*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA TALATIN DA SHIDDA. 36*
Ana zuwa gaban Sultan Aymana ta sunkuyar da kanta ƙasa, Sultan yayi murmushi yana mai saka hannu ya fara ɗago kanta, Jakadiyya ta matso da salon kiraki.
Sultan ya ɗago hular ya ɗorata akan Aymana, murna aka kama yi, Aymana wani sanyi ya ziyarceta, tabbas tasan darajar sarauta, hakan yasa take jin kamar ya bata duk wani farin ciki da zata iya nema.
Ɗagowa tayi a hankali tana mai son mayarda hawayen farin ciki dake neman zubar mata, Sultan ya koma kan kujerar shi ya zauna, Ayman ta tsuguna a gaban shi alamar godiya da kuma girmamawa.
Sultan yayi murmushi kawai, Mama ta kamo hannun Aymana suka koma mazauninta.
Mai martaba kuwa yasan tabbas hakan yana nufin Sultan ya samu farin ciki na tafiya da Aymana, shi kanshi yasan tabbas Aymana ta cancanta a yaba mata.
Waziri kuwa zuciyar shi kamar zata huda kirjinshi ta fito, wani baƙin ciki yake ji, lallai Sultan ya tabbatarwa mutanan gidan babu wani bayan Aymana.
Goggo dake gefen Ayda ta riƙe hannunta "Ki daure Kar ki..."
Fizge Hannu Ayda tayi tana mai barin wajan sanin cewar idan har ta tsaya tabbas sai tayi abinda zai ja hankalin kowa, tun kafin ta isa sashenta take kuka, Allah ya taimaketa babu kowa mutanen gidan suna farfajiyar.
Haka aka tashi taron masu murna sunayi masu baƙin ciki kamar suyi hauka.
Sultan sashen Gimbiya Ummi ya wuce don gaida ita, sai da ya gaida kowa kafin ya wuce sashen shi.
Aymana kuwa ita kanta bata samu kanta ba, saboda masu taya murna dake zuwar mata da kuma Barka da dawowa.
Jin ance Sultan ya shigo hakan yasa tayi saurin miƙewa don zuwa wajan shi, kasancewar tasan Ayda ce zata amshe shi.
Yana zama Aymana tana shigowa da sassarfarta ta ƙarasa gaban shi ta durƙusa "Allah ya ja kwanan ka, ina godiya, ina jin farin ciki har bansan taya zan yi godiya ko bada tukuicin wann..."
"Ba a biyan tukuici don wani tukuicin."
Aymana ta ɗago, Sultan ya miƙe yasa hannu ya ɗagota suka miƙe tsaye ya riƙe kafaɗunta "Wannan shine tukuicin ki da kika kasa zaɓar abinda kike so."
Murna tayi tare da rungumoshi ta kai bakinta tana sumbatar shi "Na gode."
"Shi kenan dai a fidda ranar fidda shagali don taro akan..."
"Ranka shi daɗe bana buƙatar hakan, Sam bana so sarautar ta zama zan rinƙa gudanar da ita, babu buƙatar shagali."
"Me hakan ke nufi Aymana?"
Murmushi tayi ta lakaci hancin shi "Mai kula da Sultan ba zai samu lokacin gudanar da wani mulki ba, iya kula dakai ma mulki ne."
Dariya yayi jin yadda ta zaɓe shi akan sarautar daya bata "Allah ya maki Albarka."
Bayan fitar Aymana haka tasa aka fitar da kayan tsaraba ga kowa har da Maimartaba a ciki.
Bayi da kuyangi sunyi murna sosai, Jakadiyya tsarabarta ta dabance, ita kau da ma ba tun yanzu ba Aymana ta gama da ita tunda ta kaita ƙasa mai tsarki.
Ranar Ayda sai da ta taɓo mashi zancen banbanci da ya nuna tsakanin su, shiru yayi ya ƙaleta ganin duk kalmar da zai yi mata ya riga ya taɓa yi mata wajan nusar da ita akan abinda yayi niya bazai fasa ba.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.