MASARAUTA 18

109 18 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA SHA TAKWAS. 18*

Tako biyo ya ƙara zuwa wajen ta, "Ba na son jin kina faɗar ban ɗauki masarautar ku da muhimmanci ba, ki sani Sarkin Bilyam yana da matuƙar muhimmanci a wajena, yanzu haka ban sanar dake zuwana nawa ba bayan dawowar mu, jiya kamar yanzu ina tare da shi."

Aymana ta juyo ta kalleshi, hakan ba zai sa taji sanyi ba,sai dai jinjina kai kawai da tayi, Yarima yayi hanyar fita tare da faɗin "Zan turo Farida yanzu ta gyara maki ɗakin." Yayi maganar yana fita.

Bin bayan tayi da kallo, ba jimawa sai ga Farida ta shigo ta zube a gabanta "Allah ya huci zuciyar Uwar ɗakina, ya sanyaya zuciyarki, ke mai yafiya ce ga mutanen ki, ina mai tuba gareki akan abin da aikata ba tare da sani na ba."

Aymana ta sauke ajiyar zuciya, Farida ta lumfasa hakan ya tabbatar mata da Uwar ɗakin ta ta ba zata tanka ba, ta miƙe ta isa wajan da aka ɓata ta hau gyarawa.

***
Washe gari mutanen gidan ko wanne shire-shire ake don bikin murabus ɗin Mai martaba, Yarima Amin yana tare da Sarki duk wasu shirye shiryen ɓangaren shi ne yake tsaye akai ana aikatawa.

Aymana kuwa a ɓangaren Gimbiya Ummi tayi zamanta, sai marece ta tashi don zuwa wajen Mama ta gaisheta,Mama tana zaune da wasu bayi suna harhaɗa wasu kaya a tsakar gida Aymana ta gaisheta, Bayin suka gaishe da Aymana ta amsa tare da zama kan kafet ɗin gefen Mama.

Mama ta kalleta "Ba ki haɗu da mutumin na ki ba."

Sai da ta ɗan yi shiru kafin tace "A'a banganshi ba, tun fa safe, sai dai nasan aiyuka sun sha kan shi."

"Gaskiya kam, yanzu ma shayi ne ya kawo shi."

Aymana ta yi shiru Bayin suka kwashe kayan, Mama ta basu umarnin tafiya.

***
Tun safe gida ya ɗau harama baƙi suka fara zuwa daga masarautun Nahiyoyin dake maƙotaka dasu don amsa goron gayyatar masarautar Toro akan Liyafa da Sarki ya haɗa don bikin murabus ɗin shi.

Yarima yana kan shirin shi fararen kaya ya saka ɗinkin ya amshi jikin shi, ya aza rawani  sai dai rawajin iya kaine bai gewayo fuskar shiba, ya saka takalmi tare da fesa turare ya ɗauko  agogon hannu yana ɗorawa ya fito.

Ya samu Farida tana falon tana ajiye kayan karin su, ɗan tsayawa yayi tare da faɗin "Mai ɗakin ku ta fito kuwa?"

Cikin sauri ta zuɓe tana gaishe shi tare da faɗin "Eh ranka ya daɗe  ta fito, har ma ta bani saƙon kiranta idan na ga fitowaka."

Yarima yayi shiru, Farida ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin Aymana, babu jimawa ta dawo tare da rusunawa "Tana zuwa." daga faɗar haka ta fice.

Bata ɓata lokaciba ta fito, takonta ya maido da hankalin shi saboda yadda kayan adon jikinta zuke ƴar ƙara, yana riƙe da agogon.

Aymana tana sanye da wasu kayan saƙi na jinin sarauta rigar ta buɗa sosai sai dai akwai wani abin ɗaurewa  hakan yasa sigar jikinta fitowa.

Ɗan kwalin data naɗa siraran gashinta ya baiyana a gefe da gefen fuskarta,babu kwalliya fuskarta sai dai akwai jan janbaki a laɓɓanta biyu.

Inda yake ta nufa ta bishi da kallo "Barka da fitowa."

Murmushi yayi tare da faɗin"Shigarki ta ƙayatar da zuciyar Sarkin da bashi da Mulki  a masarautar da Izza bata baiyanuwa."

Aymana wani sanyi ya ziyarceta, jin yabo daga Amin, ƙarasawa tayi ta kama agogon da yake ƙoƙarin sakawa har lokacin hakan ya bashi damar barinta don ɗaura mashi.

"Da nonon wuri dana ɗari duk farinsu ɗaya!"

Yarima ya jinjina kai jin yabon daya samu daga wajen ta "Zamu iya karyawa kafin mu fita?"

Ta gama saka agogon tare da kallonshi "Kamar bana buƙatar cin komai, hakanan yau farin ciki yake ziyartar zuciyata."

Yarima ya riƙo hannunta "Ni kuma sai na tashi da faɗuwar gaba."

"Sadauki kake faɗuwar gaba bai zama naka ba, dakewa ko wane lokaci shi yafi dacewa dakai." tayi maganar tana zama gefen kujera.

Sai kuma tayi saurin miƙewa"Yana da kyau muje wajan Gimbiya Ummi don karyawa, ko don Addu'o'i da muke buƙata daga wajanta."

"Haka ne zaki iya ɗauko maya fiki."

Aymana tasa hannu ta ja wani babban yadi mai kyalle dake ƙasa yana binta a jikin rigar, da shi ta yane jikinta suna fitowa.

Kuyanga Aisha ce ta gaishe su tare da bin su baya don yi masu rakiya.

Sun jima a wajan Gimbiya Ummi su ka yi kari, Ummi tana son Aymana sosai ganin yadda duk abubuwan yarinyar na kwarin guiwa ne zuwa ga ɗan nata.

Sai da ya miƙe don tafiya wajen taron ya koma gaban Ummi tare da durƙushewa a gabanta, Ummi tasa hannu saman kafaɗar shi "Allah ya yi Albarka a rayuwarku ya tabbatar maka da alkhairi, ya saka maka dangana akan kowane ƙaddara mai kyau ko akasin haka."

"Na gode ranki shi daɗe." ya faɗi tare da miƙewa.

Har yakai ƙofa ya juyo cikin Sa'a kuwa Aymana shi take bi da kallo, murmushi yayi ya fice Ummi tayi saurin kauda idonta akansu.

***

Sarakuna ne makyil a babbar fadar masarautar, ko wanne da shiga ta alfarma, ranar ya'yan sarakuna kansu sun bayyana, kowa yana son ganin ya hallarci wannan babban taron, Yarima Amin sai da ya bi Sarakunan ɗaya bayan ɗaya ya gaidasu cikin girmamawa.

Akan Mai martaba ne Baban Aymana yafi daɗewa, don shi kan shi Sarkin Bilyam yana mai sha'awar ganin Yarima Amin ya zama Sarki don yasan zai gudanar da adalci ga al'ummar dake ƙasan shi.

A irin yadda Mulki da muƙami yake da daɗi yau gashi ɗaya daga cikin sarakunan nahiyar su ya yanke shawarar sauka don karin kanshi.

Sai da aka fara gudanar da taron tare da jawabai daga mahukunta da kuma wasu sarakunan.

Yarima Amin yana zaune gefen yan uwanshi, su Yarima Saifu sai cika ake ana batsewa, yau yana ganin babu wani sama dashi, ganin shi ne ya saka azuciyar shi zai yi mulki bayan mahaifinsa.

Sauran ƴan uwan sarki suna gefe, su Galadima, Sarkin gida, Maga yaƙi, shantalin Sai waziri da yasha Babban rawani akai.

Bayan jawabin sarakuna aka ware lokaci mara tsayi don cin abinci da ɗan hutawa ga sarakuna.

Ba jimawa aka dawo, sai dai Mai Martaba ne zai yi jawabi akan saukar shi da kuma godiya ga dubban mutanen da suka halarci taron.

Bayan godiya da Addu'o'i da yayi, ya ciga "Ba sauka ta yana nufin zan saka ido akan abubuwan gudarwar wannan masarautar ba, dole zan kula da wanda zai hau mulki, wanda zuwa yanzu zan sanar da wanda zai hau karagata."

Kowa na wajan ya ɗago yana ƙara mayar da hankali kan Sarki, Nan take ɗakin taron ya hargitse da ƴar hayaniya ƙasa-ƙasa.

Sai dai har lokacin Yarima Amin idon shi a rufe yake tun lokacin da Mai martaba yayi magana.

Yarima Saifu ya gyara zama yana murza hannuwa alamar ƙagara.

Waziri kuwa kallon Galadima yayi tare da faɗin "Lokaci na yayi Galadima."

Gyara alkyabbar shi yayi tare da gyaran murya, hakan ya maido hankalin kowa.

Mai martaba ya ansa wata takarda da wani yake miƙo mashi ya cigaba kamar haka.

"Sakamakon goyon baya da kuma ra'ayoyin wasu daga cikin sarakunan da suke goyon bayan masarautar mu, hakan ne ya ba da damar Yarima Amin shine zai hau karagar Mulkin masarautar nan, hak..."

*Haliloss ce*

MASARAUTAWhere stories live. Discover now