MASARAUTA 7

125 16 0
                                    

💙💙💙💙💙💙💙💙
      *MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA BAKWAI. 7*

Yarima ya kalli Bilkisu"Ta ya ya za a barta babu abinci tsawon wannan lokacin,tun jiya,haba Bilkisu?"

Cikin damuwa yake maganar ita kanta Bilkisu wani irin kallo take mashi don gane gaskiyar abin da yake faɗa"Yanzu fa ta ƙi bani lokacin magana balle na yi mata tayin abinci."

Shi kan shi yasan cewar maganar auren shi da Aymana ta zo mashi a kiɗime,amma yasan dole ne ita ma ta shiga hali,musamman yadda yasan mace tana da rauni akan maganar aure.

"Don Allah Bilkisu ki samu abinci ki kai mata"

Miƙewa tayi tana barin wajan,Yarima ya bi bayanta sai dai cikin dakewa ya isa sashen Umma.

Tana zaune saman kujera,Yarima ya durƙusa gabanta,cikin girmamawa fiye da kowane lokaci,tare da gaida ita.

Umma tana murmushi"Alhamdulillah fatan kana lafiya?"

"Lafiya ƙalau Umma."

Shiru yaɗan bi bayan gaisuwar Umma ce ta daure wajan fara mashi maganar auren"Umma nima haka na samu labarin kuma inshaallah ba zaku sameni da aikata ba dai-dai ba."

Sosai ta ji daɗi"Nasan haka Yarima Allah ya daidaita tsakaninku."

Shiru yayi yana kallon ƙasa"Ita tana can tana kukan da bazai fissheta ba."

"Yanzu na tura Bilkisu ta kai mata abinci."

Murmushi Umma tayi,zata kuma magana Hajiya tayo sallama tare da shigowa,suka ansa.

Yarima yaɗan sunkuya ya gaida ita tare da miƙewa zai basu gu.

Hajiya ta ce"A zo zauna,dama maganar taka ce ta kawo ni"

Umma ta ɗan gyara zama tana kallon fuskar Hajiya sam bataji daɗi kallon da take wa Yarima ba.

"Na je na dubo Gimbiya Aymana,tunda muke da ita a gidan nan bamu taɓa ganinta cikin ƙunci irin wannan ba..."

"Hajiya ai dama zata yi hakan amma a hankali zata koma lafiya."cewar Umma.

Hajiya ta aikawa Umma da wani wawan kallo"Sam ba zamu lamunci ganin 'yarmu cikin ƙunci ba,Aymana ta yi magana da Maimartaba ya ce bazai janye maganar shi ba."

Yarima ya ɗan ɗago yana kallon Hajiya yana son karantar ta,ci gaba tayi da magana"Daga ƙarshe ya tabbatar sai idan kaine ka ce baka amince ba."

Umma ta ce"Haba Hajiya wannan wace irin magana ce,ku fa manya ne bai kamat..."

"Idan ke ba zaki iya magana ba to mu ba zamu yi shiru ba."

Yarima ya kalli Umma"Shi kenan Umma karki damu"

"Zaka janye maganar kenan?"

Yarima ya kalli Hajiya ya gano tsantsan makirci a tare da matar murmushi yayi"Ina jin nauyin Baba ba zan iya kallon idon shi na faɗa mashi ba zan bi umarnin shi ba."

Ajiyar zuciya Umma tayi,Hajiya ta ci gaba"To so kake ayi abinda zai kawo danasani,Aymana dai bata sonka  kuma na san kaima ba sonta kake ba."

Yarima ya kalli Umma data yi tagumi,tana kallon Hajiya,Hajiya tace"To ko kana son ta ne?"

"Ba ni so kuga kamar nayi rashin kunya amma tun farkon zuwana gidan nan naji tsananin soyayyar Aymana a tare dani,kuma...."

Hajiya ta miƙe tana buga cinya"Ƙarya kake wannan makirci ne,dama ba don Allah  kazo gidannan ba kazo ne don wasu manufarku akan mu."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now