3

591 29 3
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

             NA

*HAUWA A USMAN*
       ~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaAUsmanjiddarh

3️⃣

Ido ya fara wulk'itawa yana neman ta inda zai hango ta, amma ko alamarta babu,
ta bayanshi yaji ance " Deeyanah! kake nema ne?

" Tana ciki ta kulle kanta a d'aki tak'i fitowa ko abinci bata fito ta ci ba, da alama fa yadda ka kamu itama ta kamu, saurin juyawa yayi, Babah ne, kanshi ya shafa yana kallan Baban,
kai Babah ya jinjina mishi danya gane kallan da Deen keyi mishi, ya d'ora da cewa " duk da baku furta ba, amma ina da tabbaci akan hakan, dan tun jiya data dawo makaranta ta shiga d'aki bata fito ba har yanzu,
an buga mata k'ofa tak'i bud'ewa, zayyi magana Babah ya tareshi da cewa " ni dai ina baka shawara akan kayi mata magana kar lokaci ya k'ure maka,
da kayi magana da yanzu da matarka zaka tafi, ina jiye maka abinda zaije ya dawo, ina jiya maka yanayin juyawar k'addarar dake raba masoya ta k'ulla sabuwar soyayya,
cike da yak'ini Deen yace " hakan bata tab'a yiyuwa ba, Allah kad'ai zai rabani da Deeyanah, amma babu mahaluki abin halitta da ya isa ya shiga tsakanina da ita,
k'uruciya, Babah yace cikin ranshi, a fili kuma yace " wannan duk yarda da kai ne?

"A'a Babah ba yarda da kai bane, yak'ini da zuciya ne, murmushi Babah yayi ya rik'e hannun Deen yana fad'in " muje karka makara,
bazai iya yiwa Babah musu ba amma yaso yaje k'ofar d'akinta ya jiyo koda fitar numfashinta ne,
dole yabi bayan Babah idonshi kan k'ofar dakinta, basu wani jima a Airport ba jirginsu ya d'aga zuwa America,
bata fito daga d'aki ba sai da akayi kiran sallar la'asar, kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin damuwa, Ammah na zaune saman sofa tabi bayanta da kallo batare datace komai ba,
zatayi karya idan tace bataji babu dadi ba, bayan tafiyar Deen, sosai tayi kewarshi, sai da Raleeya ta sata gaba da tsokana tana cewa " da an san ana so aka tsaya jan aji, dole ta watsar ta shiga sabgar gabanta ta mayar da hankalinta gaba d'aya kan karatunta.

*MAFARIN BAK'AR K'ADDARA...!!!*

Da wuri ta shiga makarantar direct class ta nufa har tana tuntube kasancewar wayar da Raleeya tayi mata ta sanar da ita, yau me English ke had'a Assignment dinshi,
tun farkon Semester Malamin ya bada Assignment din, ta rasa wanda zayyi mata, har caffe taje amma a banza,
ga Malamin yayi gargadin kar mutum biyu suyi iri daya, muddin yaga iri d'aya zayyi musu cancel gaba daya,
" kin san Allah haukana nayi mishi, tunda shi yace bai san copy copy ni na tab'a jin irin wannan kakalen,
Cewar Raleeya tana bata fuska, rolling ido Deeyanah tayi tana fad'in " ni haukan ma na kasa yi wallahi, na rasa ta in da zan fara abin duniya duk ya isheni,
shiru Raleeya tayi na d'an lokacin kafin ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in " akwai mafita, cikin zakuwa Deeyanah tace " dan Allah?

" Eh, naji yawancin 'yan ajinmu na cewa wani d'an level 400 ne yayi musu, an ce duk makarantar nan ba mai k'ok'arin shi, wai sau kusan biyar yana samun scholarship yana k'in tafiya,
" me yasa?

Deeyanah tayi maganar cike da mamaki, " eh to wai shine bai sha'awar fita waje yayi karatu, inda yana da ra'ayi daya fita dan babanshi me mugun kudi ne,
naji ance shine sakataren governor fa, kuma shi kad'ai ya haifa, kuma mahaifinshi na mugun sonshi, kinga ra'ayin fita waje ne bayyi ba,
kamar dai ke da baki da ra'ayin fita waje karatu, Raleeya ta fad'a tana kai mata dukan wasa, baki ta tab'e tana fad'in " wallahi nima dai banga amfanin karatu waje ba,
sai b'ata tarbiyya da lalata d'abia a cirewa 'ya'ya mata kunya, su koma kamar tumakai, dariya Raleeya tayi tana fad'in " kedai kika sani, mudai samu ne da bamuyi ba, idan muka samu zamu,
" ke dai ban san surutun banza rakani wajen... wama yake...., " AJLAAL , sunanshi Ajlal.

"
Ajlal...! ta maimaita sunan saman lips d'inta, jin yadda ta Deeyanah ta maimaita sunan so calm yasa Raleeya kallanta tana murmushi tace " yayi masifar had'uwa,
ga kyau ga kudi, ga gayu da tsafta, ga Ilimi both boko da arabi ga kwakwalwa, gashi da aji wallahi,
cike da k'osawa Deeyanah ta juya idonta tana fad'in " kai nidai naga ta kaina, kodai kodai... ta k'arasa maganar tana d'age mata gira d'aya,
" wace ni kawata, wannan ai yafi k'arfin ajina,
" tab wallahi ki daina fadar haka kika san me Allah zayyi, " hmmm banda dai anan, dan bakin wuta ba wajen wasan makaho bane, guntun murmushi Deeyanah tayi hadi da gyara tsaiwarta tace " Raleeya Rayuwa kamar kwai take bata da gaba ko baya balle wani yasan alkiblarta, ba kuma asan fuskarta ko keyarta ba, ba wanda yake da tabbacin dan tsako zai zama ko ko wainar kwai zai zama, duniya kamar mace mai ciki ce babu wanda yasan abinda zata haifa,
Raleeya zata kuma magana Deeyanah tayi saurin cewa " dan Allah muje.

*AJLAL....!*

D'a d'aya tilo ga Alhaji Basaan da Hajiya Halimatu, Alhaji Basaan mutumin kirki ne ba laifi yana kwatantawa dai-dai gwargwado,
yayinda Haliya Halimatu ta kasance bak'ar muguwa kuma azzalumar mace marar imani, shi kanshi Alhaji Basaan d'in ba dad'inta yake ji ba dan tafi k'arfinshi sai abinda tace kuma take so shi yake yi, tana iya kunyata shi gaban kowa, idan tana yi mishi fad'a da tsawa saika rantse d'anta ne, daga shi har ma'aikatan gidan mugun tsoranta suke ji, ta zama mijin ya zama matar, ko kallanshi tayi yasan abinda take nufi, a b'angaren jama'a kuwa mutuniyar kirki ce ga faram-faram da mutane, sai d'an abinda ba'a rasa ba, tana zaune da kowa lafiya amma a gida yadda kasan boss haka take, taita muzurai ita kad'ai, yayinda Ajlaal ya kasancewa mutum mai saurin fushi da bakar zuciya,
idan ka b'ata mishi rai zayyi maka abinda shi da kanshi zai dawo yana nadama,
babbar matsalarshi saurin hannu yanzu zai kai duka, kodan ya taso a sangarce a kuma shagwabe ne oho, tunda Ajlaal yake bai tab'a wayar gari ya nemi wani abu ya rasa a rayuwarshi ba,
bayan wannan bashi da wani mugun hali, baya shaye-shaye, baya neman mata dan da d'an iska ne shi da an shiga uku yadda mata keyi mishi tururuwar kawo mishi tallar kansu,
amma ko kallo basu isheshi ba yanzu zai dizgaki a gaban kowa, ya sha wulakanta mata wasu ma harda mari.

Yauma kamar kullum tunda ya shigo makarantar mata ke kai mishi kokon bararsu akan soyayya, kusan mata uku ne suka tare shi suka sanar mishi suna sanshi,
babu wacce ya amsawa a cikinsu sai dai ya wuce su yayi kamar bai ji su ba, amma deep down ya kawo iya wuya, ji yake kamar zayyi bindiga saboda takaici da bakin ciki,
kwata-kwata baya san irin abun baya so, abun baya burgeshi, gani yake kamar rashin aji ne, rashin sanin darajar kai da karancin tarbiyya kesa mata su kawowa namiji tallar kansu.

Yana tafe yana mita a zuciyarshi ya gama k'uluwa sosai, ya k'uduri niyyar duk yarinyar data sake k'ok'arin tsayar dashi ko tayi mishi magana,
sayya kafa tarihi akanta wanda zai zamarwa wasu izzina, daga b'angare daya kaddara ta bud'e saban shafi a rayuwarsu ba tare da sun sani ba,
" minti d'aya please Ajlaal zamuyi magana dakai, Raleeya ta fad'i suna k'arasawa inda yake, tsayawa yayi cak tare da runtse idonshi yana jin yadda tuk'ukin bakin ciki ke tasowa tun daga kasan zuciyarshi,
"taimako nake nema daga gareka please ka taimaka man, Deeyanah ta fad'i cike da karaya,
bayyi magana ba bare ya juyo, bata damu da yadda yayi musu ba, tunda ta samu labarin yana da girman kai, da yanga, abun bai wani dame ta ba,
tunda ba alak'a take san k'ullawa dashi ba, assignment dinta kawai take san yayi mata, daga haka shikenan, k'ok'arin controlling kanshi yake san yi amma ya kasa, a tak'aice yace " a'a please, " dan Allah ka taimaka ka saurare ni,
ba wani abu bane INA SAN KA KO.....!,
loosing control yayi jin ta furta kalmar INA SANKA..., bai bari ta k'arasa fadar abinda take san fad'a ba ya d'auketa da marin daya sata kifawa,
a fusace ya juyo tare da d'aga murya yace " enough ya isa please! Am tired from all your drama, stop it please, yadda yayi maganar cikin hargowa ya jawo hankalin dalibai.......

JIDDARH

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now