*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh2️⃣3️⃣
Wata irin mahaukaciyar fad'uwa gabanta yayi, cikin kid'ima da tashin hankali taja baya tana fad'in " Aj....lal, kyakkyawan murmushinshi ya sakar mata yana fad'in " ashe zaki gane ni?
Cikin murmushin yak'e muryarta na rawa tace " so..sai ma, kawar da idonshi yayi daga kanta, dan jin wani irin mugun sonta da sha'awarta na taso mishi,
take yaji tamkar bai tab'a santa a duniya ba sai a wannan lokacin, wutar santa data lafa mishi ta taso mishi,
saboda ita yak'i aure, dan kullum gani yake zata dawo gare shi, ko sau d'aya bai tab'a cire rai da samunta ba, akanta yake kallan matan duniya tamkar maza ba mata ba,
motarta ya kalla yana fad'in " lafiya meya samu motar?Yak'e ta kuma yi tace " tsayawa tayi, hannu ya mik'a mata yana fad'in " bani key d'in, ba musu ta bashi, dan kallo d'aya zakayi mata kasan a tsorace take,
yayi yin duniya motar tak'i tashi, ya fito yace " tak'i tashi ina zaki?"Asibiti...
Sai a lokacin ya kula da cikin jikinta, wani abu yaji ya tokare mishi mak'oshi saboda bak'in ciki, murmushin dole ya k'ak'aro yace " muje na aje ki,
" a'a ka barshi zanyiwa k'aunata waya yazo yakaini,
ido ya runtse da k'arfi kana ya bud'e yana fad'in " ki tambaye shi idan ya yarda saina kaiki, tab! tashin hankali wanda ba'a saka maka rana,
Deen zatayiwa maganar Ajlaal, bayan tasan yafi san mutuwarshi akan Ajlaal,
"A'a zan hau napep kawai, yin duniya tahau ya kaita tak'i hawa, tsakiyar titi ya koma yayi zaman cin abinci ya tankwashe k'afafuwanshi,
cikin mamaki ta kalleshi kana ta mayar da kallanta kan uban go slow d'in daya had'a, mutane sai zagi suke yi, " ka tashi please, maimakon ya tashi sai yayi kneel down a gabanta,
yana fad'in " dan Allah ki hau na kaiki, yayi maganar hannunshi had'e alamar rok'o, batare daya damu da yadda mutane ke kallanshi ba, tasan halinshi da mugun taurin kan tsiya,
idan ya kafe akan abu ko za'a mutu bazai yanje ba, ganin mutane sun fara cire waya zasuyi musu video yasata cewa " tashi muje, da sauri ya mik'e duk ilahirin jikinshi na tsuma,
ya bud'e mata gaban mota, tak'i hawa ta bud'e baya ta shiga, mudubi ya saita yana kallanta, yana fad'in " shekaru biyar, watanni 60, sati 260, kwanaki 1800, awanni 43,200 ban ganki ba Deeyanah,
cikin matsanancin mamaki ta d'ago kanta dake duk'e ta kalleshi, "kina mamaki ko?Guntun murmushi yayi yace " yau da gobe taba canja komai Deeyanah sai dai tana nuna mata hak'ik'anin mutane, shekaru, watanni, satittika basa iya canja hak'ik'anin abinda ke cikin zuciyar masoyi na gaskiya,
" niko kaga na dad'e da mantawa da rufe babinka a rayuwata, dan baka zame min dole saina rayu dakai a tunani ba, kamar yadda ban zame maka dole saika rayu dani a rayuwarka da zuciyarka ba,
ko dani ko bani, ko da kai ko ba kai kowa zai iya gudanar da rayuwarshi, danya kawar da maganar yace " yaranki nawa?Banza tayi kamar bazatayi magana ba kafin tace " 1 DeeDee,
" DeeDee! Ya maimaita sunan kafin yace " Dee yana nufin Deeyanah ko?Sosai yake bata mamaki amma data tuna yadda yake da kwakwalwa saita daina, murmushi tayi tace "eh! while d'aya Dee d'in kuma na nufin Deen, kai fa kana da aure?
"Hmmmmm ina ni ina aure bayan kina raye kina taka doran k'asa, koda bakya raye bazan tab'a yin aure ba, muddin bake ce matar ba,
yayi maganar cikin ranshi, a zahiri kuma yace " eh nayi aure harda yara biyu, Deeyanah da Ajlaal , sunan yarana, dayake 'yan biyu shine na saka musu sunan mu, idan tace bataji tausayin shi ba k'arya take take yi, "wannan wacce irin soyayya ce?Ta fad'a cikin ranta, cikin sanyi tace " Allah ya raya su, ya amsa da " Amin ya Allah, kanta ta mayar kan wayarta ta cigaba da abinda take yi bata k'ara yi mishi magana ba.
*************************************
Farkawa tayi ta ganta a gidanta mijinta Deen zaune kusa da ita yana yi mata sannu, sosai kanta ya kulle bazata iya tuna komai ba, daga lokacin da take zaune a motar Ajlaal yana fad'a mata sunan yaranshi, kanta ta dafe tana san tuna wani abu amma ta kasa tuna komai,
jikinta tabi da kallo taga babu abinda ya canja, ta kalli Deen tace " Dee! ya akayi nazo nan?"Waya akayi min, aka sanar dani nazo na d'aukeki an tsince ki cikin motarki a sume, ajiyar zuciya ta sauke still tana san tuna wani abu ta kasa, kanta take tambaya da " meya faru dani?
"Ya akayi haka ta faru?
"Ina Ajlaal?
"Meke faruwa ne?
Ta jerawa kanta da kanta tambayoyin, tayi nisa cikin duniyar tunani ya katse mata tunani da fad'in " dama saida nace miki ki bari na kaiki kikace a'a, cikin mutuwar jiki ta kwantar da kanta saman k'irjinshi tana fad'in kayi hak'uri, ya shafa kanta yana murmushi, shiya taimaka mata tayi wanka ya shirya ta, hannunta cikin nashi suka fito falo ya zaunar da ita tare da bata abinci a baki, sukuku take Allah kad'ai yasan meke faruwa cikin ranta, haka nan hankalinta yak'i kwanciya, wani irin mugun tsoro da fargaba suka shige ta, in banda fad'uwa babu abinda gabanta keyi, tana san ta fad'awa Deen gaskiyar abinda ya faru tana jin tsoro.
Bayan kwana biyu Deeyanah zaune a falo tana kallon SunnaTv, ta shagala sosai da kallan saboda tarihin Sayyadina Umar ake yi, film d'in ya tafi da ita, shigowar sak'o cikin wayarta yasata d'auke idonta daga kan TV ta mayar kan wayarta,
sharewa tayi ta cigaba da kallanta, jim kad'an wayarta ta soma rori, saida taja tsoki saboda an katse mata kallanta kana tayi picking wayar batare data duba number ba,
" Assalamu Alaikum, Amin wa'alaikissalam, jin muryar Ajlaal yasata zaro ido sosai a tsorace, " lafiya?"Ina ka samu number ta?
Cikin isa da tak'ama yace " zan turo miki address d'in gida na kizo yanzu ina san ganinki, wayar ta cire daga kunnenta ta duba a karo na biyu, kana ta mayar da wayar kunnenta tana fad'in " ka san wacce ka kira kuwa?
" Inaga baka san da wacce kake magana ba, dariya ya sanya sosai yana fad'in " da Mrs Deeyanah Deen nake magana na sani,
tsaki taja had'i da cewa " inaga dai ka samu tab'in hankali Ajlaal, tana k'ok'arin kashe wayar yayi saurin cewa " a'a kul karki soma kashe min waya, ga sak'o nan na turo miki ta WhatsApp ki duba saiki yanke hukuncin zaki zo ko a'a, yana gama magana ya kashe wayar,
jikinta na rawa ta duba WhatsApp d'in, video ta gani ya turo mata hannunta har rawa yake, tayi playing videon, itace kwance tsirara haihuwar uwarta da ubanta,
tana kwance wani namiji yazo shima jikinshi ba kaya amma ya rufe fuskarshi da mask, ita da kanta ta jawoshi jikinta ya fad'a kanta, suka shiga aiwatar da masha'a, videon ya d'auku sosai fuskarta ta fito tarrr kamar blue films....Bata san sanda ta buga wayar da bango ta tarwatse ba, kanta ya shiga juyawa ta soma ganin komai bibbiyu, k'ara tayi ta sulale k'asa a sume......
JIDDARH....
YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...