24

349 15 2
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*


             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

2️⃣4️⃣

Bata farka ba sai cikin dare, bakinta d'auke da salati ta dafe kanta tare da yamutsa fuskarta, a hankali ta bud'e idanuwanta da sukayi mata nauyi ta fara ganin komai dishi-dishi kafin a hankali idanta ya washe tarr,
k'ok'arin mik'ewa zaune ta soma hannunta dafe da kanta, " yi a hankali, taji an furta daga gefenta, idonta ta sake warewa sosai tana bin inda take da kallo, sai a lokacin ta kula da a asibiti take, hannunta jone da cannula ana k'ara mata ruwa.

"Sannu..! Deen! yace yana tallafe ta, juyawa tayi ta kalleshi, tana d'ora idonta akanshi komai ya shiga dawowa mata, tunaninta ya dawo, wata irin mahaukaciyar k'ara tayi tare da tushe kunnuwanta da hannayenta ta saki rikitaccen kuka tana fad'in.

"Na shiga uku!... na shiga uku na lalace.

"Subhanallah me yayi zafi haka Deeyanah?

Deen ya fad'a yana rik'e ta.
Ammi tace " kul karna sake jin kince kin shiga uku kinji ko?

A haukace kamar zararriya ta kalli Ammin tana girgiza kanta while tana kukan tace " idan da abinda yafi shiga uku ma na shiga, na shiga dubu ma ba uku ba, ina cikin bala'i da musiba Ammi,
wannan wacce irin bak'ar k'addara ce Allah ya d'ora min?

"Me yasa saini?

Rik'e mata hannu Ammi tayi tana fad'in " kowacce dak'ik'a data harba a agogo tana harbawa ne da rubutun wata k'addara a rayuwarmu,
K'addarar da ka iya zama shafi cikin littafin rayuwarmu, fatanmu Allah ya gina mana katangar karfe da mummunar k'addara.

Cikin kuka Deeyanah tace " amma meyasa saini?

"Meyasa akaina kawai zata fad'a?

Idon Deen kanta yace " Deeyanah ki manta da abinda ya cutar dake amma karki sake ki manta da darasin daya koyar dake,
zatayi magana Deen yace " wai mema ya firgitaki haka?

D'an jimm tayi tana tunanin ta fad'a musu ko karta fad'a musu, "kiyi addu'a koma meye yazo miki da sauki saboda taka tsantsan baya hana afkuwar masifa, amma addu'a tana tasiri akan masifar data sauka dama wacce bata sauka ba, Masifa takan sakko sai addu'a ta tareta, suyita fafatawa har ranar tashin alkiyama, kinga masifar bazata cimma ma'abocin addu'a ba,
cikin mutuwar jiki tasa hannu ta goge hawayen dake ta faman zubowa saman fuskarta, " Ammi ki tayani addu'a mummunar k'addara ta afkawa min.

Kallon juna Ammi da Deen sukayi kafin suka mayar da kallonsu ga Deeyanah cikin rashin fahimta Ammi tace " kamar ya ban gane inda maganarki ta dosa ba!?

"Bazaki gane ba Ammi.

"Duk irin bayanin da zanyi miki bazaki fahimci komai cikin zance na ba, ni kaina na kasa fahimtar komai, ko kalma d'aya na kasa fahimta Ammi.

"Ki nutsu kiyi ki kwantar da hankalinki, kyayi mana bayani daga baya, Deen ya fad'a yana k'ok'arin had'a Ido da ita tak'i bashi dama, wani iri take ji cikin jikinta wai itace tayi video tsiraici na batsa?

Itace irin wannan bak'ar k'addarar ta fad'awa, komawa tayi ta kwanta had'i da lumshe idanuwanta hawaye na gangarowa ta gefen idanuwanta.

Ba bacci takeyi ba, tana jin hirar da Ammi da Deen keyi amma bata fahimci ko kalma d'aya cikin maganganun da sukeyi ba, hankalinta baya jikinta, k'ofar d'akin aka bud'e DeeDee ya shigo da gudu yana fad'in Momy, wani abu babba taji ya tokare mata mak'ogwaro ya soki Zuciyarta.

"Momy! Deedee ya fad'a yana fad'awa jikinta.

A fili ta sauke nannauyan ajiyar zuciya kafin ta d'agoshi tana k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta lullub'awa fuskarta.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now