*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA ASHIRIN DA HUƊU. 24*
Sunkuyar da kanta ta yi jin yadda yau Sarki Amin ya saka mata Albarka, sai dai bata ƙarasa tunanin ba ya cigaba "Tabbas kinyi matuƙar ƙoƙari, kin kuma cancanci yabo Aymana!" Ya yi maganar da nuna maryabawa gareta.
Aymana ta ɗago ta kalle shi a karo da biyu, ta fara tunanin yadda ta samu yabo daga gare shi, wani ɓangare na zuciyarta ya tuna mata yadda Kaka ta jajirce tare da nusar da ita muhimmancin yin wannan Walimar.
Awanni kaɗan bayan Aymana ta shiga hali akan Ayda ta kasance ta farko da Sultan ya tara da ita, lokacin data rasa mafita da kuma hanyar do sa, Kaka ta kira ta na kuka tare da sanar da ita halin da take ciki.
Kasancewar Kaka tsohuwar data fito daga Babbar masarauta hakan yasa ta ba Aymana shawara da kuma umarnin shirya wannan taro zuwa ga Sultan Amin.
Don tasan yin Walimar zai samarwa jikanyarta martaba a idon Sultan da mahaifinshi.
Yarima ya katse mata tunani da faɗin "Ina mai godiya gareki a karo na biyu!".
A zuciyarta tace Kaka ce ta cancanci ka yiwa godiya, sai dai a fili ta ɗan jajirce wajan faɗin "Girman ka ne, Allah ya taimakeka."
Bayan ta bar wajan Yarima tana komawa ta samu kiran Kaka ta sheda mata yadda akayi taron da kuma yadda Sultan ya nuna jin daɗin shi.
***
Haka aka ɗauki ƴan kwanaki, har girki ya dawo hannun Aymana, babu abinda bata yiwa Yarima Amin ba kamar yadda take mashi, sai dai yana gama cin abinci ta kalle shi "Zan je in kwanta."
Ta faɗi tana miƙewa, tayi sashen ɗakunan shi, hakan ya sa ya kwantar da hankalin shi, don yayi niyar idan har ta ce ɓangaren ta zata tafi tofa za suyi rigima.
Abinda bai sani ba, ita kanta Aymana tana yiwa kanta yaƙi ne kar mutannen gidan su fuskanci wani abu.
Ko da ya tashi ya shiga ciki yayi mamakin ganin bata ɗakin shi,ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kayan bacci.
Ɗayan ɗakin dake kallon nashi ya shiga, kwance ya sameta har tayi bacci, ya jima yana ƙare mata kallo, tabbas yasan Aymana itace a cikin zuciyar shi, yana jin ƙaunarta sosai, musamman data kasance mashi wani bango daya jingina har ya kai shi ga matsayin da yake a yanzu.
Haka ya gama ƙare mata kallo har ya gaji ya fice, tun daga wannan ranar ɗakin ya zama ɗakin Aymana domin kuwa duk ranakun girkinta anan take rayuwar ta.
***
Komai ya daidaita gare shi ta ɓangaren gudanar da mulkinshi, da kuma samun haɗuwar kan al'ummar dake ƙarƙashin shi hakan yasa bashi da wata damuwa.
Damuwar shi ta ɓangaren Waziri da Yarima Saifu ne, suna ƙoƙari wajen son ganin sun shige mashi, da kuma kawo wasu tsare-tsare na su a masarautar, hakan ya sa ya gane su ya fara nuna ƙarfin mulkin shi akansu da duk wanda yake ganin zai kawo mashi cikas.
Ya zama na ya daina sakasu a cikin mashawartan shi, duk wani abinda ya shige mashi duhu ya kan je wajan Mai martaba ya sanar dashi, shi kuma ya ɗora shi akan hanya.
***
Yau Aymana daga cikin gida ta dawo da saurinta ta nufo sashen su, tana son ganawa da Sultan ne game da zancen da taji yana yawo akan zai naɗa Sarkin sarakunan Nahiyar, wato ɗaya daga cikin masarautun nahiyar zai bawa sarautar.
Ta san tabbas idan aka yi hakan kenan Masarautar Bilyam da mahaifinta yake mulka za ta ƙara ƙanƙanta, bayan kuma ada itace babbar masarauta.
Idan har Sultan Amin ya yi wannan naɗin to masarautar zata zama itace ta biyu a duk nahiyar, wani ɓangare tana mai gudun naɗin ya kawowa shi kanshi Sultan ɗin nakasu ya zama waccen masarautar ce zata ringa jagorantar masarautun nahiyar ba shi ba.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.