MASARAUTA 29

101 18 2
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ASHIRIN DA TARA. 29*

"Allah ya kawo mana Magajin Sultan Lafiya, ki sanar a kula da ita, a tabbatar da lafiyarta, da lafiyar Magajin Sultan." Cewar Aymana.

Jakadiyya ta miƙe tana nufar ƙofa, Aymana kuwa wani irin tashin hankali da bugawar zuciya ne suka ziyarceta a lokaci guda.

Sultan kuwa wani farin ciki ne fal zuciyarsa, ya rufe idanuwan shi, Aymana ta lura da murmushi dake ɗauke a fuskar shi.

Tunani ya fara yi, akan su Ayda da mahaifinta, ya san yau burinsu zai cika, za su samu yaro ko yarinya daga ɓangaren shi, ya fara jin zafi a zuciyar shi, wani ɓangare na zuciyar shi kuma ya sanar da shi yaro ko yarinyar da zai zo duniya jinin shi ne dole ya so shi.

Buɗe ido yayi ya kalli Aymana, saurin nemo annuri tayi tare da baiyanar da shi a fuskarta "Tabbas yau gidan Sultan muna cikin farin ciki."

Shiru bai yi magana ba, ta miƙe "Yana da kyau na shiga ciki don sanin halin da Gimbiya da Magajin Sultan suke ciki."

"Aymana!" Ya kira sunan ta, ta dawo ta sunkuya "Allah ya baka nasara."

"Ki zauna tare dani." Ya faɗa cikin bada umarni "A gafarceni farin ciki ba zai bar ni ba."

Kai ya ɗaga mata. Ta yi hanyar waje tana kallon yadda yanayin gidan ya sauya, sai bayi da kuyangi suke kai kawo daga cikin gida zuwa ɓangaren Ayda.

Sashen Gimbiya Ummi ta fara nufa tun daga ƙofa ta ke kwalla mata kira, Gimbiya Ummi ta fito babu alamar fara'a ko nuna farin ciki, sam bata so ace Ayda ce zata zata haihu tare da yaron nata. Aymana jikin ta yayi sanyi.

Ta durƙusa tare da faɗin "Yau akwai yiwar zuwan Yarima a gidan nan."

Murmushi tayi "Hakane  Aymana, sai dai ban so daga ɓangaren Waziri ba." Wannan lokacin Gimbiya Ummi ta kasa ɓoye damuwarta, har ta fitar.

"Haba Gimbiya Ummi, ai yaron ne namu ba su ba, ki nuna farin ciki ko don jin daɗin Sultan."

Ajiyar zuciya tayi ta ruƙo hannunta suka ida zama a tare, suna zaune Sai ga Mama ta shigo da murnarta, Suna gama gaisawa Aymana ta miƙe tayi musu bankwana ta shiga ciki.

Tana shiga falonta ta fara jiyo guɗa daga Jakadiyya, faɗawa tayi kan kujera tare da lumfasawa da gudu Farida ta turo ƙofa.

"Allah ya taimaki Gimbiya, Sultan Ya samu Magaji, Allah ya sauki Ayda Lafiya ta samu ɗa namiji."

Rufe idanuwa tayi, Farida ta ce "Ki gafarceni, jin daɗin mu ace Magajin Sultan na farko kece mahaifiyar sa, amm..."

Kafin ta ida Aymana ta ɗaga mata hannu, tare da faɗin "zaki iya tafi Farida." Jiki a sanyaye Farida ta bar falon.

    Aymana ta miƙe tayi cikin ɗakinta kan gado ta faɗa tare da sakin wani irin kuka mai sauti, wannan wace iriyar ƙaddarace akanta, wane irin ƙiyayyace a tsakaninta da Sultan irin haka.

Dafe kai tayi tana sharar kwalla, wata zuciyar ta sanar da ita, dama fa bawai kunyi aure don haɗa mu'amala bane, miye naki na jin zafi akan Sultan bai kusance ki ba, ya kusanci matar shi.

Cire kayanta tayi ta faɗa banɗaki tare da sakarwa kanta ruwa, sanyi take son samu daga zuciyarta.

Tana fitowa ta hau shiri, don ta samu nutsuwa, Addu'o'i ne fal bakinta don samun sukuni da kuma dakewa.

Ƙayataccen shiri tayi tana mai fitowa a hankali, magana tayiwa Farida akan zataje sashen Sultan.

Yana tsaye yana kai kawo a falon bayan fitar Jakadiya, Aymana ta shiga sam bai san da zuwanta ba ta fara magana "Gaisuwa ga ingarma a cikin sarakuna, Jarumi a cikin jarumai, ɗan sarki jika ga sarki, kayi zamanin ka xakayi na wasu, Ɗan Mu'azzam baban Mu'azzam Barka da samun ƙaruwa."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now