💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA SHA UkkU. 13*
Aisha ta ɗago za ta yi magana,suka jiyo motsin shigowar Yarima jin muryoyin fadawanshi dake mashi a fito lafiya.
Yana ɗan murmushi ya shigo,su Farida suka durƙushe suna kwasar gaisuwa.
Aymana ta matsa wajan shi,ganin ya ɗan tsaya yana kallon ta,su Farida suka fice.
Aymana tace"Barka da dawowa."
Bai amsa ba yayi hanyar shiga Aymana ta bi bayanshi,a falon ya cire hular shi yana ajewa kan kujerar,kafin ya zauna tare da faɗin"Na sami Gimbiya Lafiya?"
Wani kwanji taji jin ya kambama wajan faɗin sunan tace"Alhamdulillah ko da buƙatar wani abu?"
Zatayi magana Hassatu ta shigo falon riƙe da tire tana sallama,Aymana tace"Za ki iya shigowa."
Gaban Aymana ta durƙushe tana aje tire ɗin,shayi ne a kofi biyu,tana ajewa taɗan tsaya"Za ki iya tafiya."
"Na barku lafiya"
Aymana ta je can gefen kujera ta matso da tebur gaban Yarima ta maida tire ɗin a sama,tsawan lokaci baiyi magana ba.
"Abin motsa baki"ta ce ba tare da ta motsaba
Rufe ido yayi ahankali ya jingina da kujera"Ga dukkan alamu akwai gajiya a tare Da Yarima"
Ɗagowa yayi ya buɗe ido"Nayi ziyara cikin gari don ganawa da talakawan yankin mu"
"Adalin shugaba"ta furta da nuna yabawa
Yarima yasa hannu ya ɗauki kofin ya ɗan kai baki,Aymana ta miƙe ta ɗauki ɗayan kofin"Zan shiga ciki,a huta lafiya"
Binta yayi da ido har ta shige,ya ɗan jima kafin ya miƙe ya wuce ɓangaren shi.
Da Marece Aymana ta fito don shiga cikin gida,kuyangi zasu bita tace Farida da Aysha kawai yayi.
Bangaren bayi da ma'aikatan gidan ta nufa ta zaga ko ina akayita gaisheta,daga nan ta wuce wajan Hajiya mai gado a ɗaki tace ta shiga bayan gaisuwa kaɗan Hajiya tace"Duk wanda ya tashi gidan sarauta yasan wani abu dangane da bayyana fashewar kwai a gidan sarauta."
Aymana ta kalleta"A wancen gidan ana son kawo sauyin hakanne."tayi matanar da Izza da kuma nuna isa.
Cikin mamaki Hajiya Maigado ta kalleta,kenan tana nufin sune suka ɓoye bayyana Amarcin su,ɗaga baki tayi zatayi magana Aymana ta sunkuya alamar bangirma"Zan gaida sauran mutanen gida,ki huta lafiya"
Wani wawan kallo ta bi bayan Aymana dashi.
Ɓangaren Yarima Saifu suka nufa bata wani samu karɓuwa daga wajan matar ba, hakan yasa suna gaisawa ta juyo.
A hanya Farida ta ɗan jera da Aymana tace"Allah ya taimake ki,abinda nike gaya maki kenan ɗazu."
Batayi magana ba sai Aysha da take tambaya hanyar da zasubi zuwa sashen Ummi.
Ta samu Ummi tana ɗan hutawa,a gabanta suka fara Gaisuwa,Ummi ta sa hannu ta ɗagota,ta juya tana kallon su Farida"Kuje tana fitowa."
Taja Aymana zuwa kan kujera Aymana ta zame jikinta tana shirin komawa saman kafet"Kiyi zaman ki,bana son wannan janye jikin da kike,bari in tado maki Saratu dama ɗazu nake mata faɗa bataje wajan ki ba."
Murmushi tayi dama ance Yarima yana da ƙanne amma bata gan su ba"Allah ya taimaki Ummi ki barta zan shiga ba sai kin wahalar da kanki ba"
Ummi ta koma ta zauna,ta kalli Aymana tana nazarinta,tana son Yarinyar sosai sannan taga alamun hankali tare da ita.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.