💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMA ILYAS KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA UKKU*
A ƙofa ta haɗu da Hajiya ta na shirin shigowa ɓangaran,Aymana ta sauke ajiyar zuciya Hajiya tace "Yanzu jakadiya ta ke gayamin Hawan Yarima,kenan zamu saka ido ya zama shima ya na da wani tsari a gidannan."
"Sam ba zai yiwu ba,ba zai samu wannan izinin ba."
"Ai idan bai samu ba ba za ki ji Sanarwa ba"
"Kenan Mai martaba ya bada umarni?"cewar Aymana tana zaro ido,don tasan an riga an gama tunda har Maimartaba ya bashi izini.
Hajiya ta har zuƙa"Lallai ba zamu saka ido ba,wai miyasa Maimartaba baya tunanin ko Yaron nan yazo da wani tsafine,baya tunanin ko yazo ƙara mallakar gidan nan."
"Ko ma miye nizan je gun Baba,zanyi magana dashi."Ta yi maganar tana wuce Hajiya.
Aikuwa haka akayi Aymana ta na zuwa duk mutanen ƙofar babu wanda ya tambayeta ko Lafiya za ta shiga wajan Sarki a yanzu,ganin fuskarta a ɗaure hakan ya sa Gaisuwa ce kawai ta haɗa su.
A Zaune ta samu Maimartaba,ta nemi izinin zama tare da Gaishe da shi kamar yadda ta saba,kallonta yayi tare da faɗin
"Fuskar ki babu walwala Allah ya sa ba wani ya taɓa ƴarlelena ba"
Jin yayi salon rarrashinta da bata dama hakan yasa ta samu kwarin guiwa"Akan Hawan zamiya da akace Yariman Toro zaiyi ne"
"Me ya faru da hawanne?"
"Maigirma ina ganin kamar muna sakin jiki,da kuma basu dama data wuce iyaka,ina gudun kar hakan ya..."
Bata ida ba ya katseta"Aymana har yanzu abinda baku gane ba shi zaman lafiya yafi zama ɗan sarki,Ke yafi ma sarkin kan shi,Mu zauna da Masarautun nahiyarmu lafiya shine zai bamu damar kuɓuta daga nauyin da Allah ya bamu"
"Baba amma Takobin gidanmu dake hannun su fa kenan."
"Kar a kumayi man magana akan wani abunmu dake gunsu,Sun riga sun ci gasa,hakan ya basu damar mallakar takobin gidannan."
"Amm.."
kafin ta ida ya katseta"Zaki iya tafiya,Ni da kaina na bada izinin hawa ga Yarima Amin,babu wanda ya isa ya hana,kuma babu canza baki a tare dani."
Wani irin abu Aymana taji hakan yasa ta duƙar dakai tana neman afuwa ganin fusatar da yayi.
Cikin wani irin yana yi tayi ɓangaren Hajiya acan ta samu bata nan sai dai tana ɓangaren Mama,a mamakinta duka yaran gidan suna zaune.
Ko da suka ganta basu tsaya tambaya ba,Aymana bata zaune ba ta dafa wani"Akan wani yau Sarki ya haƙiƙance mani,wannan wane irin abune."
"Me sarkin ya ce?"
"Ya ce babu makawa akan abinda ya ce?"
Ta na maganar fa juya tana fita daga ɓangaran,Sashen Umma ta nufa acan ta samu Bilkisu tana ma Umma tsarin yadda zasuyi.
Aikuwa tasha faɗa agun Aymana,Sai dai Aymana bata samu goyon bayan Umma ba,don Umma bata son wasa haka bata lamunci raini ba.
Aymana ta dafe kai tana zama"Shi kenan Umma kuyi Hakuri"
"Ni ba haƙuri na nemi ku bani ba,kuna ɗauka mutanen gidannan suna son kune komi?dole ne sai kunyi haɗin kai dasu?"
"Ni dai Allah Umma na daina kamar yadda kika buƙata." cewar Bilkisu.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.