MASARAUTA 53

139 9 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA HAMSIN DA UKKU 53*

Mai martaba ya kalli Yarima Saifu tare da faɗin "Me hakan ya ke nufi Yarima?"

"Na sani iya kulawa da Soyayya ka nuna a tsakanin yaranka, Kowa yasan Sultan shine mai jiran gado a tsakaninmu, amma sam hakan bai sa mun bi ka ba, Ina roƙon gafarar ka Baba."

Cikin sauri Mai martaba ya rike shi "Shi kenan Yarima, Allah ya muku Albarka, Allah ya yafe mana baki ɗaya."

Yarima Saifu ya juya zai yiwa Sultan magana, Sultan ya kaɗan mashi kai ya dafa kafaɗar shi "Ba na buƙatar jin komai ɗan uwana."

Yarima Saifu ya rungume Sultan yana hawaye, Sultan ya ɗago shi yana goge mashi, Mai martaba ya ji daɗi sosai anan ya ƙara saka masu Albarka tare da jan hankalinsu gaba ɗaya.

Lokacin da Yarima Saifu ya je ya samu Gimbiya Mai gado da yadda suka yi da Sultan wata irin tsawa ta daka ma shi "Ba ka da hankali Saifu, Sultan dinne ka amince mawa? Lallai ashe kayi asara, To bari ka ji in sanar dakai, babu wata soyayya a tsakanin ku, haka kuma ba zan taɓa kallon su a matsayin masoyanmu ba."

"Gimbiya ki tsaya ki fahimce ni."

"Fahimtar me? Ko dai an asirce min kai? Ba zan taɓa yadda ba, ko ba daɗe ko ba jima sai ka hau karagar shi, ko da hakan zai zama sanadin m...

"Sam ba na buƙata, ko da kuwa Sultanne ya bani da hannunshi, sam ban cancanta na zama sarki ba."

"Wallahi ban yadda ba, Kare baya kukan banza!"

Hakan da ta ce ya sa Yarima Saifu miƙewa sanin kanshi ne bai zama lallai a zama ɗaya ya shawo kan mahaifiyar shi ba, sanin irin yadda ta ke da kwaɗayi tare da burin ganin ya riƙe sarauta.

Lokacin da Waziri ya ji cewar Yarima Saifu ya koma ɓangaren Sultan tashin hankalin shi ya ƙaru musamman yanayin yadda Yarima Saifu yake girmamma Sultan tare da bin duk umarnin shi, ya zamana kamar Yarima saifu ya na neman fara gudanar da mulkin kujerar shi.

***
Ayda kuwa ta rasa hanyar shawo kan Sultan, duk inda take son ganin darajarta ta ɗaukaka a gidan hakan ya faskareta, gashi yanzu Waziri iya kanshi yake wa yaƙi.

Gaba ɗaya Bayi, kuyangi da barorin gidan sun fita harkarta.

****

Lokaci yana tafiya Alhamdulillah hankalin Aymana ya kwanta ganin komai na gidan yakan tafi ne da saninta, yayin da abubuwan fada kuwa Sultan baya zartarwa sai ya nemi shawararta.

Ta ji daɗin yadda Yarima Saifu yake mu'amala mai kyau da Sultan hakan yasa ta ɗan sake mashi, Gimbiya Mai gado kuwa tana nan akan ƙudirinta na son ganin Yarima Saifu ya hau karaga.

Sultan ne ya shigo Uzairu yana take mishi baya da wasu kaya a hannunshi, Sultan ya zauna.

Aymana ta fito daga ɓangaren ɗakunan shi, Uzairu ya gaishe da ita cikin girmamma, ta juya tana wa Sultan sannu da Zuwa, Sultan bai amsa ba, Aymana ta nufi kayan da Uzairu ya aje lokacin ya fita.

Wasu sandunane kalar wanda Sultan yake amfani dashi na kwalliya, ta buɗe tare da faɗin "Wannan fa Allah ya baka nasara?"

Rawanin shi ya cire tare da faɗin "Yarima Saifu ne ya kawo min."

Shiru tayi na wani lokaci, Sultan ya tsaya yana nazarinta, wannan lokacin ta fara tunanin Sultan ya fara daidaitawa da 'yan gidan shi, amma ita tana son yi mishi magana akan Baba Haroun, ganin kwata-kwata ko labarin shi bata taɓa ji ba, tun bayan da aka kawo shi masarautar.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now