MASARAUTA 41

124 14 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ARBA'IN DA ƊAYA 41*

*SIYYA COLLECTION* 07033111950

Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*

Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*

Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.

Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.

Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*

Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.

Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.

Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.

*Page 41*

Aymana ta fashe da kuka tare da ƙanƙame shi, wani irin ciwo zuciyarta take mata, tabbas ta san ko zata jure komai to banda nisantar Sultan dinta.

Hankalin Sultan kanshi ya tashi yanzu ya sakawa kan shi lallai tashin hankalin da ake zai iya taɓa lafiyar  Aymana da kuma yaron cikinta.

Ajiyar zuciya yayi "Ki tashi muje ciki, zan bawa Baba haƙura, sam Sultan ba zai taɓa rabuwa da ke ba."

Haka suka tashi Sultan babu nauyin mutanan gida haka ya wuce da Aymana a hannunshi har ɓangaren shi, yanzu ya sawa ranshi komai zai faru babu wanda zai kuma magana da Aymana don ba zai yadda wani abu ya same ta ba.

Ayda ce ta shigo falon, lokacin Aymana tana cikin ɗakin shi, yana tsaye yana kai kawo "Sultan zai buƙaci wani abu kuwa?"

Ɗagowa yayi babu wani annuri a fuskar shi, ya san ba don Allah take tambayar ba, haka kuma sam bata iya salon tambayar ba.

"Ba na buƙata."

"Me zai damu Sultan bayan Allah ya taimake ka, babu abinda ya faru, haka kuma bata fita da Mulkinka ba, tunda Ashirinta ya tonu sai..."

Tsawa ya daka mata, yana nuna mata hanyar fita, Ayda ta gyara mayafin kanta "Na san kana cikin ruɗu da ɓacin rai amm..."

Rufe idanuwanshi yayi "Na ce ki fita."

***

Gimbiya Ummi duk yadda ta so ganawa da Sultan bata samu hakan ba, hankalinta ya tashi ainun, ta yadda aka sanar da ita Aymana ta aikata laifi babba irin wannan.

Saboda Soyayyar da take mata sai ta ke ji aranta kamar ba gaske ba, ko da ta tabbatar abin ya faru hanyoyi take nema na wanke Aymana.

Ɗakin Gimbiya Maigado kuwa, farinciki fal zuciyar su, sun tabbatar koda ba a ce Sultan ya sauka mulkiba, idan aka raba auran to ya samu wani naƙasu a mulkinshi domin sun gama tabbatar da Aymana itace komai na shi.

***
Ƙarfe Hudu aka kuma wani zaman, mahukunta su ka yi jawabi sosai, wannan lokacin sun saka fahimta a cikin lamarin, kowane ɓangaren ya ƙara kare kanshi.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now