MASARAUTA 2

176 30 0
                                    

💙💙💙💙💙💙💙💙
      *MASARAUTA.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMA ILYAS KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA BIYU*

Chak ta ja ta tsaya ta na juyowa domin kallon shi,a lokaci ɗaya su ka haɗa ido,ɗan murmushi ta yi wanda bai kai zuciba,sai dai kuma duk da haka kyawunta ya baiyana,daƙyal ta iya buɗe baki"In sha Allah."

Ba ta kuma magana ba,Yarima ya shige ciki,da kanta ta je wajan da ake haɗa Abinci,zuwanta ya  sa ma'aikatan dagewa wajan harhaɗawa,aka biyota da shi,sai da ta tabbatar an ajiye komai kafin ta bar ɓangaren tana ɗan sauri jin an fara kiran salla.

     ****
Dadaddare suna wajan zamansu domin yin fira,duka yaran kowa yana wajan,haka su kan yi lokaci bayan lokaci Musamman yau da suke ganin suna da Zancan tattaunawa.

Bilkisu ta ɗan ja guntun tsaki,Faruk ya kalleta"Tun ɗazu sai wani shan tsamiya kike mana,kin kasa magana."

"Mi ye abin saita furta,bayan kunsan damuwarta"Cewar Yarima shureim.

Aymana ta ɗago"Idan kina da damuwa ki faɗi,nasan dai maganar bata wuce ta Yarima Amin."

"Atunanina zai so da TAKOBIN gidanmu ne,ashe ba abinda ya kawo shi ba kenan."

"Hmmm na faɗa muku,haka nan suke ganin zasu maido alaƙarmu dasu."

Faruk ya kaɗa kai"Sam ni banga wani abin alaƙa dasu ba,Amma Sarki ya dage akan hakan,Martabarmu na hannunsu,sam bamuna wani ƴenci ko martaba a wannan nahiyar kum..."

Bai idaba Aymana ta miƙe"Na barku lafiya,tuna har yau babu wata ma fita da muke da ita don kwato TAKOBI daga hannun masautar Toro."

Tana maganar tana barin wajan,wajan su Yarima ta nufa sai dai Fadawanshi sunce yana ciki ne,Hakan yasa ta juya,domin dama zuwan don tambayar ko sun buƙatar wani abu ne.

        ****

Tsaye ta ke a Falon farko na ɓangaran baƙin,ga kuyangu da kayan karin Yarima Amin,sai dai Aymana ba ta ba su Umarnin ajiyewa ba.

Yarima ya fito daga Cikin ɗakin shigarshi a yau ba kayan Sarauta bane,wani farin yadi ne da aka yiwa ɗinki na zamani ya amshi jikinshi sosai,kanshi babu Hula sai sumar kanshi data kwanta saboda gyara da yake mata.

Agogon Hannu yake ɗorawa,Ƙamshin turaren shi ne yasa Aymana ɗagowa,tana kallon shi,Farine yana da tsayi sai dai baya da kwarin jiki,yana da gyawun fuska.

Kallonsu yayi yana amsa gaisuwar su.Aymana ta yi saurin faɗin"Ga kayan kari har rana tayi kum..."

Bai bi ta kanta ba,ya kalli kuyangun tare da magana"Babu nauyi ne,ba za ku ajiye ku huta ba?"

"Ku Ajiye"cewar Aymana tana masu nuni da wani wajan cikin Abinci"A'a a ƙasa zaku ajiye"

Cikin sauri da ladabinsu suka hau jera Abincin kamar yadda Yarima yace.

Yarima ya maido hankalinshi akan Aymana"Ina kwana."

Sam ita ta manta da maganar gaisuwa sai taji babu daɗi"Fatan ka tashi lafiya"Tana maganar ta maida hankalinta kan kuyangunta.

"Tsayuwar me kuke?"

Cikin sauri su ka yi hanyar fita,sai ɗaya da ko wane lokaci tana tare da ita,hakan yasa bata tafi ba.

Yarima ya matsa yana zama kan kujerar da ke gefen shi"Za ki iya zama."

Ɗan shiru tayi tana kallon Ƙasa don batasan miye dalilin zaman ba,Yarima ya ɗauki wayar shi yayi kira,ba jimawa Fadawanshi suka shigo.

"Na fito ban ganku ba?"

"Ranka ya daɗe bamu san ka gama ba."

Yarima yayi Murmushi"Zaku iya zama ayi ƙari,ina son mu fita gaishe da Baba"

MASARAUTAWhere stories live. Discover now