*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh1️⃣1️⃣
Bayan hannunta ta saka ta goge hawayenta, had'i da mik'ewa ta shige bathroom batare tace mishi komaiba.
Kofar toilet din data shige yabi da kallo, tare da sauke numfashi mai sanyi yana sake jinta cikin zuciyarshi saboda komai nata yana tab'a shi dalilin kaunarta datayi nauyi cikin zuciyarshi.
Mik'ewa yayi ya fice daga d'akin cikin ranshi yana godewa Allah, kuma koma dai yayane hankalinshi ya kwanta tunda ta riga ta zama mallakinshi.
Deeyanah kuwa a cikin toilet d'in tsayawa tayi gaban madubin toilet din tana kallon fuskarta idanuwanta na sake cika da hawayen data rasa dalilin zubarsu, gabaki d'aya ta rasa menene makomar farin cikinta da kwanciyar hankalinta da wannan rayuwar auren data tsinci kanta ciki rana tsaka.
Ta d'an dad'e a ciki kafin ta wanko fuskarta ta fito ta nufi wayarta dake gefen gadonta ta d'auka tana son yin waya amma kuma bata cikin dad'in zuciyar yin wayar dan haka tayi wurgi da wayar gefen pillow tana zamewa ta kwanta jiki a mace.
Wuni tayi a d'aki i cikin damuwa da sanyin jiki batare da ta fito ko abinci ta nema ba Ammu ma bata damu da takura lalle sai ta fito ba, dan bazata iya b'atawa kanta lokaci kan abinda tasan bazai tab'a canjuwa ba.
Sai dare bayan dawowar Babah har yaci abinci baiga ko inuwar Deeyanah ba ya tambayi Ammu.
" Tana d'aki ta rufe kanta ciki ko abinci bata fito taci ba.
Shiru yayi yana sake nazarin yanda lamarin yazo a gaggawa wanda kusan dole ce tasa akai hakan amma koma menene koma yaya lamarin yazo Alhamdulillah tunda dai tazama ikon 'dan uwanta da suke da tabbacin bazata tab'a kuka ko shiga k'unci a hannunshi ba, ya san Idan tagama damuwa kwana biyu zata karbi komai da hannu biyu insha Allah.
Kwance take sanye da doguwar riga brown ta bacci mai dan nauyi yanayinta yasa taji kaman sanyin zazzabi takeji shiyasa ta saka rigar bacci mai taushi da dan nauyi.
Idanuwanta a rufe suke amma ba baccin takeyiba taji shigowar Ammu amma takasa bude idanuwanta sbd jikinta da babu qwari.Kallonta Ammu tayi tana dan zama bakin gadonta kai tsaye tace,
"Deeyanah ki tashi ga tea a dining na aje miki kisha, hana kanki cin abinci ko walwalwa ba shine zai baki ko sauya miki komaiba,
Deen dai ba wani bako bane da zakice baki saniba an daura miki aure dashi hankalinki ya tashi,
Dan uwanki ne kuma jininki ne
A yanda muke miki fata da addua shine zai zama gatanki kuma farin cikinki insha Allah ko bama raye.A hankali ta bude idanuwanta dasukai laushi ta kalli Ammu, ita kanta ta rasa meyasa duk jikinta ya mutu yayi sanyi haka,
Tasani dai bata bakin ciki da auren kaman yanda bata farin ciki dashi sai dai kuma damuwa dole ce a gunta ace rana tsaka an daura aurenta da wanda bata taba zata ba kuma daga sama batare da an baka lokaci na komai ba,
Tayaya ma yanzu zata fara yiwa Deen kallon miji??Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tare da tashi zaune, k'afafuwanta ta ziro kasa batare da tace komai ba, tana san cin wani abu a cikinta itama.
Bathroom ta shiga ta wanke fuskarta da bakinta ta fito ta zira flat slippers dinta masu kyau sbd bata yawo ko acikin gida batare da takarmi a kafafuwanta ba ak'idarta ce wannan.
Qaramar hulace kawai a kanta suka fito daga dakin nata zuwa palo Ammu na sake kokarin jan hankalinta da yaba halayen Deen wanda take jinsa tamkar itace ta haifesa sbd kaunar datake mishi, dama ta dad'e tana san auren Deen da Deeyanah, tana san yaron tasan ko bayan ransu ita da Babah zai kula da Deeyanah, koda aka d'aura auren hamdala taitayi cikin ranta dan ba k'aramin dad'i taji ba.

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...