💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**EXQUISITE WRITER'S FORUM.*
*2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMATU KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA SHA BAKWAI. 17*
Babu ɓaga lokaci ya iso fadar yana mai durƙusawa"Allah ya ƙara maka nasara..."
Bai idaba Maimartaba ya kalli mutanan wajan,cikin ƙanƙanin lokaci suka fice.
Sarki ya zauna"Mi wannan yake nufi?"
Amsar takarda yayi yana karantawa,cikin gigita ya miƙe yana shirin fita,bincike ya farayi a fadar.kafin ya shiga ciki a ɓangaren Ummi ya barta hakan yasa ya nufi wajan.
Tun a ƙofa ya fara kiran sunanta,kafin ya fara magana"Me wannan yake nufi,kina tunanin zaki iya saka hannunki a jerin manema karagarmu?Nan masarautar Toro ne ba Darul-Bilyam ba,har kike son zama Sarauniya?"
Aymana ta miƙe ganin Yarima ya kai maƙura wajan tunkarota,ja tayi ta tsaya cak,cikin mamaki yau an samu wanda yake mata tsawa yake mata hayaniya akai ba tare da ta ɗau hukunci ba.
"Isa,Izza,mulkin sarautarku a ƙarƙashin mulkin gidanmu yake,ya zama dole ki ƙasƙantar da kanki wajan girmama masarautar mu"
"Dakata!!!" Aymana ta faɗa cikin hucin zuciya.
"Kana min magana akai ta yadda bana fahimtarka,kayi ƙoƙarin tsabtace kalaminka akan masarautarmu bazan laminta ba! Da kake faɗar inason mulkarku akanme?waye yace maka nace zan mulke ku?"
"Gashi ki duba rubutunkine,ko zaki musa,Nace ko zaki min musu!!!"
Yayi maganar cikin ƙara ji,Aymana tasa hannu tana duba takardai abin mamaki kalar rubutunta ne akayi amfani wajan rubutun.
Kankujera ta faɗa tana dafe kai,Yarima ya yarfe hannuwa"Baki da abin cewa kin aikata kenan?"
"Ban aikata ba,sam wannan ba rubutuna bane"
"Amma ke kikayi aiken zuwa fada."
Aymana ta miƙe tana nufarshi,Yarima ya ja baya"kar kizo min nan kar kizo min nan"
"Idan ba ke ki ka yi aiken ba taya Farida zata kai saƙo zuwa fada"
Gimbiya Ummi ta buɗe ƙofa tana fitowa da sauri"Wai me nake ji haka?"
Juyawa suka yi suna kallonta,Aymana ta durƙushe kan guiwoyinta,dai dai ƙafafun Gimbiya Ummi,ta kalli Yarima"Ba magana nake maka ba?"
Aymana tace"Laifinane Ummi Laifinane."
Tana maganar tana miƙewa,ta fice,bajimawa ta dawo Farida tana binta baya,a tsakiyar falon Aymana ta kalli Farida,ta dafa kafaɗunta duka biyu,ta jijjigata.
"Kinyi bacci ne ko me Farida?"
Sai kuma ta fara sauke mata mari a gefen kuncinta,Farida ta zube a gabanta"Ina mai tuba gareki uwar ɗakina."
"Yaushe na Aike ki da wannan takardai zuwa fada?"
Cikin zare ido Farida ta kalla,ta maida idonta kan Yarima dake huci"Wallahi ba ke kika aikeni ba"
Aymana ta miƙe taye ta dafe kai,ta kalli Farida za ta yi magana Gimbiya Ummi tace.
"Zan barku da iyawar ku,idan ba zaku iya yimin bayani ba"
Farida ta matsa gaban Ummi tana gaya mata wadda ta bata takarda zuwa fada.
Da sauri Yarima ya matso yana duƙawa"ke baki da hankali zasu aike ki kije?"
Aymana ta faɗa kan wata Kujera,Yarima ya fice cikin sauri.
Gimbiya Ummi ta kalli Aymana"Kar wannan ya fara gusar da tunaninku!kar ku taɓa tsumayen Alkhairi inda baku ga haske!!"
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.