*BAK'AR SHUKA...!*
NA
*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:HauwaausmanjiddarhBazan rink'a yin posting Asabar da Lahadi ba, posting dina zai kama daga ranar Monday zuwa Friday.
8️⃣
"Nifa bana jinka, in zakayi magana kayi da sigar rok'o ba kana magana kamar kana bani umarni ba, kayi magiya Malam, ka rok'e ni, idonshi ya sake runtsewa da tsananin k'arfi kana ya d'an d'aga murya yace " kayi hak'uri dan Allah, sai a lokacin Malamin ya sauke ajiyar zuciya kana ya d'ora da " bakomai dama ni ban k'ulla ce ka ba, HOD yayi musu 'yar nasiha akan rayuwa, tayi mishi godiya dan shi ko kalma d'aya bai tsinta ba cikin nasihar saboda tsabar zafin zuciya.
Suna fitowa su HOD suka rufarwa wannan Malamin da fad'a dan bayyi dai-dai ba.
Har bakin get ya kaita ta shige gida, shi kuma ya wuce bai nemeta sai dare ya kira wayarta tana zaune kan sallaya wayarta ta soma ringing bata amsa kiran ba sai ta shafa addu'ar, "an huce kenan?
"Au da fushi nayi?
"Sosai ma kuwa, wai dama haka kake da bak'ar zuciya?
"Anya zakayi saurin yafiya kuwa!?
Kwashewa yayi da dariya sosai yace " me kike nufi?
"Ai gani nayi cikin d'an lokaci ka canja har kalar idonka ma saida ta canja kala anya da a zamanin su fir'auna da Abu Jahil kazo zaka karb'i musulunci kuwa?
Dariya ya kuma yi sosai har da buga k'afa had'i da cewa " ai zuciyar bata kai nan ba, waya sukayi sosai kana sukayi sallama.
*America....*
Kwance yake saman kujera idanuwanshi lumshe dukda kasancewar ba bacci yake ba, abin duniya ya isheshi, tunda ya taho ko a waya baiji Deeyanah ko sau d'aya ba,
baiji halin da take ciki ba, muskutawa yayi ya gyara kwanciyarshi yana fad'in " gaskiya nayi k'ok'ari wata shida kenan fa ban ganta ba banji daga gareta ba,
k'arar shigowar sak'o dayaji a wayarshi yasashi jan d'an guntun tsaki yana d'aukar wayar, a Arewa Youth's Achievers group yaga alamar an turo sak'on,
group d'in daya had'a manyan matasan Arewa da suka zama wani abu a rayuwarsu, Ajlaal ne kad'ai wanda baya aiki, kuma d'alibi a group d'in,
shima dan ana saka ran gobenshi mai kyau ce, shiyasa aka saka shi, gashi da kwakwalwa da hazak'a gami da nacin karatu,
kuma yana bada gudunmawa sosai a group d'in dan sau da dama za'a bawa masu yin master Assignment su kasa sai Ajlaal ne zai koya musu,
sak'on da aka turo Deen ya karanta _" d'aya daga cikin Member d'inmu na wannan group Ajlaal Basaan wanda ba b'oyayye bane anan, kowa ya sanshi,_
_ya fad'a soyayya da wata yarinya, a makarantarsu bayan ya ci mutuncinta ya ci zarafinta ya muzantata ya tozartata ya wulakantata,_
_daga k'arshe Allah ya jarrabeshi da matsananciyar soyayyarta,_
kamar ya share sai kuma yayi playing videon da aka turo, baki ya tab'e had'i da cewa " sharmeee zambur ya mik'e tsaye kamar an tsikare shi, bakinshi bud'e cike da mamaki gami da tsoro ganin Deeyanah ce,
take jikinshi ya d'auki rawa da kerrrma yana tsuma, komawa yayi ya sake duba rubutun da akayi a k'asan videon, "meke faruwa ne?"Meya had'a Ajlaal da Deeyanah?
"Me tayi mishi daya wulakantata yaci zarafinta?
"Ya akayi ni duk ban San wannan na faruwa ba?
"Ina nan ina zaton bani da matsala da ita, ina tunanin ina da yak'ini akanta, yayi maganar yana dafe da kanshi, kanshi ya d'aga alamar tunani ya dad'e a haka kafin ya sauke ajiyar zuciya a karo na ba adadi,
mik'ewa yayi ya shiga bedroom d'inshi da sauri, kayanshi ya shiga had'awa cikin gaggawa a trolley, ko wanka bayyi ba ya saka kayanshi ya jawo trolley,
ma'aikatan gidan yabarwa sallahun zaije ganin gida bazai dad'e ba zai dawo, su kula da gidan,
direct airport ya nufa, yasha wuya sosai kafin su bashi ticket, sai da yayi musu k'aryar mutuwa akayi mishi,
k'arfe 12:30 na dare ya sauka a Nigeria,
jirgin sama ya hau daga Abuja zuwa Kano, bai shiga gida ba sai 5:00 na safe, babu wanda ya gayawa yana tafe dan haka babu wanda yasan da zuwanshi,
d'akinshi ya wuce saboda damuwar dayake ciki bai ko cire kayan jikinshi ba ya kwanta, Allah Allah yake gari ya k'arasa wayewa.

YOU ARE READING
BAK'AR SHUKA...!
SpiritualGurbatacciyar zuciya me cike da zallar soyayya, soyayyar da bata da alkiba, bata da gaba balle baya, soyayyar da tunda aka fara ta babu farin ciki da jin dad'i har izuwa k'arshenta, duk da sun kasance ma'aurata amma rayuwa suke gudanarwa a juye ta b...