35

350 24 5
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*
   

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

3️⃣5️⃣

cikin ranta ta soma maimaita " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un badai tafiya zayyi ya barni ni kad'ai cikin wannan babban bala'in ba?

"Bazan iya ba, bazan iya d'auka ni kad'ai ba, ganinka kawai da nake yi a kusa dani yana sakamun nutsuwa da kwanciyar hankalin cewa koba komai ina da mai tayani yak'ar Ajlaal wata rana, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga uku ina zan kai wannan mummunar k'addarar?

Ta fad'a cikin ranta, kamar bazayyi mata magana ba sai kuma ya dawo ya kalli idonta dake cike tab da ruwan hawaye yace " zan tafi, na aje miki kud'i, idan sun k'are ko kina buk'atar wani abu muyi magana.

Wani irin kuka ne mai nauyi da k'unci ya kwace mata, bata san sanda ta fad'a jikinshi tana fad'in " karka tafi ka barni ni kad'ai ba, bazan iya jurewa k'addarori biyu a lokaci d'aya ba, na gwammaci mutuwa ta sau dubu yaya da irin rayuwar da nake yi, sai da yayi da gaske ya iya mayar da abinda ke taso mishi, a hankali ya rabata da jikinshi dan baiga dalilin yin kukanta yanzu ba,
duk wata dama ya bata, ya tambayeta idan tana cikin matsala ta fad'a mishi su raba matsalar tare, amma tak'i bashi damar data cancance shi, ta hanashi hakk'inshi dake kanta wanda Allah ya halarta mishi.

Hannunshi ta rik'e gam cikin nata hawaye nabin fuskarta tace " da nace ina sanka a karon farko nasan ka jini, na fad'a na sake maimaitawa badan ina da shakku kan yardarka ba, sai dan ranakun da kalamai zasuyi min k'aranci, dan ranakun da yanayin k'addara zasu iya yi min katanga da fad'ar, dan ranakun da bani da tambacin samun damar fad'ar, na so ka jiya, ina sanka yau, babu kuma abinda zai canja gobe, Deen zuciyata taka ce kai kad'ai, koda k'addara ta gifta a tsakaninmu ka sani nayi abinda nayi ne danku.

Juyowa yayi ya kalli cikin kwayar idonta yace " ina sanki jiya ina sanki yau, cin amana ne kad'ai zai canja gobe, Deeyanah ina sanki da komai nawa, numfashi na bai tab'a fita batare dana tunaki ba, amma ki sani muddin cin amana ya shigo tsakaninmu nayi miki alk'awarin zan tsane ki fiye da komai har izuwa k'arshen rayuwata, kuma wallahi har ki mutu bazaki sake gani na a duniyarki ba, murmushin yak'e tayi tana shafa fuskarshi amma deep down yadda kasan ana tsikarawa zuciyarta alluran da suka shekara a wuta haka take ji, tana kallanshi har ya fice ta kasa cewa komai balle ta bishi, abinda take ji yau ya girmi bak'in ciki, kalamanshi sun saukar mata tsoro da fargaba.

"Karki bishi Deeyanah, karki sake kiyi gigi da gangancin binshi, dan binshi tamkar kin sallama kowa cikin ahalinki ne ciki kuwa har da tilon d'anki, sannan shima saina sashi ya tsaneki fiye da mutuwarshi dan saina saki videon nan, kuma bazaki tab'a b'ace min a duniya ba, duk inda kika shiga saina nemomi a duniya.

Kalaman Ajlaal daya fad'a mata bayan sun dawo daga wajensu Abbi da Babah suka dawo mata, tana nan tsaye inda ya barta kamar wacce aka dasa hawaye nabin fuskarta, taji an hura mata iska a fuska, ajiyar ta sauke a fili ta kalleshi batare datace komai ba.

Allah ya taimaka su Abbi basa gida lokacin da Deen zai tafiya danshi a zatonshi da Deeyanah zai tafiya, jiya da daddare daje yi musu sallah nasihar dayayi mishi ta shafi ta zamansu acan, sama-sama ya biya yayiwa su Ammu sallama ya wuce yana juya kalamanta cikin kanshi.

Light kiss yayi mata a gefen fuskarta yana fad'in " kin samu freedom ko?

"Hararshi tayi tana d'oye damuwarta tace " ka dai samu freedom, tuntsurewa yayi da dariya sosai yana cewa " tab! sannunki, ai ni dama can a freedom d'ina nake kece dai a kulle kamar dabba, bataji dad'in maganarshi ba, amma ta basar, "zamuje can ne ko anan zamu soye, yayi maganar had'i da kashe mata ido d'aya ya cije leb'enshi na k'asa, ai yadda yayi mata take taji wani yarrrr a jikinta wutar ta ta kawo bata san, sanda ta had'e bakinsu tana k'ok'arin nemarwa kanta sauk'i da sassauci kan halin da take ciki ba.

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now