace, idan kuwa bai taɓa aure ba, sai a yi masa bulala ɗari, sannan a
baquntar da shi a wani gari daban tsawon shekara guda.

Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga Allah Ya keɓance shi da wasu abubuwa masu yawa, saboda munin zina, ga kad'an daga cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa.

1. Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta hanyar jefewa, ko kuma bulala da bakuntarwa shekara guda.

2. Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu ukuba Allah yace :-

ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِى فَٱجْلِدُوا۟ كُلَّ وَٰحِدٍ مِّنْهُمَا مِا۟ئَةَ جَلْدَةٍ ۖ وَلَا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِى دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْءَاخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٌ مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِين

"Mazinaciya da mazinaci to ku yi bulala d'ari ga kowanne ɗaya daga gare su, kuma kada tausayi ya kama ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kuna yin imani da Allah da ranar lahira, sannan wani yankin jama'a daga muminai su halarci azabarsu.  (Annur : 2). .

Ayi musu ukuba a gaban mutane ba'a yarda a yi musu a boye ba.

Imamul Bukhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga Maimun Al-audiy ya ce,

"A lokacin jahiliyya na taɓa ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka taru suka jefe su.

Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar makwabcinsa, Allah ya kare mu.

ILLoLin Zina: Babu shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, waɗanda suke shafar mazinacin ko mazinaciya, ko su shafi al'umma gaba daya.

1. Zubar da mutunci da jawo wa kai k'ask'anci, Duk matar da ta yi zina to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta ƙasƙanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya, Idan har ta sami ciki ta haihu, sannan ta kashe ɗan, to ta haɗa laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai, In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu, Idan kuwa mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da taɓewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba daya.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now