*MASARAUTA.*
*EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA TALATIN DA UKKU. 33*
SADAUKARWA GA:
_Rahama Niger tare da Ummi Zariya._Cikin jin tsoron tsawar da Sultan yayi Ayda ta ja baya, ya gane ta tsorata ne hakan ya sa shi kasa ida magana, sam bai san ta yaya zai ɓullowa Ayda ta gane rayuwa ba, a ganin shi rawar kanta ya yi yawan da har take wuce muhallinta.
Ƙofa ya nuna mata tare da rufe idanuwanshi, cikin tsanannin ɓacin rai, jiki babu kwari ta fice, cikin takaicin kalar wulaƙanci da Sultan yake mata aduk lokacin da tazo mi shi da zance.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da koma wa ya zauna samar kujera yana kawar da ɓacin ranshi.
***
Washe gari tun safe suka gama shirin su, mutanen gida kowa ya fito don ganin tafiyar Sultan.Aymana ta fito daga ɓangaren ta, tare da kuyanginta, sai dai a babbar ƙofar falon shi suka barta, ta tura ƙofar tana mai gyara Alƙebbar ta.
Fitowa yake daga sashen ɗakunan shi, cikin wasu kayan Sarauta da suka amshe shi, ya rike wata sanda a hannun shi, yana ɗan azata ƙasa cikin tafiyar Sarauta.
Aymana ta ja ta tsaya sam bai ganta ba, saboda wani maɓallin Alƙebba da ya ɗan cire, ji yayi ya kaiwa mutum karo, cikin sauri ya ɗago yana kallon ta.
Aymana ta yi Murmushi tare da faɗin "Barka da fitowa ."
"Yauwa" ya faɗa yana ƙoƙarin gyara maɓallin, Aymana tayi saurin saka hannu tare da faɗin "Ko zan iya taimakawa Sultan."
Bar mata yayi tare da maida hankalin shi akan shigarta, ta burgeshi sosai yanayinta yayi kamar Sarauniyya dake jagorantar nahiya mai girma.
Ɗagowa tayi daidai lokacin da ta gama gyara mashi, Sultan ya yi murmushi kamar yadda ya gani a fuskarta.
"Ana jiran fitar Sultan."
"Sultan yana son keɓewa da matar shi." Yayi maganar yana mai ƙara tako zuwa gareta, Aymana ta ƙara shaƙar ƙamshin shi, tasa hannu tana dafa kafaɗar shi, cikin sauri Sultan ya sunkuya yana riƙota "Adon sarauta yana maki kyau Aymana"
"Ba kamar Yadda yake wa sarkin ba."
Ji tayi ya manne jikinsu, tare da sumbatarta a kumatu, cikin sauri ta matsa tare da faɗin "Kar ganin ruwa yaga Sultan."
Murmushi yayi yana tako zuwa fita, Aymana ta take mashi baya suna ficewa, haka suka samu ana ta jiran fitowarsu.
A bakin ƙofa suka haɗu da Ayda, don dolenta ta fito rakiyarshi tana gudun abinda zai ce ya dawo.
Sultan ya cigaba da tafiya suna binshi, a bakin farfajiyar cikin gidan duk matan gidan sunfito, iyayen su da sauran ahalin gidan.
Hannu ya rinƙa dagawa yana fitar da Murmushi, Gimbiya Ummi ta na tsaye ƙofar sashenta, wajan ta suka nufa, suka sunkuya, tare da kwasar Gaisuwa.
Ta kallesu bata nuna wani abu a fuskarta ba saboda matan gidan dake wajan.
Sultan ya matsa wajen sashen Gimbiya Mai gado ya sunya mata. Kafin ya juyo yayo hanyar fita.
Sai lokacin Aymana ta iso wajen shi, waigawa yayi sai yaga Ayda can nesa har ta tsaya.
Hakan yasa ya gyara tsayuwarshi tare da kallonta, kowa ya juya yana kallonta, kai Sultan ya ɗaga mata cikin salon da baya so a gane bai yi niyar zuwa da ita ba.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.