5

488 23 1
                                    

*BAK'AR SHUKA...!*

NA

*HAUWA A USMAN*
~ JIDDARH~

Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh
ArewaBooks:Hauwaausmanjiddarh

5️⃣

*Cigaban Labari....*

Bata damu da yadda hawaye ya jik'a mata fuska ba, ta mik'e dakyar tana d'ingishi tabar cikin bolar, hanjin cikinta ya fara juyawa alamar yunwa take ji,
yadda kasan mahaukaciya haka Deeyanah ke tafiya ba takalmi, kafarta duk faso ta tsatstsage jini na bin k'afar, kayan jikinta sunyi fata-fata sun yage,
da bak'ar leda tayi dan kwali ta rufe gashin kanta, koda wasa batayi gangancin bi ta inda gawar mutanen daya kashe suke ba,
danta tabbatar zuwa yanzu mutane sun cika wajen, ta baya ta zagaye tayi ta tafiya ga yunwa da k'ishirwa na azalzalarta,
tayi tafiya takai ta awa biyu kafin takai bakin titi, jikinta na b'ari ta galabaita sosai harta manta da wacece ita, ta isa gaban wani shago muryarta sark'ewa tace " ru....ruwa
Bakinshi a sake yake binta da kallo tun daga sama har k'asa, tunanin daya fara zuwa ranshi ko mahaukaciya ce, bayyi magana ba ya mika mata pure water, jikinta na rawa ta wafta a hannunshi cikin abinda bai wuce dakika biyu zuwa uku ba ta zuke ruwan tas ta yadda ledar,
ta kara zuba mishi ido a karo na biyu, " baki k'oshi ba?

Da sauri ta daga mishi kanta alamar eh, bayyi magana ba ya mika mata wani ruwan, ta amsa ta shanye duka, cike da tausayawa yace " kin koshi?

"Kai ta daga mishi tana fad'in " Alhamdulillah, da sauri ya juyo ya kalleta yana mamaki dan har lokacin yayi tsammanin bata da hankali, " nagode tace tana barin wajen, yabi bayanta da kallo cikin ranshi yana mamaki mace har mace amma ta zata kamar tababbiya saboda yanayin rayuwa,
tsaye tayi gaban mai saida doya da kwai, ta k'urawa doyar ido bata ko kiftawa, jikinta har rawa yake saboda matsananciyar yunwar dake azalzalarta,
kallanta mai doyar yayi cike da k'ama yace " bar wajen nan, da ido kawai Deeyanah ta bishi batare dayi abinda yace ba, a tsawace yace " nace ki bar nan ko?

Deeyanah bata motsa ba ta cigaba da kallan doyar, zayyi magana wani dake zaune yana cin soyayyar doya da kwai yace bata ta biyu,
jin ace a bata yasata ta kalli Wanda yace abatan hawaye na gangaro mata tace " nagode sosai Bawan Allah, Ubangiji ya biyaka, ya amsa da Amin, me doyar ya d'ago kanshi ya kalleta yana fad'in " dama ba mahaukaciya bace ke?

Cikin sanyinta ta d'aga mishi kanta, faranti ya cika da doyar ya hada mata da soyayyar kwai da k'undu ya mik'a mata,
jikinta na rawa ta fisga ya kalleta cike da tausayawa, yadda take ci hannu baka hannu kwarya duk ilahirin jikinta na tsuma ya kara karya mishi zuciya,
tas ta cinye ta mik'e mishi faranti bakinta cike da doyar tace " nagode, ya amshi faranti tare da mika mata ruwa, ta amsa ta tabi, titi tabi taita tafiya saida ta fita daga cikin mutane sosai sannan ta samu gindin bishiya ta zauna,
ta sani duk rintsin da zata shiga bazata tab'a rasa mataimaka ba, saboda addu'ar da  mahaifiyata tasha yi mata,
ta fashe da kuka data tuna yadda rayuwarta take a  baya, yadda ta taso cikin babban dangi da suke santa, ta taso cikin gata da kulawar 'yan uwanta, balle uwa uba  MIJINTA mai santa saboda Allah, wanda baya san ganin bacin ranta kona dakika daya, amma taci amanarshi tayi mishi butulci, duniyar tunani ta tsunduma tana tuno rayuwarta ta baya mai kunshi da haske da farin ciki.

*WAIWAYE.....*

Cikowar mutane Raleeya ta gani makil a harabar makarantar wanda yawancinsu d'alibai ne, kallo d'aya zakayiwa dayawa daga cikinsu ka fahimci suna cike da tsantsar mamaki,
kutsawa ta farayi cikin mutanen dan ganewa idonta abinda ke faruwa wanda ya tara d'alibai har da Malamai haka, idonta ta zaro cike da mamaki gami da zallar tashin hankali, ganin AJLAAL BASAAN durk'ushe gaban DEEYANAH bisa gwiwowinshi,
idanuwanshi cike da hawaye yana fad'in " KECE RAYUWATA DEEYANAH, KE KAD'AI NAKE SO, KI YARDA DANI, zan baki kulawar da wata mace bata tab'a samu daga wajen d'a namiji ba,
zan soki sanda ba'a tab'a yiwa wata d'iya mace ba, zan tarayrayeki zan baki kulawa nayi miki alk'awarin bazan tab'a barinki cikin k'unci ba balle harta kai ga d'igon hawayenki ya zuba,
wallahi tallahi billahil azim da Allah yayi umarni wani yayiwa wani SUJJADA dake zan fara yiwa SUJJADA, da ace bautawa wanin Allah ba laifi bane dake zan mayar abin bautata,
saboda tsantsar soyayyar danake miki, da kisan kai ba babban laifin bane dana tsaga k'irjina na ciro miki zuciyata na d'ora ta a tafin k'afarki kin taka,
naji labaran soyayya da dama, wad'anda suka faru a jinsi daban-daban a jin Larabawa akwai Lailah Majnun, a turawa akwai Romeo & Juliet, a indiya akwai Ram da Sita,
amma duk cikinsu bana jin akwai wanda yakaini san abar sona, inaga mune zamu kafa namu tarihin a namu jinsin Deeyanah
dan Allah ki taimakeni ki amshi k'ok'on barana karkice a'a, idan kika k'i karb'ata a matsayin masoyinki ina mai tabbatar miki anan take zan mutu,
ya k'arashe maganar hawaye na zubo mishi, idonta ta juya had'i da yamutsa fuska ta nuna kanta tana fad'in " ni?

"Ni Deeyanah kake so?

"Ni Deeyanah daka gama tozartawa kaci mutuncinta ka wulak'antata a gaban mutane?

Murmushi tayi tana cije lips d'inta had'i da cewa " da alama baka san me kake yi ba, baka san me kake fad'a ba, idan ma ka sani hala ka manta da wacce kake magana,
idonta ya ciko da hawaye yana k'ok'arin zubowa juyawa tayi da nufin barin wajen, yayi saurin rik'e k'afarta gami da fashewa da kuka wiwi,
" ki taimake ni dan Allah, ki tuna Allah yana san mutane masu yafiya, na sani na b'ata miki ban kyauta ba amma zan iya hukunta kaina a bisa laifin danayi miki,
kanshi ya soma duka da duka hannayenshi da iya k'arfinshi had'i da buga kanshi a k'asa cikin k'ank'anin lokaci bakinshi da kanshi ya fashe,
jini ya b'ata mishi jiki, cak ta tsaya tare da goge hawayen idonta ta taka zuwa gabanshi, ido ta kafeshi dashi na d'an lokaci kafin tace " ko zaka mutu, ko zaka kashe kanka bazan tab'a sanka ba,
tsayawa cak yayi zuciyarshi na dokawa da tsananin k'arfin dake neman tarwatsa k'irjinshi baki ya bud'e da nufin yin magana ya kasa, harshenshi yayi nauyi, jikinshi a mace ya zube k'asa idanuwanshi suka soma rufewa da bud'ewa,
dakyar yayi k'arfin halin kiran sunanta amma bata tsaya ba, ta cigaba da tafiya tana goge hawaye, duk kiran da yake mata bata saurareshi ba.

Ido Raleeya ta murza ta bud'e ta kalli abinda ke faruwa danta tabbatarwa kanta gaskiya ne ko mafarki ne, baki bud'e mutane ke kallan abinda ke faruwa,
Raleeya na kallan Deeyanah na tafiya amma saboda tsabar mamaki ta kasa abinta.

Yau kam mamaki neman kashe kowa yake, bakin su duk ya mutu duk anyi tsit, dakyar Raleeya ta iya jan k'afarta tabar harabar makarantar, ta shiga motarta tayi gidansu Deeyanah.

A harabar gidansu Deeyanah tayi parking ta fito da sauri ta shiga main gidan, a tsaitsaye ta gaida Ammi dan Allah Allah take taji yadda akayi,
tana san ta tabbatar da abinda ta gani, Deeyanah na Sallah Raleeya ta shigo, ganin Deeyanah na sallah ya tuna mata batayi sallah ba, san jin kwakwaf ya mantar da ita,
tana jin Deeyanah tace " Assalamu Alaikum tace " kawata ya akayi haka ta faru?

Murmushi Deeyanah tayi tana cewa " Rayuwa idan babu k'alubale to babu nasara, idan kuwa akwai K'alubale to lalle akwai Nasara, a haka Allah ya tsara rayuwar,
Cikin rashin fahimta Raleeya tace " kamar yaya ban gane ba?

"Kina mamaki da ikon Allah ne?

" Ko kina tunanin tashin dare da nake ina tsayawa bisa tafukana ina kai kukana wajen Ubangijina akan ya saka man zai tafi a banza?

"Yaushe abin ya soma da har yayi nisa haka ban sani ba?

Baki Deeyanah ta tab'e tana mik'ewa tace " tun last week ya fara bibiyata sama-sama abun bayyi tsamari irin this week ba,
ajiyar zuciya Raleeya ta sauke tana rafka tagumi tace " to yanzu meye abinyi?

"Me kuwa?

Cikin zaro ido Raleeya tace " mak'iyinki ne fa?

" Dan mak'iyina ne sai akayi yaya?

"Masoyi da mak'iyi ina alfahari da kowanne daga cikinsu saboda kowanne akwai ranarsa haka yana da amfanin dazai yi min

Makiyin?

Amfani fa kika ce?

"Hmmmm, Deeyanah tace gami da sauke ajiyar zuciya kafin tace " kwarai kuwa dan zan iya cewa amfanin makiyi yafi na masoyi,
Cike da mamaki Raleeya kebin Deeyanah da kallo batare datace komai ba, " eh mana, saboda shi makiyi a koda yaushe kokarinshi yaga kuskurenka yayi ta yadawa danya aibataka a wajen mutanen da suke ganin k'imarka,
batare dayasan yana gyara maka dabi'u da kurakuren rayuwarka ba, muddin kayi kuskure kaji an fada ka kuma gane kuskure ne bazaka kara maimaitashi ba,
haka munafuki burinshi yayi abinda zai burgeka danka bashi yarda da amana, ya kara samun kusanci dakai shiyasa zayyi tayin abinda zai burgeka, babban amfaninshi zai rinka rage maka zunubi, ya kwashe daga kanka ya d'ibarwa kanshi, kinga duk mutumin da zai rage maka zunubi yayiwa kanshi kyautarshi shine masoyi,
Masoyi na gaskiya kuma har abada ana tareshi dashi ba yardarka ko bashi amanarka yake bukata danya cutar dakai ba,
haka bazai baka lu'u-lu'u, gwal, azurfa, gida ko mota da kudi ba, zuciyarshi da rayuwarshi zai baka, tashi gaskiyar da amanar, hadi da yardarshi zai baka.

Raleeya zatayi magana Deeyanah tayi saurin barin d'akin tana fad'in " ke ni yunwa nake ji, dan tasan idan bata bar d'akin ba suna iya kwana Raleeya na damunta da tambayoyi kamar 'yar jarida.

Bayan Deeyanah tabi tana fad'in dan Allah zo ki k'arasa labarta min labari kin sanni da san jin zance, suna zaune a dining suna cin abinci minti d'aya minti biyu sai Raleeya tace "unhunn namiji kenan ba kunya.

*WACECE RALEEYA?*

BAK'AR SHUKA...!Where stories live. Discover now