MASARAUTA 43

160 20 0
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA ARBA'IN DA UKKU. 43*

*SIYYA COLLECTION* 07033111950

Ki na buƙatar HUMRA mai ƙamshi? *Nemi Siyya collection.*

Ki na neman TURAREN WUTA, Na jiki, kaya, da na tsugunno, kina son zama ƴar gayu saboda ƙamshi mai sanyi ? Nemi *Siyya collection*

Ina Amarya da uwayen gida dake son dawo da martabar Auren su *Siyya collection* na da ingantatun kayan gyaran jikin amare. Akwai kayan mata masu ciko da jiki da kuma saukar da ni'ima.

Kina son fatar ki tayi laushi da santsi tare da haske mai kyau? *Siyya collection* ta tanadar maku, light cream, whiterning cream da Glowing cream kala-kala.

Sabulun wanka masu saka fata haske, ingantattu da basu da illa. ki nemi *Siyya collection*

Supplement domin ciko da inganta Breast da hips, akwai na kyaran fata xalla, ba sa da illa ga lafiyar ku.

Don gyaran gidanku da tsabtar shi *Siyya collection* tana siyar da turaren mopping.

Ku dai ku Tuntuɓeta akwai sauƙin kuɗi, haka kuma muna tura kayanmu duk garin da kuke. *Siyya collection*
Call:-09136159778
Whatsapp 07033111950.

*Page 43*

Dariya Ruƙayya ta bawa Aymana, ta kalleta ta ce "Haba! haba! Idan kin barni me ki ka yi kenan, ki jira ki ida ladar ki."

Tayi maganar tana miƙewa suka nufi ɗaki don kwantawa sai dai Ruƙayya bata barta ita ɗaya ba gudun wata matsala.

Ƙarfe biyu da 'yan daƙiƙu, Sultan yayi saurin farkawa daga baccin, yasa hannu ya dafe kanshi tare da karanto Addu'o'in kariya, ya miƙe yana kallon Ayda da ta ke gefen shi, Khairat tana cikin gadon jarirai.

Ya faɗa banɗaki yayi alwala, ya fito, ya canza jallabiya yanayin shigar larabawa, ya ɗauki wayar shi, ya buɗe ƙofa, yana son ganin Aymana ko don tabbatar da lafiyarta, hakan ya sa yabi ta ƙofofin baya ya shiga sashenta.

Ɗakinta ya duba bai sameta ba, ya ɗan kwankwasa ɗakin da Rukkayya ta sauka, ganin bata nan hakan yasa hankalinshi ya tashi ya nufi ɗakin da suka shirya don haihuwar Aymana.

Har zai kwankwasa sai yaga kamar hakan zai ɓata lokacin shi, da sauri Ruƙayya ta kalli ƙofa, Sultan ya nufi bakin gadon wajan da Aymana take nishi.

Tana ganin shi ta kawar da kanta gefe, Sultan ya kalli Ruƙayya "Me ke faruwa?"

"Allah shi taimakeka, ta na gab haihuwa da yardar Allah."

Ta yi maganar tana mayar da safar hannu ta likitoci, Sultan ya kamo hannun Aymana, lokacin tana dafe mararta, Ruƙayya tayi saurin gyarata, Sultan ya kalli ta "Ah Rukkaya Kiyi a hankali fa.

Shiru tayi ta cigaba da aikin ta, Aymana ta fara jin ciwo ya canza mata, lokacin ta fara wata irin zufa, duk yadda ta daure kar tayi magana sai da ta saki cizon da takewa harshenta tare da fara salati da ƙarfin murya.

Ruƙayya ta dawo tana shafa cikinta, ta duba ta taga har kan jariri yana tunkarowa, Aymana ta fara kyarma, Sultan ya riƙe ta yana mata Addu'a, Aymana ta ce "Mutuwa zan yi, Na san mutuwa zan..."

Bata ida ba Sultan ya daɗe mata baki "Ba zaki mutu ki barni ba insha All..."

Rukkayya ta matso tana ɗago kan Aymana ta dannata "Kiyi Nishi kar abin cikin ki ta samu matsala, yaron yana neman taimakonki."

MASARAUTAWhere stories live. Discover now