💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA SHA HUƊU. 14*
Murmushi yayi yabi hanyar ɓangaren shi,a nan ya sameta tsaye jikin bango"Allah ya taimaki Gimbiya an fitar da shi."
Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta,jin kiranta da yayi da Gimbiya tako ta farayi,ya bi bayanta da kallo,tana shiga bata tsaya komai ba sai da ya nemo Farida don gani yake kamar wani abun zai zo mata.
***
Aymana ta fara kwasar kwanaki a gidan,Mai martaba ya ziyarci masarautar Bilyam yayi godiya akan auren da aka ba yaron shi,duka ɓangarorin biyu sunji daɗi kuma sun fahimci juna.Cikin mutanen da sukayi tafiyar ne,Baba Haroun ƙanin mahaifin Aymana ya bada wani saƙo a kawo mata.
Sai dai cikin rashin sa'a saida ya buɗe saƙon aciki yaga wata doguwar takarda,ya shiga tsananin tashin hankali jin yadda ake jadda mata muhimmancin abinda taje ɗokowa don kar ta shagala.
Ya kiɗima sosai saidai yayi dogon tunani Daga ƙarshe ya yanke shawarar kai mata,kuma bazai baiyyanawa kowa ba gudun matsalar da zai iya saka kanshi.
Tana zaune Farida ta shigo ta zube gabanta"Allah ya taimaki Gimbiya wannan saƙone daga gida,an sanar Baba Haroun ne ya aiko."
Cikin sauri ta karɓa,ta warware ganin akwai tarda ta kalli Farida"zaki iya tafiya."
"To ranki ya daɗe"A hankali ta miƙe tabar wajan ta ciga ciki,ita kanta tasan yadda Baba Haroun yake son ta mayar da TaKOBI gidansu,kenan har yafi su Mama da Hajiya saka abun a zuciya.
Tsaye ta tashi tana kai kawo,ji tayi ana shirin shigowa ta yi saurin naɗe takardai,Yarima ya shigo da kayan hawa jikin shi,Aymana ta ce"Barka da sirdi."
Harɗe hannuwa yayi"Kowa ya halarci kallon hawa ban da ke me hakan yake nufi."
"Bana da buƙata don a raina ba wannan lokacin naso ka shirya hawanba."
"Miye dalilin ki na ƙin sanar dani?"
"Ina ganin kamar ba hurimina bane"
Juyawa yayi zai fita,sai kuma ya tsaya"Ya zama dole na rinƙa sanin abinda yake zuciyarki,bazan lamunci wannan ba"yayi maganar cikin izzar dake yawo jininshi
Taɓe baki tayi,yana ficewa ta miƙe ta na fitowa karo suka yi da Hassatu riƙe da tire da kayan marmari,ta jima a wajan tana sauraron su duk da ba komai take jiyowa ba.
Zubewa tayi tana faɗin"Allah ya taimakeki abin motsa baki na kawo"
Bata ce komai ba sai barinta da tayi a wajan ta fice zuwa ɓangaren Baba Galadima wajen Mama.
***
"Kar mu saki jiki dasu,bokanya ta sanar dani muna gab da shiga babban haɗari yana tunkaromu."Inna ta ce"kaje ka samu Yarima Saifu ko yasan wani abu dangane da hakan."
Waziri ya miƙe yayi wajan Yarima Saifu,suna tattaunawa"Ni fa babu abinda na sani illa in gaji mahaifina,koma miye zai tunkaromu dole ne mu fuskance shi."
"Ka kwantar da hankalinka,dukkanmu magoya bayanka ne,babu wanda ya isa zama mamallakin gidannan sai kai."
Cikin sauri Farida ta juya jin abinda su Waziri suke faɗa,wajan Aymana ta nufa ta samu tana salla haka ta zauna tana jira harta ƙarasa ta maido hankalinta gunta,ta labarta mata.
Aymana ta miƙe tsaye,cikin nuna isa da nuna ko in kula"Wannan bai shafi masarautar Bilyam ba,Zaki iya tafiya Farida."
"Allah ya huci zuciyarki,ya kauda maki ɓacin rai,bansan hakan zai taɓa zuciyar ki ba."
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.