43

247 13 2
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*
   

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

4️⃣3️⃣

Tana san tayi magana amma idonshi dake kanta ya hanata bata damar yin maganar.

Cikin suyar k'irji yace " haka kika yi tayi min wan can karon har na gaji nayi zuciya na barki da abunki, yanzu ma gashi kin kuma, anya Deeyanah babu wani abu da kike b'oyewa, shekara kusan biyu fa bamuyi sex ba, and shekara d'aya da rabi bama tare baki ganni ba ban ganki ba, bakiji d'umin jikina ba ban ji d'umin jikinki ba, amma ace dana dawo ko marmarima da d'orina bakiyi?

"Dana tafi America ko sau d'aya tak baki tab'a kira na kince min sha'awa na damunki ko you're in the mood ba, baki tab'a kira na video call ba, ke bama ki bani time & attention d'inki ba, babu wata kula da kika bani har naje na dawo a matsayi na mijinki, dana dawo maimakon ma ace kece ke rushing in to sex amma kece ke denied, why Deeyanah?

"Ina sha'awarki take tafiya?

"Wake gusar miki da ita Deeyanah?

"Anya bakya neman maza da aure na akanki!?

"Wad'annan sune tambayoyin da ke san na rink'a yiwa kaina har zarginki ya shiga raina auren mu ya haramta?

"Ko ko kin d'auki aure abin wasa da sai lokacin da kike da buk'atar koma meye za'ayi?

"Bana san na zarge ki, please karki tilastawa zuciya ta zarginki dan hakan bazai tab'a haifar mana d'a me ido ba, dan Allah karki tursasa ni na shiga zarginki, daga ni har ke bazamu ji dad'in abun ba, gwara tun wuri ki nemarwa kanki mafita, imma wasu k'awayen kikayi suke neman hure miki kunne gwara ma tun wuri tun kan dare yayi miki ki canja tunani, har ya juya zai bar wajen ya juyo ya sake jefa idonshi cikin nata yana kallan kwayar idonta ya nuna mata d'an yatsa yace " duk abinda zakiyi kije kiyi ta yinshi zan iya jurewa, amma middin kika sake kika ci amanata, ya cije lips d'inshi na k'asa.

"Dan bai yiwa ni ina d'a namiji da duk kalar iskancin da zanyi dan iya yinshi ba aure ne akaina ba ko duniyar ce akaina zan iya aikata koma meye amma na kame kai na, ke da kike mace a k'ark'ashin ikona sannan ke keyin abinda kike so, wallahi Wallahi tallahi na rantse miki da girman Allah kika sake na kamaki da cin amanata saina barki har abada koda kece autar matan duniya, koda hakan yana nufin bazan k'ara aure ba har a nad'e k'asa, k'asa-k'asa yayi da muryarshi yace " wallahi koda hakan yana nufin mutuwa ta, kuma zan tsane ki tsana ta har abada, Deeyanah bazaki sake gani na ba a iya tsayin rayuwar da zamuyi a duniya, yana kaiwa nan ya juya ya barta nan tsaye.

In banda rawa babu abinda jikinta keyi, duk da sanyin ac dake d'akin bai hanata yin gumi ba, mak'ogwaronta ya bushe har wani d'aci-d'aci yake mata yayinda da zuciyarta da k'irjinta ke luguden bugu, ji take yi kamar ana d'agata sama ana bugawa da k'asa, idonta yaji yake yi mata sosai saboda tsantsar tashin hankali, jikinta a sanyaye ta zame ta zauna kan kujerar dake bayanta had'i da cusa yatsunta duka goman cikin gashin kanta, bata san sanda ta saki kuka me k'una da soya zuciya ba, kukan dake fitowa daga can  k'asan zuciyarta, ta rasa yadda zatayi, ta rasa mafita gaba d'aya kanta ya gama kullewa b'am, wannan wacce irin bak'ar rayuwa ce?

In banda na shiga uku, babu abinda take fad'a, ta durk'ushe nan wajen taita rusa kuka wiwi.

Shi kam a b'angaren shi yana shiga bedroom d'inshi ya zube saman bed rigingine idonshi kan roping, tunanin daya fara zuwa kanshi shine koyaje ya sanar da iyaynsu halin da ake ciki?

Kanshi ya girgiza had'i da furta " ni! nakai k'arar mace saboda sex Allah ya kiyaye?

Har yamma tayi yana nan kwance yama rasa tunanin da zayyi, ko sallar azahar bayyi ba, " kodai wani ta samu wanda ya fini iya sex?

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now