MASARAUTA 52

103 12 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA HAMSIN DA BIYU. 52*

Inna ta juyar da kanta, tana mai jin takaici, ita ba ma halin da Waziri yake ciki ne matsalar ta ba, a'a ko yaya ne tana son ganin Ayda ta zama wani abu ko da kaɗan daga darajar Aymana ne.

***

Sun shiga hidindimun auran Saratu wanda gaba ɗaya komai na Auren Aymana ce ta shirya, ta jajirce wajan ganin hidimar ta tafi yadda ake buƙata tare da ƙayatar da komai kan tsayi.

Tana tsaye tsakiyar gidan Farida ta nufota da An-nur ta kalle su tana faɗin "Daga ina haka?"

"Allah shi taimakeki Wallahi rigima ya ke."

"Ba na da lokaci Farida kuje da sh...

Bata ida ba Sultan ya ƙara so gabanta, ya amshi kayan da take haɗawa ya aje gefe, ya kalli ƙofar ɗakin Gimbiya Ummi ya ce "Ki same ni ciki."

Ya bawa Farida Umarnin bin shi baya, A tare suka Shiga Aymana tana take mashi baya, ya zauna dirshen gaban Gimbiya Ummi yana gaidata.

Gimbiya Ummi ta kalli Aymana "Gimbiya an gama haɗa kayan."

"Allah ya ja kwananki Ƙara na kawo fa, Ina gaisuwa amma ba ta ni ake ba."

Gimbiya Ummi ta kayar da hankali kan shi "Allah ya taimakeka, wa ya taɓa ka?"

"Akwai wanda ya isa bayan Aymana."

Aymana ta matsa cikin sassarfa tana zubewa gaban Gimbiya Ummi Sultan ya ce "Kin ganta, ba ta da lokacin An-nur."

Aymana ta kalle shi "Wai har yanzu ba ka gane ya cika rikici bane."

"Wai Gimbiya Ummi ta ya yaro yana kuka amma ba zata bar abinda take ta kulashi ba?"

Aymana zata yi magana Gimbiya Ummi ta riga ta "Kai dai ana kula ka ko?"

Sultan yayi shiru jin irin tambayar da akai mashi, ya Sunkuyar da kanshi ƙasa, yama rasa abin cewa ya ɗago ya kalleta "Idan yana kuka ki rinƙa kulamin yaro, so kike ya tashi da rikici a gidannan, kina ganin yadda ake renon yara ana kula su amma ke ba ki yi."

Dariya Gimbiya Ummi tayi tana kallon yadda yake magana ta ce "Allah ya taimakeka ita ba irin matannan bane masu ɗoki akan 'ya'ya."

"Dama na san ba zaki taɓa goyon baya na ba akan ta." Ya yi maganar yana miƙewa.

Aymana ta dafa kafaɗar shi "Allah ya huci zuciyar Sultan, duk abinda ka ce haka ake yi a gidanka, a gafarceni ina tuba."

Ta juya tana kallon Farida tare da cewa ta bata An-nur.

Sultan ya miƙe zai fice ba magana, Gimbiya Ummi ta ce "Na Barka lafiya."

Juyowa yayi da sauri ya na sunkuyawa ya kalli Aymana "Kina neman zautani a gidan nan."

"Allah ya baki nasara Na barku lafiya."

Su suka sukayi dariya, Sultan ya fice abinshi.

***

An gama biki komai ya lafa a gidan, Sultan yana jin shi kamar wani Ingarman doki a sarautar shi, yanzu ya iya riƙe ragamar komai na mulkinshi, hankalinsu kwance Addu'o'i kuwa ba dare ba rana sun jajirce.

Sultan da kanshi ya jagoranci 'yan uwan abokinshi Bilal don nema mashi auran Bilkisu a masarautar Toro, bayan sun tafi ya rage daga Sultan sai Mai martaba.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now