MASARAUTA 35

145 22 7
                                    

*MASARAUTA.*

*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*

*2021*
      *HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
       (AuntyHaliloss).

*SHAFI NA TALATIN DA BIYAR. 35*

Ya jima kafin bacci ɓarawo ya ɗauke shi, da asuba bacci bai ishe shi ba haka ya lallaɓa ya zame jikinshi daga nata ya shiga banɗaki yayi wanka tare da ɗoro Alwala ya  fita Masallaci, bai ɗauki lokaci ba ya dawo don baya son ta tashi baya kusa.

Shigowa yayi ya zauna bakin gadon yana binta kallo mai ɗauke da tsananin soyayya, ya matsa a hankali yakai hannunshi, yana mai dafa kanta tare da fara shafa gashin kanta cikin wani irin yanayin so.

A cikin baccin Aymana take jiyo shi, buɗe idanuwanta tayi a hankali tana sauke su akan shi.

Yarima ya gyara kwanciyarshi tare da faɗin "Na tashe ki ko?"

Cikin sauri Aymana ta rufe idon ta don wata kunyar shi ta ziyarceta, tasa hannu ta ja bargon tana rufe fuskarta.

Ƴar dariya Yarima yayi ya gane kunyace ta jagoranceta, hakan yasa ya jawo ta jikinshi "Lokacin Sallah yayi, ki tashi naga lafiyarka." Ya faɗa cikin kulawa.

Jin bata bashi amsa ba, ya sa hannu yana shirin janye bargon, Aymana ta sa hannunta tana rufe fuskarta Yarima yayi dariya "Yau kuma Sultan ɗin ake jin kunya."

Da murmushi ɗauke a fuskarta "ka barni naje nayi salla."

Ɗagota yayi "Ni fa ba na riƙe ki bane."

Ido rufe Aymana ta fara lalubar son tashi tana ƙoƙarin saukowa, amma jikinta wata irin zafi tayi saurin komawa ta zauna, Yarima ya riƙota "Muje na taimaka miki."

"Bana so."

Dariya yayi yana mai tuno maganganun ta na daren jiya hakan ya sashi faɗin "Bana so, Mai martaba ka barni na daina."

Sauri tayi ta buɗe idonta, ta na kai mashi duka a kirji, tsaye ya miƙe "Au ni ko? Ai kuwa yanzu zan kuma."

Yana maganar yana jawota, cikin sauri ta zulle "Tuba nake Allah shi taimakeka."

Dariya ya saka ya riƙo hannunta tare da miƙewa "Shi kenan muje na gani, na shirya miƙi."

Ba jiranta yayi ba, hanyar banɗaki kawai ya nufa da ita, ya zaunar da ita "Zauna bari na haɗa ruwan."

Aymana ta jingina kanta da bango tana kallon shi, ya haɗa ruwan ɗumi ya juyo ya kalle ta cikin nuna kulawa "Kin gaji ko?"

Shiru tayi hakan yasa ya nufi wata ma'ajiya ya ɗauko burosh da abin wanke baki, ya matsa, ya zauna gefenta, yakai burosh ɗin bakinta, yana son fara yi mata kafin ruwan su gama taruwa.

Da taimakonta ya gama mata ya wanke ya juya ya kashe ruwan, yasa hannu ya na janye rigar da ya saka mata, wata kunya ta ƙaraji, sam Sultan bai damuba, baya son ganin zata wahala.

Cikin ruwan ya sakata, yana gaggasa mata jikinta, ya jima sosai kafin ya mata wanka, da kanshi ya saka mata towul kafin ya riƙota zuwa ɗakin.

Komai Sultan ne yayi mata idan tazo yima zai anshe yayi, mamaki sosai tare da ita, yau ya ƙara canza mata tana ganin kamar ba Sultan ɗin da ta sani ba.

Da taimakon ta ya saka mata kaya, ya shimfiɗa mata abin salla, ganin ta kabbara sallar hakan yasa ya fita falon don shigo da kayan abincin da ya yi oda.

Sai da ya aje komai, Aymana ta jima tana Addu'o'i tare da roƙon Allah farinciki a rayuwarsu mai ɗorewa.

Ganin baya nan hakan yasa ta ci gaba da zamanta, tsawon lokacin sai gashi ya shigo ɗakin, bisa mamakinta, da shiri taganshi kenan wanke yaje ɗayan ɗakin yayi.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now