MASARAUTA 1

658 47 2
                                    

💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA*

*HAKKIN MALLAKA*
*HALIMATU ILYAS KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).

*SHEKARAR RUBUTU*
*2021*

*GODIYA*

_Tsantsar godiya ga ubangijin talikai wanda ya ke iko akanmu bayinsa,ya kyautar mana da lafiya,ya kyautar mana da iskar shaka,wannan kadai abin godiya ce a gare mu ga ubangijinmu Assamadu._

*HAR KULLUM HAR ABADA*

_Ina jinjina ga iyayenmu,ina rokon Allah ya kara masu lafiya tare da nisan kwana,ya Kara saka mana jinkansu a zukatanmu._

*GAME DA LABARI.*
_Ba cin zarafi ne ga wasu ba,illa iyaka ilmantarwa da kuma nishadantarwa,don haka wanda ya ga wani abu ya kusance shi,to arashi ne._

*SADAUKARWA GA*

_Daukacin masoyana da kuma litattafaina,wanda idan babu ku,to fa Halimatu ba za ta kai labari a fagen Rubutu ba._

*BismillahirRahmanirRahim.*

  
SHAFI NA ƊAYA. 1

Tafiya take yi a hankali, sanye da alkyabba a saman wani leshi mai tsada, da wasu takalma irin na jinin sarauta, hannunta da wuyanta sanye da wasu kayan ado, Kuyangi ne ke take mata baya, sai wata a gefenta ɗauke da kayan marmari  irinsu; Lemo, Inibi da Ayaba a cikin wani maɗaukin kaba. Gidan ganye suka nufa, wani wurin shaƙatawa ne da sarki kan zauna don hutawa, hakan ya sa ba kowa ne yake zuwa wurin ba, bayan shi sai Gimbiya Aimana, domin kuwa ita ce 'Yar da ya fi ji da ita a cikin jerin 'Ya'yansa.
       Wata mata ce ta fito tare da Jakadiya, Gimbiya Aimana ta ɗan tsaya tana ƙara daidaita nutsuwarta tare da ɗan rusunawa alamar ban girma zuwa ga mahaifiyarta.

"Ranki ya daɗe Umma." Matar ta gyara mayafinta ta ce,

"Gimbiya ina za ki je a wannan lokacin da muke sauraron shigowar baƙin namu?"

"Za a iya tarar su, ni zan je Gidan ganye ne in huta." Jakadiya dake gefen Umma ta ce.

"A gafarce ni Uwar ɗakina, rashin ganin ki zai sa ran Mai martaba ya sosu, kuma kin ga sauran matan gidan nan kowacce za ta bayyana da iyalanta ne." Yamutsa fuska ta yi tana ɗaga baki za ta yi magana, Umma ta ce.

"Lallai ki zo tarar baƙin nan da za su zo." Tana maganar tana ci gaba da tafiya, Gimbiya Aimana ta ɗan tsaya, kuyangar da take gefenta ta ce.

"Yar sarki jikar sarki, takawarki lafiya, ɓacin ranki fushin yaranki." Juya idanuwa ta yi, ta yi hanyar komawa cikin gidan, gaba-ɗaya kuyangin suka yi saurin buɗa mata hanya suna komawa bayanta. Babban ɓangaran su ta nufa, tana ɗan sauri, don sam ba ta so aka dakatar da ita ba, saboda ba ta son haduwa da baƙin.

       A falo suka bar ta, ta ƙarasa shigewa ɗakin ta fara cire Alkyabbar jikinta, ta zauna kan wata kujera tana jan gajeran tsaki. Wata matashiyar budurwa ta fito daga banɗaki tana tsane jikinta, ga dukkan alamu wanka ta fito, yarinyar ta kalli yayar tata, "Gimbiya lafiya kuwa, kin fasa fita hutawar ne?"

"Umma ce muka haɗu, ta ce lallai sai na jira baƙin sun zo"

"Ai na faɗi maki, ba za ta bari ba, musamman yadda ta ga Mai martaba yana murnar zuwan baƙin nan."

Gimbiya Aimana ta cire takalmin ƙafarta, "Sam ban ga amfanin murna akan baƙuncin da masarautar TORO za su kawo mana ba, akan me za mu sakar masu jiki!" Juyawa Budurwar ta yi tana ci-gaba da shirinta, "Idan da Maimartaba za ya amince da zancenmu, to da bai karɓi baƙuncin su ba." Aimana ta miƙe tare da barin wurin don yin nata shirin.

A cikin gida kuwa, kowanne ɓangare na masarautar shiri ake don zuwan baƙin, duk da suna ganin zuwan Yaron Sarkin Masarautar TORO kamar wani leƙen asiri ne ga tasu masarautar.

MASARAUTAWhere stories live. Discover now