💙💙💙💙💙💙💙💙
*MASARAUTA.**2021*
*HAƘƘIN MALLAKA*
*HALIMA ILYAS KANGIWA.*
(AuntyHaliloss).*SHAFI NA HUDU. 4*
*Sadaukarwa ga Mum Sayyed & Noor ina jin daɗin yadda ki ke posting littafin Masarauta.💖💖💖*
Yarima kuwa shiga ya yi irinta yaran sarakan nahiyar,bai saka kayan da Aymana ta bashi ba,tun a ƙofar ɓangaren ya hau dokin shi sai faɗawa dake jan linzami.
Haka suka nufi wajan taron,Dai-dai lokacin Aymana ta na kan zama saman kujerar da aka tanada dominta.Chak taja ta tsaya don kallon shigowar Yarima Amin,ayau yayimata kalar Sarauta sosai shigar ta burgeta duk da taji babu daɗi ganin bai saka nata kayan ba.
Murmushi tayi tasa hannu ta ɗan gyara Alƙebbar jikin ta,Bilkisu ta matso"Kin ga ɗan gayun Yarima ko?"
murmushi ta kumayi mai nuna isa tana riƙo hannun Bilkisu.anan aka sanar da zaman Aymana sannan Yarima Amin.
Sai dai yace yana jiran zuwan maimartaba kamin zaman shi,Yana kan faɗa sai ga Sarki ya shigo da zagagen shi,ana mashi kirari.
Yarima ya sauko yana nufa gun Sarki anan ya kai gaisuwa,Sarki ya miƙa mashi hannu,shi kam yarima baya iya haɗa hannu da Manyan shi hakan yasa ya ƙara sunkuyar da kai.
"Fatan komi ya kammala."
"InshaAllah yanzu za a fara"
"Allah ya bada sa'a"
yana niyar tashi sai ga Aymana ta zube gaban sarki don gaishe shi"Aymana shiri yayi Allah yayi maki Albarka"
"Ameen Baba"
A tare suka miƙe yana nufar tsakiyar filin yayin data koma kan kujerarta,Yarima yana hawa dokin aka faɗi cewar Zai fara zamiyane ga Gimbiya kafin Sarki.
Aymana ta fara kallon mutanan wajan dake kirari suna kiɗe kiɗe.
Can ƙarshen fili ya koma Yarima ya gilgiza linzamin doki yana ƙara daidaita sirdi.
kafin kace mi,dokin ya harzuƙa ya fara sukuwa,ya na sassarfa,dokin ya fara gudu yana gudu idan ka gani zakayi tunanin Yarima zai faɗo,da gudu dokin ya nufi Wajan Aymana,a tunanin kowa Aymana zata razana,amma Sai miƙewa tsaye da tayi tana gangarowa tana tunkarar dokin.
ihu aka saka,Dokin yayi wani irin kuka yana ɗaga hafa kamar zaya haye Aymana.wata irin zamewa sukayi daidai lokacin Yarima ya zare wata wuƙa yana tilli da ita zama.
Ga mamakinsu Dokin ya tsaya wuƙar ta dawo hannun Yarima,kiɗa da busa aka soma,Yarima ya sauko yana miƙa dokin hannun wani bafade.
Haɗa ido sukayi da Aymana.Murmushi tayi hakan shima nashi ɓangaren.
Ya juya yana ɗaga hannuwa sama.yayi tattaki.
Hajiya da Mama suka kalli juna basuyi tunanin Zai sauko kan dokin lafiya ba,Jakadiya ta biƙe haɓa"To ko dai shima da abinda ya taka?"
Shi kuwa Yarima wajan zama ya nufa,ya dan zauna kadan ana gudanar da wasu shagulgulan,ya mike ya nufi cikin gida bai jima ba ya dawo da shigar kayan da Aymana ta kai mashi.
Ya k'ara yin kyau sosai kowa ya san yarima akwai gayu,ba b'ata lokaci ya kumayin zamiya ga Mai martaba.
Kowa abin ya burge shi.
Sai da aka fara kiran sallar magriba aka tashi,hakan yasa kowa ya wuce.
***
Washe gari Aymana bata je gun shi ba,saboda tsananin gajiya,mutanan gidan sunji dad'in zuwan yarima koba komai sun samu sauk'i daga bangaran mulki irin na Aymana don yanzu sai su wuni basu ganta ba.
YOU ARE READING
MASARAUTA
RandomLabari akan masarautu guda biya Darul-Bilyam da Masarautar Toro,sarƙaƙiya akan son mallakar Takobi da kuma sarauta.